LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 65*

Ana d'ora Ummi Aziza akan gado nurses suka gurgura gadonta zuwa wani k'ebantaccen d'aki wanda ya kasance na mutum d'aya ne,da sauri doctor Nazeer ya chanza wasu kaya suna na aikin asibiti ta kutsa kai cikin d'aki yayinda yabarsu Zainab tsaye cirko-cirko awaje kowanensu zuciyarsa k'unshe take da bak'in ciki mara misaltuwa,idanuwansu sun chanza launi gaba d'aya sun koma kamar ba na mutane ba akan yawan kuka!.
Su kansu barisster Hayatu k'arfin hali kawai sukeyi amma abin yayi matuk'ar razanasu da rikita musu tunani,basason su k'ara karyawasu Maijiddah zuciya shiyasa suke k'ok'arin ganin sun danne rad'ad'in da sukeji aransu.

Acikin emergency room anyi nasarar ciwo wuk'ar da aka chakawa Ummi amma jinin dake zuba ajikinta yak'i tsayuwa,hakan yasa kafin a ankara harta zubar da jini mai yawa dak'yar da sud'in goshi suka wuni suna abu d'aya sannan suka samu suka tsayar mata jini, dukkan abinda ya dace sunyi mata doctor Nazeer da kansa ya siyo goran jini har guda uku aka k'ara mata ya k'ara siyo goran ruwa biyu domin ba k'aramin hasarar jini Ummi Aziza tayi ba ajikinta.
Hannunta sanye da gorar jini doctors da nurses suka fito daga cikin room d'in suna goge zufa afuskarsu, doctor Nazeer ne na k'arshen fitowa awahalce ya iso wurinsu barisster Hayatu yace"an samu an cire wuk'ar acikinta an kuma tsayar da jinin..".
Barisster Hayatu murya araunane k'asa k'asa yace"ina wuk'ar take..?".
Doctor Nazeer yace"tana nan na adanata wani wuri domin so nake idan hankali ya kwanta inyi bincike akan wuk'ar..".

"Da k'yau abokina".

Su Aunty Maijiddah sukayi masa caaaaaa da tambayoyinsu tace"Ummi zata warke..?".

"An tsaida jinin Ummina".Cewar Zainab tana kuka.

Bintalo tace"an samu nasarar cire wuk'ar acikinta likita..!?".

Doctor Nazeer ya rik'e kansa saboda wani irin sara masa dayake yi arayuwarsa ya tsani yaga mace tana kuka musamman wadda yake mutuwar so wato Zainab,ayau ganin da yayi mata yaji wani irin wutar soyayyarta sai k'ara ruruwa takeyi a k'ok'on zuciyarsa.

Ganin ya dafe kai yasa barisster Hayatu ya rik'oshi yana kallonsu yace"doctor bayason damuwa yana cikin tashin hankali duk tambayoyinku anan shine anyi nasarar cire wuk'ar acikinta an tsaida jinin dake zuba ajikinta muna sa ran da izinin ubangiji zata warke".

Dukansu sunyi farin ciki fiyeda misali domin kallon fuskarsu kawai zakayi ka tabbatar da haka,DPO Usman da yaransa sai jinjina al'amarin aransu sukeyi cikeda tsananin jimami da alhini.
Aranar akace ba'a buk'atar kowa wurin Ummi Aziza sai barisster Hayatu haka dai su Zainab suka dawo gida cikeda tsananin damuwa da fargabar abinda zai faru da Umminsu!.

************************
Da tsakar dare asanadiyyar damuwa da k'uncin dake wanze a k'ok'on zuk'antansu babu wadda ta runtsa,kowace Allah Allah takeyi gari ya waye taje taga halin da Ummi ke ciki ko zata samu natsuwa da sa'ida arayuwarta.
Gari na waye dak'yar suka daure sukayi breakfast atare but saboda babu dad'in rai basu ci abincin kirki ba,ahaka dai suka cuccusa abincin cikin baki babu ko dad'i acewarsu sannan suka shirya tsab suna fitowa suka ci karo da Labbo driver driven barisster Hayatu yazo d'aukarsu,gaggaisawa sukayi atsakaninsu yayi musu jaje tareda tada motar suka nufi hanyar zuwa asibitin doctor Nazeer.

*************************
Labbo driver yana parkerwa kowaccesu agaggauce ta fito daga cikin motar suka jera atare tareda d'unguma zuwa d'akin da aka kwantar da Ummi,awaje suka had'u da barisster Hayatu zaune saman bench da sauri Aunty Maijiddah tace"daddyn Jawaheer ya jikin Ummi?".
Sauran gaidashi sukayi ya amsa musu cikin yanayin natsuwa nan suka ji hankalinsu ya k'ara kwanciya.
Barisster Hayatu ya nuna musu wurin zama suka zazzauna akai sannan yaja gwauron numfashi yace"Jiddanah taji sauk'i yanzu hakama goran ruwan da aka sanya mata ya kusan k'arewa".

LAHANIWhere stories live. Discover now