LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 6*

Mama Halima tana shigewa cikin Laweezi ya jawo laptop d'insa yana wani aiki da ita wanda ya shafi harakokin business d'insa, can saiga hajiya Halima ta fito daga kitchen d'auke da tire ahannunta ta shak'o abinci acikinsa, tana isowa ta sunkuya k'asa ahankali ta dire tiren agabansa tace"son bismillah zo kaci abinci".Laweezi ya saki murmushin dake fallasa sihirtaccen k'yawonsa tareda aje laptop agefe ya tashi ahankali cikin tafiyarsa ta k'asaita ya iso gab da Mamansa dake zaune saman carpet yace"gani Mama".
hajiya Halima ta rik'o hannunsa na dama ta sanya cikin k'aramar roba ta wanke masa hannu tass, sannan ta bud'e kular abincin k'amshin girkinta ya daki hancinsa ya lumshe fararen idanunsa cikeda wani irin nishad'i da tsantsar farin ciki dake kwaranya a k'ark'ashin zuciyarsa.
"son fara cin abincin nizan shiga d'aki inyi barci..!".
Laweezi ya b'ata fuska cikeda sagarci yace"baza kiyi feeding d'ina ba Mama...?".
hajiya Halima ta dafe kanta alamar rashin son takura tace"kayyyy Laweezi ka cika takura fa..!".
"ya dace kabi hanyar da duk zaka bi Zainab ta dawo cikin gidan nan kona huta da yawan damuwarka..!".
"yanzu Mama damunki nakeyi ban sani ba...!".
"ko kin fara gajiya da d'aukar d'awainiyata ne yanzu inyi fushi insa akawomin Angel..!".
Mama ta k'unshe dariyarta azuciya tace"eh mana kayi zuciya d'in kaga sai in huta da takura..!".
Laweezi ya langwab'e kansa yace"to shikenan zanbi hanyar daya kamata Zainab ta dawo...!".
"dakam yafi maka zama gwauro...!".
"zama ahaka ai babu dad'i kanada kud'in k'ara aure ba bakadashi ba...!".
"idan ta nuna bazata dawo ba ka rabuda ita ka auro budurwa d'anya ai kud'in yaro ke k'arewa ba abin sayarwa ba...!".
"bazaki tab'a fahimtar yadda nakeji gameda Zainab ba wlh soyayyarta ta riga ta mamaye jinin jikina da ruhina....!".
"bazan tab'a iya rayuwa idan babu ita ba domin k'aunarta tuni tayi gini akatafaren filin zuciyata...!".
"yanzu ma da batanan cikin gidan nan ji nakeyi kamar babu wasu halittu acikinsa ya zamo kango ji nakeyi babu wani sauran nishad'i da kuzari atattare dani....!".
hajiya Halima ta saki murmushi irin nasu na manya tace"kaidai son baka rabo da shiririta da shirme fa...!".
Laweezi yace"saboda mi kikace haka Mama..?".
hajiya Halima ta yatsine fuskarta cikeda iyayi da kinibibi tace"haba Laweezi kanada kud'i kanada yaran da idan kabasu umurnin su kawo mata ita akowane lokaci dole subi umurninka...!".
"amma tana matsayin matarka zatayima taurin kai tace bazata dawo ba wannan ai salon iskanci ne da rainin wayo irin na 'yan matan zamani...!".
"ka tura yaranka kawai su dawo da ita ta k'arfi wannan hanyar itace mafi sauk'i agareka...!".

Laweezi yayi jugum kamar bazaiyi magana can yace mata"idan nayi haka kina ganin babu wata matsalar da zata kunno kai Mama...!?".

"auuuu tsoro ma kakeji son da kaida matarka uban waye ya isa ya rabaku...!?".

"to tun wuri ka mayarda ita cikin gidan nan kafin taje tana watsewarta awaje kana nan kana sakin baki da tutiyan ita matarka ce...!".

Laweezi ya kalli fuskar mahaifiyarsa cikin ido da ido cikeda tsananin jin zafin yadda ta danganta Zainab da zina yace"Mama zan iya rantse miki da mahaliccina in fito abainar jama'a inyi bugun gaba ince matata Zainab ba mazinaciya bace...!".
"koda na aureta abudurwa na sameta sannan kuma yarinyar tana yimin biyayya da ladabi gwargwadon iyawarta...!".

hajiya Halima ta hararesa da wasa tace"hoooo mara kunya 'ya'yan yanzu lamarinku saiku..!".
"ai maganar gaskiya ce duk inda take a fad'eta...!".
"naji mai gaskiya yanzu dai bari inbarka kaci abincinka hankali kwance..!".
Laweezi ya kalleta yana yamutsa fuska yace"please Mama ki daure kiyi feeding d'ina...!".
hajiya Halima batace uffan ba ta wanke hannunta cikin roba sannan ta fara d'ibar abincin ta sanya masa cikin baki, yana taunawa ahankali kamar bayaso cikeda matuk'ar sagarci idan ya had'iye lomar sai Mama ta koma sanya masa abincin abaki, haka ta cigaba da feeding d'insa har saida yaci abincin da dama ta ciko cup da drink ya sha rabi yayi gyashi alamar ya k'oshi.
ganin ya k'oshi ne yasa Mama ta jaye tiren gefensu suka cigaba da tab'a firarsu cikin fara'a da kwanciyar hankali sunayi suna dariyarsu cikin walwala da tsananin nishad'i..

LAHANIWhere stories live. Discover now