LAHANI

18 2 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 1*

Zainab ce zaune saman gado cikin room d'inta tayi tagumi da hannunta yayinda sirarrun hawayen nadama da tsantsar dana sani suke shatata afuskarta, kallo d'aya zakayi mata ka gane tana cikin matsanancin hali da matuk'ar damuwa adalilin k'alubalen rayuwar data fuskanta arayuwarta tareda rasa iyayenta alokaci guda, wani irin tuk'uk'in bak'in ciki da tsananin zogi zuciyarta keyi dak'yar take iya saukar da numfashin k'unci azuciya.
tunanin iyayenta ya fad'o mata arai ta dinga risgar kuka kamar zata shid'e shasshekar kukanta kawai kakejin ya gauraye cikin d'akin, jijiyoyin kanta sun taru tsiri tsiri ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya ji takeyi gwara ace ta mutu da wannan matsananciyar rayuwar da take fuskanta arayuwarta domin mijinta Laweezi ya riga ya cutar da rayuwarta tareda yi mata *LAHANI* azuciya alal hak'ik'a har abada bazata tab'a mantawa dashi ba saboda ya riga ya cutar da zuciyarta tareda k'unsa mata bak'in cikin rayuwa,amma tasan duk abinda ya faru da ita itace silar faruwar hakan saboda asanadiyyar rashin biyayya ga iyayenta ta gamu da duk wad'annan masifun da suka faru da ita, tasan cewar kwad'ayi da dogon burinta ne yaja mata haka domin da tayi biyayya awurin iyayenta da hakan bai faru ba!.
Kukanta kawai takeyi alokaci d'aya idanunta suka kumbura akan yawan damuwa da tsantsar tashin hankali,ta dad'e sosai tana zubar da hawayen zallar takaici da k'unar zuciya batasan inda zata saka kanta taji sanyi azuciyarta ba, can saiga Aunty Maijiddah ta izo k'ofar room d'in ta shigo tsakiyar d'akin hango Zainab da tayi tsakiyar gado tana kuka yasa hankalinta ya tashi zuciyarta ta girgiza, da azama ta isa wurinta ta dafa kafad'arta cikin tausayi da sanyin murya tace"subahanillah!Zeey mi ya sameki kike kuka?".
Zainab ta d'ago idanunta jajir da suka rine sukayi ja ta kasa bud'a bakinta tayi magana saboda zuciyarta sai k'una takeyi mata,kauda fuskarta gefe tayi tanata zubar da hawayenta domin kunyar Aunty Maijiddah takeji saboda duk ire iren bak'in ciki da tsagwaron taskun da suka shiga itace sanadiyyar tab'arb'arewar farin cikin gidansu da kuma mutuwar iyayenta!.
ta rasa dalilin dayasa Aunty Maijiddah takejin tausayinta tareda nuna mata k'auna da soyayya na musamman, saboda ita aganinta bata cancanci tausayi ko rangwame awurinta ba domin duk wani irin tasku da tsantsar walak'ancin da suka fuskanta arayuwarsu itace ginshik'in lalacewar komai.
ta fad'a cikin kogin tunanin rayuwarta ta baya can taji Aunty Maijiddah ta sake k'yaro mata tambaya cikin sanyin murya tace"Zeey magana fa nakeyi miki amma kinyi shiru....!".
"wai mi yake damunki ne k'anwatah....!?".
firgigit Zainab ta dawo cikin hayyacinta tareda duk'ar da kanta k'asa cikin mutuwar jiki tace"Aunty ba komai...!".
Aunty Maijiddah ta girgiza kanta cikin matuk'ar rashin yarda tace"ba komai Zeey kika zauna kinata kuka cikin d'aki ke kad'ai...!".
  "miyasa har kullum baza kiyi hak'uri ki rungumi k'addararki hannu bibbiyu ba...!".
"sannan ya dace ki fito fili ki gayamin damuwarki k'anwata saboda bakida wadda zata share miki hawayenki fiye dani, nice tamkar mahaifiya agareki saboda haka koke koken ya isa ya kamata ki fawwalawa ubangiji komai shi zaiyi miki wata mafitar alkhairi arayuwarki...".
