LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 68*

Aunty Maijiddah tana zaune cikin d'aki tana tunanin k'anwarta Zeey,Ramatu dake gugar tufafinta tana kammalawa ta rungumo tufafin ajikinta ta shigo ta tsarasu acikin akwatin Maijiddah.
  Ramatu ta juyo fuskarta kallo d'aya tayiwa Maijiddah ta hango damuwa k'arara afuskarta cikin tausayinta tace"Aunty Maijiddah har yanzu tunanin Zainab kikeyi?".
"Har yanzu baki dangana ba ki fawwalawa ubangiji komai ba shine masani akan komai dayake faruwa".
Aunty Maijiddah ta nisa cikin rad'ad'i da tsantsat zogin zuciya tace"ya zanyi Ramatu dole inyi tunanin Zainab domin banida kowa aduniya saiku sai ita..!".
  "Ta yaya kike tunanin in manta da k'anwata bayan ta zamo ginshik'in rayuwata..?".
Ramatu ta dafa hannayenta cikin k'auna da tausayi tace"tabbas mantawa da ita abu ne mai matuk'ar wahala agareki amma ya dace ki sassautawa zuciyarki kada ki kamu da wani ciwo Aunty".
"Ubangiji shine k'addaro muku wad'annan iftila'in rayuwar da kuketa fuskanta arayuwa nasan idan kukayi hak'uri alal hak'ik'a zakuji dad'in rayuwa..".
Aunty Maijiddah ta numfasa tace"hak'uri ya zamo dole inyi Ramatu domin babu abinda zan iya yi akan haka".
Ramatu ta jinjina kai tace"gaskiya ne kun shigar da maganar kotu ne Aunty..?".

"A'a daddyn Jawaheer yace saiya k'ara bincike akai sannan ya gabatar da k'arar agaban alk'ali".

"Hmmmmm ai ya kamata ya fara kai maganar kotu sannan bincike ya biyo baya lokaci fa yana k'urewa ina jin tsoron kada ya k'ara cutar mana da Zainab". Fad'ar Ramatu cikin tsantsar jimami da alhini.

Aunty Maijiddah ta saukar da numfashi tace"nima haka nakeson yayi kafin Laweezi ya nakkasamin rayuwar k'anwa kinga ko isasshiyar lafiya batada ita".

"To ki k'ara yi masa magana ko za'a dace".

"Zanyi k'ok'arin ganin na shawo kansa ya amince ya fara shigar da k'ara".

(.)(.)(.)(.)(.)(.)(.)(.)(.)(.)(.)

Da tsakar dare misalin k'arfe goma daidai 10:00pm bayansu baby Jawaheer sunyi barci tuntuni itama Ramatu tayi, alokacin ne su barisster Hayatu suke k'unshe cikin d'aki sai aiki yakeyi alaptop yana duba wasu files na cases har uku,Aunty Maijiddah dake kwance kusa gareshi akan gado sai juye-juye takeyi ta kasa barci domin tunani da tsantsar damuwa sun hana mata sukuni da walwala arayuwa.
Ganin tana mutsul-mutsul yasa barisster Hayatu ya juyo fuskarsa akanta yace"Jiddanah miya sameki naga kinata motsi...?".
Aunty Maijiddah ta tashi zaune sai hamma takeyi alamar barci ne kwance cikin k'wayar idonta fuska ta b'ata tace"daddyn Jawaheer dole in shiga cikin damuwa in kasa barci..!".
  Barisster Hayatu ya zare hannu akan laptop d'insa cikeda matuk'ar mamaki yake kallonta yace"miye ya hanaki barci..?".

Aunty Maijiddah ta yakune fuska kamar zata rushe da kuka tace"adalilin har yanzu ba'a gano wad'anda sukeda hannu dumu-dumu akan mutuwar iyayena ba,ya kamata ace kuma mun kai Laweezi k'ara akan ya sakarmin k'anwa domin bai dace da ita ba".

Barisster Hayatu ya girgiza kai cikeda tsananin tausayi cikin sigar rarrashi yace mata"yanzu duk akan wannan maganar ne kika kasa barci..?".

Maijiddah tace"eh mana akanta ne barisster".

Yah Hayatu ya saki gwauron numfashi yace"to ki kwantar da hankalinki matata insha Allahu jibi zan kai k'arar Laweezi akotu domin rashin mutuncinsa yayi yawa bai dace ace shine mijin Zainab ba".

LAHANIWhere stories live. Discover now