Chapter 1 page 55

220 16 3
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 5⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


*
Zaune take bayan ta idar da sallah magariba ta jinginar da kan ta da gado idon ta a lumshe. In banda ciwo ba abinda kan ta yake yi.

Hajara ce ta shigo dakin rike da kwano ta ajiye a gaban Halima. Halima na shakar kamshin miyar ta mike da sauri tayi waje. A bakin rariya ta dinga kwalaya amai kamar zata amayar da ya'yan cikin ta. Sai da ta gama Hajara dake bayan ta ta taimaka mata ta dauraye bakin ta ta gyara wajen.

Tsayawa tayi rike da kai tana fadin
" Kije ki fitar da tuwon can bana son warin sa."

Daki Hajara ta shiga ta fitar da tuwon sannan ta fesa freshner ta dawo tace
"Na fitar."

Hijab ta saka ta toshe hancin ta ta wuce ta falo inda kannen ta ke cin tuwon ta nufi dakin su. Tana shiga ta fada saman gadon tana fadin
"Wash!"

Ta dafe kanta.
"Sannu Yaya!"
Hajara ta fada. Kai ta gyada mata. Hajara tace
"Me zakici to?"

"Hajara gurasar mai balango nake so ki siyon."
"Toh!"

"Duba jaka ta da ragowar dubu daya ki siyo min da lemon fata."
Mikewa Hajara tayi ta dauki kudin sannan ta dawo tace
"Yaya ko zamu asibiti dai?"

Kai ta girgiza tace
"Anjima nasha paracetamol sai daina ciwo."
"Sannu Allah sauwake!"

Ta fada ta mike ta fita. Tana fita soro wayar da Kabir ya bata ta dau kara zaro ta tayi ta daha ta kai kunnen ta.
"Assalamu Alaikum!"
"Wa'alaikum salam ina yini?"

"Lafiya lou! Ya Haliman?"
"Wallahi bata da lafiya!"

"Me yake damun ta?"
Ya fada da sauri.
"Nima dai ban sani ba amman tana yawan cewa ciwon kai yanzu kuma tayi amai dazu ma haka."

"Ya salam kunje asibiti!"
"A'ah tace in tasha paracetamol ma zai sauka!"

"Alright gani nan ina gefen unguwar ku zan karaso me zata ci?"
Shiru Hajara tayi. Yace
"Kar ki damu ki fadan me zataci!"

"Gurasa tace na siyo mata!"
"Wacce irin gurasa?"

"Ta masu nama."
"Alright gani nan ki tsaya a waje."

"Toh!"
Batai minti ashirin ba sai gashi nan. Parking motar yayi ya fito da manyan ledoji guda uku sai karama guda daya. Yana karaso ya mika mata. Amsa tayi tace
"Angode!"

Yai murmushi yace
"Ba komai! Kunyi magana kuwa?"

"Eh to dazu dai na mata magana take fadin taje kasuwa bata same sa ba in ta kira bata samun sa. Ita bata san me tai masa ba in wani laifi tai masa ya fada mata ta bashi hakuri. Gaskiya Yaya na son Isma'il dan Allah ka taimaka ka tambayrme shi mai tayi masa dan ta bashi hakurivdan tana ikirarin in ta rasa sa zata iya rasa ranta ni kuma ba zan juri rasa yar uwa ta ba dan Allah ka taimaka mana."

Ta fada idon ta na kawo kwalla. Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Kada kiyi kuka insha Allahu zanyi iya yina kinji."

"Kai ta gyada. Yace
"Ki mata sannu zamuyi waya gobe Allah sauwake!"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now