LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 75*

Su Habule anan suka cigaba da zama har gabatowar sallar azahar alokacin ne aka buga k'ararrawar tashi daga makaranta,yara k'anana maza da mata sanye da school uniform suka fara shisshigewa cikin school bus ana lodasu ana kaisu gidajensu.
Wasunsu kuma mototin iyayensu ne suka parker ajere kamar companyn saida mototi,kowane mahaifi ko mahaifiya sai ya fito daga cikin motar yana jan hannun 'ya'yansa suna wucewa,haka aka dingayi har zamana filin makarantar ya zamo tsit teacher's d'in makarantar tuni sun watse maigadi ya fad'a cikin d'akinsa ya d'auro alwala ya nufi masallacin dake kusaga school d'in.
Iren-irensu Mahafuz ne kawai suka rage wad'anda ba'a zo d'aukarsu da wuri ba,yara ne zazzaune suna jiran azo d'aukarsu yayindasu baby Jawaheer suka fara gajiya da zama cikin makarantar.

Mahafuz ne ya fara hamma yana gyangyad'i ya kalli Jawaheer yace"yaya Jawaheer har yanzu baba Labbo baizo d'aukarmu ba..?".

Jawaheer ta gyad'a kanta tace"eh Mahafuz ina ganin k'ila wani abu ya rik'esa ahanya...".

Mahafuz ya b'ata fuska kamar zaiyi kuka yace"ni na gaji da zaman school kuma barci nakejii..".

"Hak'uri zamuyi har ya k'araso nima na gaji amma muje bakin titi muyi tsaye kafin ya iso..".Inji baby Jawaheer cikeda alamun gajiya atattare da ita.

"Saidai mu fara takawa ahankali da k'afafunmu idan muka had'ushi d'aukarmu kawai zaiyi amma ni bazan iya jimirin tsayuwa akan titi ba".Cewar Mahafuz yana wani marairaicewa.

Jawaheer taja hannun Mahafuz tace"shikenan muje".Kai tsaye suka fito daga cikin harabar makarantar suka fara takawa da k'afafu domin su rage tazarar tafiyar dake gabansu,suna tsaka ga tafiya su Habule sukayi fitar burgu daga cikin kangon da suke sukayo wurinsu suna isowa suka watsawa su baby Jawaheer wani farin abu mai kamar powder luuuuuu sukayi zasu fad'i k'asa Habule ya sungumi baby Jawaheer,yayinda d'aya daga cikinsu ya sungumi Mahafuz suka koma gefe can Ogansu yazo da mota suka ciccib'esu suka saka acikin mota, nan take Ogansu ya tada motarsa suka bar harabar makarantar gaba d'aya.

Bayan tafiyarsu da minti biyar saiga Labbo driver wanda ya had'u da cinkoson mototi ahanya shine dalilin dayasa ya b'ata lokaci,yana isowa bakin get d'in makarantar ya parker motar tareda fitowa daga ciki kai tsaye ya fad'a cikin harabar makarantar koda yazo yara duk sun watse babu kowa, dube-dube lungu da sak'o ya dingayi baiga yaro ko yarinya ko d'aya ba hankali atashe yazo bakin k'ofar d'akin maigadi ya fara sallama,baba maigadi dake kishingid'e akan katifa yana sauraren labarai a rediyo ya amsa masa ya fito daga cikin d'akin,kallo-kallon sukayi atsakaninsu sannan Labbo driver cikin fargaba da damuwa yace"baba nazo d'aukar yara amma ban gansu ba...!".

Baba maigadi ya fitar da idanu waje afirgice yace"ikon Allah yaro ai tun d'azu aka tayarda yaran daga makaranta kuma koda na tafi sallah masallaci tuntuni ban taras da kowa ba..".

Labbo driver yaji gumi ya fara tsattsafo masa ajiki cikin yanayin tsinkewar zuciya yace"subahanillah!Baba kenan yaran nan sun b'ace...!?".

Baba maigadi ya kwantar da murya sosai saboda ganin ya gigice yace"kar kayi saurin karaya ka kira gida kaji idan sun koma gida..".

Labbo driver ya jijjiga kai alamar to sannan yace"shikenan ba komai nagode sosai baba sai anjima..".

"Ka gaida mutanen gida insha Allahu za'a gansu..".

LAHANIWhere stories live. Discover now