LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 11*

Su Jawaheer ne dake cikin parlour suna k'irinniya da wasarsu itada k'anenta Mahafuz da taji ana doko sallama ta taso ahankali ta bud'e k'ofar, ganin baba maigadi ne yasa ta saki murmushinta ta gaidashi ya amsa cikin fara'a da nishad'i aransa yace"Jawaheer ina Abbanki...?"."Yana cikin d'akinsa..".
baba maigadi yace"je kice masa yayi bak'i..".Jawaheer ta dubesa cikin matuk'ar ladabi tace"to baba".Tana ida maganarta taja k'afafunta ta nufi hanyar zuwa room d'in mahaifinta.
alokacin ne baba maigadi ya maida k'ofar parlour ya rufe yayi tsaye yana jiran fitowar yah Hayatu, babu dad'ewa saiga yah Hayatu ya fito waje ganin baba maigadi ne yasa suka gaggaisa cikin mutunci da girmamawa sannan yace masa"baba lafiya dai kake nemana..?".
"bani nake nemanka bak'i ne suka zo wurinka".
barisster Hayatu ya dinga maimaita maganar a zuciyarsa can yace"bak'i bak'i kuma ina suke..?".

"suna saman teburina zaune".

"to yanzu abinda za'ayi kaje ka jagorancesu har cikin parlourn saukar da bak'i ni kuma bari in cewa Zainab ta kawo musu ruwa..".

"shikenan Oga babu damuwa".

Hayatu ya juya ya koma cikin d'akin Aunty Maijiddah ya gaya mata yayi bak'i ta turo masa Zainab ta kawo musu ruwa, nuna masa tayi babu matsala zata aikata abinda yace sannan ya chanza tufafinsa masu k'yau ya tunkari parlourn saukar da bak'i, koda yaje tuntuni baba maigadi ya kaisu Hudairu cikin parlourn suna zazzauna suna tab'a fira atsakaninsu.

Da sallama abakinsa ya shiga ciki suka amsa masa fuskarsu asake kai tsaye yaje ya zaune saman kujerar dake fuskantar fuskokinsu, ganinsu Hudairu ne yasa annurin dake shimfid'e afuskarsa ya gushe nan yaji wani irin tuk'uk'in b'acin rai da tsananin bak'in ciki ya mamaye sassan jikinsa amma dayake baisan abinda ya kawosu ba dole ya sassauta fuska, parlourn ya d'auki shiru na mintuna k'alilan can saiga Zainab ta shigo tsakiyar parlourn hannunta rik'e da tire shak'e da kayan marmari ta iso gabansu tareda sunkuyawa cikin matuk'ar karamci da mutunci ta dire agabansu,sannan ta tsiyaya musu lemon juice akofi ta ajiye har ta mik'e tsaye d'agowar da zatayi idanunta suka fad'a cikin na Hudairu d'immmmm taji gabanta ya fad'i zuciyarta ta karaya nan take tayi kicin kicin da fuskarta cikeda tsananin haushinsu jikinta yana k'yarrrma da makarkatar tsoro tamkar mai jin sanyi yayinda wani irin tururin d'aci da tsantsar zogi zuciyarta keyi dak'yar ta bud'i baki tace"mi..ye..ya..kawoku...gi..dan..nan...!?".
Hudairu yayi wani irin murmushin mugunta yace"so muke ki koma gidan mijinki...!".

Agigice Zainab tace"mi!Shi Laweezin ne ya aikoku saboda in koma gidansa..?".
"to kuje ku gaya masa cewar bani bashi na rabudashi kamar yadda na rabuda cikin mahaifiyata..!".
"saboda haka tun wuri yaje ya nemi matar aure..!".Tana k'arashe maganarta taja k'afafunta ta fice daga cikin parlour ahargitse cikeda d'acin rai da k'unar zuciya yayinda hawayen k'unci da tsantsar takaicin auren Laweezi suka dinga sintiri afuskarta, cikin k'wayar idanunta har jiri takeji dak'yar ta dinga dafa bango har ta k'arasa room d'in Aunty Maijiddah.

Su Hudairu lemon juice d'in kawai suka iya sha sannan suka dinga kallon fuskar barisster Hayatu suna aiyana abubuwa da dama cikin zuciyarsu.

Hudairu ne yayi gyaran muryarsa cikin k'arfin hali yace"barisster wurinka muka zo".

"ina saurarenka.".

"dama munzo ne mu baka hak'uri akan irin abubuwan da suka faru tsakanin Laweezi da Zainab adalilin walak'ancin da yayi mata, wanda ya kaisu ga samun sab'ani da ita har ya saketa sannan kuma yanzu ya hak'ura yace ya maidata d'akinta...!".

LAHANIWhere stories live. Discover now