Chapter 1 page 85

206 14 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*




Sai dare Muhammad yazo ya dauki Fauziyya suka tafi. Bayan ya tafi Hafsa ta kwanta wayar ta taji tana kara tana dubawa taga Ahmad ne. Dauka tayi cikin sanyin murya yace
"Baby na lafiya?"

"Lafiya alhamdulillah."
"Anya naji muryar ki haka."

"Ba komai fa!"
"Kinyiwa Yaya Fauziyya maganar."

"Na mata amman in kazo mayi maganar."
"Da akwai matsala ne?"

"Babu."
"Shikenan ai gobe muna tare."

"Allah kaimu."
"Amin. Wai bacci kika fara ne?"

"A'ah but your voice show akwai wani abu."
"Eh Deedat tsoro nake ji!"

"Wanne irin tsoro?"
"Kada wata rana ka juyan baya."

"Baby ba abinda zai sa na juya miki baya."
"Ka tabbata?"

"Na tabbata to me zai sa na juya miki baya ina sonki!"
"Kasan halin mazan."

"Ki cire haka akai na."
"To Allah yasa."

"Baby na miki alkawarin har abada ba zan juya miki baya ba."
"Allah ya yadda."

"Zan kula dake zan faran ta miki nai miki duk abinda kike so."
"Nima zan maka biyayya insha Allahu."

"Allah ya yadda ba zaki soni ba."
"So kuma na nawa!"

Yai murmushi yace
"Kina so na?"
Kai ta gyada tace
"Eh ina son ka."

"Godiya nake."
Tai murmushi. Yace
"Me kika tanadar min gobe?"

"Me kake so?"
"A'ah ai ni na fara tambaya."

"Shikenan zan tanadar maka kaina gobe zaka ganni zan maka kwalliya sannan da wani albishir."
"Dan Allah da gaske?"

Kai ya gyada yace
"Godiya nake amman da ki fadan albishir din na kagu naji."

"A'ah sai goben?"
"To ni me kike so na kawo miki?"

"Kai kadai nake so Deedat!"
"Ai daman ni naki ne."

"Wannan haka yake to ganin ka kawai nake so."
"Kada kisa na taho yanzu."

"Ah haba Madam din fa da kace tare zaku zo."
"Gobe ta taho."

Tai murmushi tace
"Ka kwantar da hankalin ka Allah dai ya kaimu goben."

"Amin amman kinsan kuwa mun fi wata ukun da na diba."
"Kai Deedat!"

"Wallahi kinga lokaci ya kusa ko?"
Tai murmushi tace
'Kabi komai a sannu."

"Haba Baby duk wannan bin da nake a sannu."
Tai murmushi tace
"Shikenan dare yayi ka tafi wajen Anty na."

"Ai tayi bacci ni kuma na kasa shuyasa na kira ki mu sha wayar mu"
"Da gaske?"

"Eh!"
"Toh ya labari?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now