hawayen rad'ad'in bak'in ciki suna kwaranya afuskarta ta iso gab da Aunty Maijiddah ta rungumeta tana shassheka alokacin ne tsantsar tausayi da bak'in ciki ke nuk'urk'usar zuciyarta, Maijiddah ta k'ara k'ank'ameta cikin matuk'ar k'auna da tausayawa rayuwarta itama idanunta sun cicciko da ruwan hawaye taff kamar zasu zubo amma ta daure ta had'iye ruwan hawayenta cikeda tsananin damuwa da tausayin kansu tace"ya isa k'anwata ki daina kuka kinji duk abinda kikaga ya faru dake k'addara ce saboda haka ki kwantar da hankalinki duk wanda ya cutar da wani arayuwa tabbas *SAKAYYAR ALLAH* saita sauka akansa....!".
"sannan kuma ita rayuwa da kike gani kowane mahaluki aduniya da irin k'alubalen rayuwar dayake fuskanta arayuwarsa, babu yadda za'ayi ace kodayaushe mutum yana cikin bak'in ciki ko farin ciki dole abubuwan rayuwa su dinga jujjuya maka akowane lokaci...!".
Zainab ta had'iye wani irin abu mai matuk'ar d'aci azuciyarta dak'yar ta iya bud'a baki tace"Aunty bazaki tab'a fahimtar yadda nakeji azuciyata ba...!".
"wallahi ji nakeyi kamar in kashe kaina akan bak'in ciki ji nakeyi kamar ace yanzu na mutu inbar duniya ko takaici da tsantsar bak'in cikin dake mak'ale azuciyata zai rabuda ni....!".
"ki daina cewa haka Zeey ba k'yau kinji amatsayinki na musulma ya dace ace kiyi tawakkali da dukkanin k'addarorin da suka faru damu ashekarun baya...!".
"bawai kin dinga fad'ar wasu maganganu ba marasa dad'in saurare saboda su Ummi sun riga sun rasu babu abinda suke buk'ata da muradi fiyeda addu'armu akowane lokaci...!".
Zainab tace"amma Aunty kinsan cewar duk abinda ya faru dasu Ummi nice silar faruwar hakan ko....!".
Aunty Maijiddah ta musk'uta cikeda matuk'ar d'acin rai tace"a'a ba kece sanadin mutuwarsu ba dama tun fil'azal ubangiji Allah ya k'addaro zasu mutu adalilinki...!".
"naji Aunty tunda bak'ya son in dinga alak'anta mutuwarsu Ummi akaina to na daina...!".
Aunty Maijiddah ta saka hannu ta share mata hawayenta cikeda matuk'ar k'aunar 'yar uwarta tace"yauwa Zeey ko kefa yanzu dai tashi muje dinning table kici abinci kafin doctor Nazeer yazo ya dubaki...!".
Zainab ta chuno bakinta gaba tace"na k'oshi Aunty wannan doctor ya cika takura...!".
Maijiddah ta harareta da wasa tace"Zeey banason sagarci idan ba'a d'ora ki akan magani ba so kikeyi ki tabbata da ciwon sanyi bayan kinsan yayi miki mugun kamu...!".
"ko saboda doctor Nazeer ya nuna yana sonki ne kike wani ja mishi aji bayan kinsan taimakonki zaiyi saboda yanada 'yan matan da suke kai kansu wurinsa....".
Zainab tayi rau rau da idanu kwallar zallar takaici ne ta taru cikin k'wayar idanunta tace"ni ina ruwana Aunty da masu sonshi....".
Murmushi Aunty Maijiddah ta saki tace"ke ko kikeda ruwa Zeey domin idan kika bari kikayi hasarar Nazeer to ina tabbatar miki kinyi hasarar mai k'aunarki da gaskiya wanda duk rintsi duk wuya bazai tab'a guje miki ba....!".
Zumb'ura baki Zainab tayi tace"naji".
"tashi muje kici abinci 'yar k'anwata kinji ki cire komai aranki komai yayi zafi maganinsa Allah....".Inji Aunty Maijiddah bayan ta mik'e tsaye alokacin ne Zainab ta tashi tsaye yayinda Aunty Maijiddah ta shiga gaba Zainab tana biye abayanta suka rankaya suka nufi parlour.

LAHANIWhere stories live. Discover now