LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 71*

Su doctor Nazeer suna cikin mota suna firarsu atsanake akan maganarsu baba Yunusa,sunyi matuk'ar mamaki akan yadda baba Yunusa ya maida maganar ta fad'a bayan ta lalama suka biyo musu.
"Abinda baba Yunusa ya fad'a baiyi min dad'i arai ba harda tsine mana albarka yayi".Inji barisster Hayatu yana kallon mototin dake giftawa asaman titi.
Doctor Nazeer ya musk'uta yace"aiko ya tsine mana bashi zaisa tsinuwar ta sauka akanmu ba domin ba haihuwarmu yayi ba..".
Barisster Hayatu ya shafi k'irji yace"duk da haka ba dad'i akan aikinka mutum yace zaici zarafinka..".
Doctor Nazeer dayake tuk'a mota sai kallon kan titi yakeyi yace"hak'uri zamuyi dama rayuwa ta gaji haka wata rana munyi retire daga aiki k'annenmu da 'ya'yanmu ne akan mulki ko aiki..".

Barisster Hayatu ya langwab'e kai cikin matuk'ar nazari yace"babu shakka maganarka gaskiya ce".

Tafiya suka cigaba dayi har suka k'araso cikin unguwarsu iyayen Laweezi adaidai inda sukaga Muttak'a ranar nan suka parker motar,suna jiran suga wulgawarsa doctor Nazeer ya tab'o hannun Hayatu yace"barisster ka manta ne ranar nan ka amshi nombarsa fa..?".
Hayatu ya rik'e kai yana tunani can ya d'ago idanu yace"eh Nazeer na tuna bari in lalubo nombar awayata..".
"Lalubo nombar ka gani".
Barisster Hayatu ya ciro wayarsa a aljihu shiga cikin contact d'insa yayi ya duba nombar Muttak'a,wurin sunaye masu farawa da M yayi searching saiga sunan Muttak'a dana Malam Hakimi ya bayyana,nuna masa yayi yace"Nazeer kaga harda nombar Malam Hakimi nayi serving awayata..".

"Ka k'yauta domin wata rana nombar zatayi mana amfani..".

"Bari in kira Muttak'a inji yana ina..?".

Nombar Muttak'a yayi dialling ta fara ringing d'id'id'id'i tana shiga Muttak'a ya d'auka yace"yallab'ai an wuni lafiya..?".
"Lafiya k'alau Muttak'a ya aiki..?".
"Alhamdulilahi yallab'ai".
"Kana ina yanzu..?".
"Ina gida".
"Gamu cikin unguwarku adaidai inda muka tab'a had'uwa..".

Muttak'a ya tashi tsaye yace"okay gani nan zuwa wurinku yallab'ai".

"Saika iso". K'it barisster Hayatu ya katse wayar ya ajeta.

Babu dad'ewa suka cigaba da firarsu can suka tsinkayo Muttak'a tafe k'asa sanye da shadda light brown colour sai waige-waige yakeyi, saboda bayason mutanen unguwar su fahimci cewar yanada alak'a da Hayatu suje su tseguntawa Laweezi.
K'arasowarsa keda wuya barisster Hayatu ya bud'e k'ofar motar na seat back ya shiga ya zauna ya rufe.
"Mu matsa daga nan domin banason yaran Laweezi su ganni tareda ku..".Inji Muttak'a cikin sanyi jiki.

"Ina kake tunanin zamuje inda mutane basu cika wulgawa ba sai can ba'a rasa ba..?".Cewar doctor Nazeer yana kallon fuskarsa acikin madubi.

Muttak'a ya saki gyashi cikin yanayin rashin kuzari yace"tada motar muje zanyi maka kwatancen inda ya dace aparker motar sai muyi maganar daya kamata". Doctor Nazeer baiyi gardama ba ya tada motar Muttak'a yana yi masa kwatankwacen wurin da zasu keb'e har suka k'araso adaidai wani wurin da mutane basu faye yawan wucewa ba.

Acikin motar suka tsaya basu fito ba sai alokacin barisster Hayatu ya juyo fuskarsa yana kallon Muttak'a yace"Muttak'a mun zauna akotu zama na farko abokinka Laweezi yayiwa kotu bayanin cewar aikin company yakeyi,jikina ya bani abinda ya fad'a ba gaskiya bane amma in tambayeka bayan aikin company babu wani business da yakeyi a b'oye..?".
Muttak'a yayi shiru yana nazari da dogon tunani can ya saukar numfashi yace"yallab'ai tabbas Laweezi yana aiki a companyn dayake mallakinsa nima kaina ina zargin yana aikata haramtacciyar sana'a amma bansan wace irin sana'a bace,duba da cewar basa sakani cikin al'amarinsu shida Hudairu ganin cewar idan sukayi ba daidai ba nakan fad'a musu gaskiya".

LAHANIWhere stories live. Discover now