Chapter 1 page 31

265 23 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

__________________

Washe gari da safe yana tashi wayar sa ya duba ko zai ga reply din ta amman bai gani ba sai ya kawo hakan ko da jan aji ne na mata. Wanka ya shiga ya fito ya hau shiryawa. Gajeren wando ya saka da singlet yana zaune yana neman layin Hafsa. Basma ta shigo da sallama. Hannun ta rike da basket na kayan karin Yayan nata.

"Ina kwana Yaya?"
"Lafiya."

Ya fada yana cigaba da danna wayar sa. Kallon sa tayi dan ba haka ya saba amsa mata gaisuwa ba. Wannan yasa ta hada masa tea din sannan ta mika masa tana fadin
"Ga tea din."

"Ajiye."
Ya fada yana kara trying number Hafsa da ake cewa a kashe take amman yaki yadda yana tunanin ko matsalar network ne.

"Yaya wa kake nema haka ne?"
Wayar ya ajiye yana kallon ta sai ya saki murmushi yana fadin
"Antyn ki "

"Anty nah?"
Ta tambaya. Kai ya gyada yace
"Eh Amarya ta mai zuwa ba."

"Oh tana lafiya? Ko kishi take zaka angwance yau."
"Hmmm!"

Kawai ya fada yana daukar tea da ta hada masa. Sha ya fara yi ya bude flask din cheaps ne da kwai kadan yaci ya mike yana duba agogon wayar sa karfe goma da minti ashirin.

Wajen wadrobe ya nufa zai saka kaya lokacin da Momy ta shigo dakin hannun ta rike da wata sabuwar farar shadda yar gaske an mata aiki da farin zare. Yana ganin Mommy ya durkusa ya gaishe da ita. Amsawa tayi ta mika masa kayan tace
"Maza ka saka ka fito lokaci na tafiya kasan karfe sha daya ne daurin auren ko?"

Kai ya gyada ya amsa ya  saka sannan ya feshe jikin sa da turare. Wani kyau yayi ya fito a angon sa. Agogo ya saka na azurfa ya saka bakin takalmi da bakar hula. Tare suka fita da Basma da Momy.

Yana fitowa Dady na fitowa daga dakin sa cikin shigar sa ta manyan kaya yar ciki da babbar riga milk tai masa kyau. Gun Dady yayi ya durkusa yana fadin
"Barka da asuba."

"An tashi lafiya?"
"Alhamdulillah."

Basma ce ta matso tana daukar su a hoto. Nan suka saka Momy a tsakiya sannan suka shiga dukkan su sannan akaiwa Momy da Dady. Daga nan suka shiga mota tare da duk masu aikin gidan maza suka tafi inda za a daura auren.

Karfe sha daya saura suka karasa. Nan aka zazzauna. Karfe 11am dai dai aka daura auren Ahmad da Hannah Akan sadakin dubu dari. Ana shaidawa aka wuce gun da za ai reception.

Ahmad kuwa Allah Allah yakoma gida ya kira Hafsa amman ba shi ya samu kan sa ba sai karfe biyu suka koma gida. Yana shiga gidan a cike yake dan yan yini sun fara zuwa. Da kyar yayi cikin dakin sa yana shiga ya cire kayan jikin sa. Ruwa ya watsa sannan ya fito ya zauna agefen gado yana kara neman layin nata. Amman still a kashe mamaki yake anya kuwa number tace ba wrong ta bashi ba.

Murmushi yayi yace
"In ba ma dai dai ta ban ba anjima zata ganni."

Ya fada yana kwanciyya nan bacci ya dauke shi. Momy da tin da aka dawo daga daurin aure take neman Ahmad bata ganshi ba dan ayi hotu na. Har akai la'asar dakin sa ta nufa dan dauko abu amman tana shiga ta ganshi yana ta bacci.

"Ahmad! Ahmad!!"
Ta kira sa. Ido ya bude yana kallo ta.
"Daman kana gidan ne?"

"Eh tinda muka dawo na shigo na kwanta."
"To maza ka tashi ka shirya."

"Me kuma za ai?"
"Uwar ka za ai."

Ta fada tana hararar sa. Mikewa yayi ya shige bandaki ya watsa ruwa ya dauro alwala yana fitowa bata dakin. jallabiyya ya saka ya tada sallah. Yana idarwa Basma ta shigo hannun ta rike da kayan sa. Kallon ta yayi yace
"Wai me za ayi ne?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now