LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 44*

Ummi Aziza tana shiga cikin d'akin Zainab ta hangota kwance rigiggine tana tunani,Ummi ta k'araso wurinta tareda dafa kafad'arta tace"Zainab tunanin mi kikeyi ne..?".
Firgigit Zeey ta dawo cikin natsuwarta tana murmushi tace"ba komai Ummi kawai dai kaina ne yakeyimin ciwo..".Cikin tausayawa Ummi Aziza ta langwab'e kai tace"assha Zainab tashi kisha magani..".
Zainab tace"ai nasha Ummi"."To karki damu zakiji sauk'i kinji.."."Uhmm Ummi..".
Ummi Aziza ta musk'uta tace"kizo babanki yanason magana dake yanzu".
Zainab tace"to Ummi".
"sai kin fito".Cewar Ummi tana tunkari k'ofar fita daga cikin d'akin tana isa ta fice daga ciki.

Bisaga dole Zainab ta tashi zaune tana dafe goshinta tareda yamutsa fuska tace"ko kiran miye baba yakeyimin..?".Jikin asab'ule ta mik'e tsaye ta fad'a cikin bathroom ta wanko bakinta da fuska sannan ta zura hijabi ajikinta ta nufi room d'insu Ummi Aziza.

Tana shiga ta iskesu baba Sa'idu zazzaune saman tabarma Zainab ta samu wuri agefe ta zauna sudai kallonta kawai sukeyi cikin so da k'auna.
Murya asanyaye tace"gani baba".

Baba Sa'idu ya numfasa yace"akan maganar wannan yaro d'an gidan marigayi Haruna Mai dawaki nayi bincike iya bincike akansa na gano ba yaron kirki bane saboda haka amatsayina na mahaifinki ina baki shawara akan ki fita sha'aninsa....!".
"domin bazan tab'a amincewa da aurenki dashi ba saboda duk uba nagari zai so 'yarsa ta auri miji nagari mai nagarta..".
Da sauri Zainab ta d'ago fuska ta kalli mahaifinta yayinda ruwan hawaye suka cika taff cikin k'wayar idanunta jikinta yana rawa race"baba idan bakwa son in auri Laweezi waye kukeson ku aura mini..?".
"bayan na riga na mallaka masa zuciyata na tsumduma akogin soyayyarsa..!".

Ummi Aziza ta harareta tace"tunda wuri ki mance da wani Laweezi arayuwarki domin bazamu tab'a yarda ki auresa ba..!..".

Baba Sa'idu yaja dogon numfashi yace"Zainab ita rayuwa da kike gani ba komai mutum yakeso ba yake samunsa ba amatsayinmu na iyayenki mune yafi dacewa da cancantar mu zab'a miki abokin rayuwa nagari mai kirki wanda ko bayan ranmu zai rik'eki amana,amma ke na lura zuciyarki ta mutu akan so wanda bakisan ainahin halayensa ba bakisan miyasa mutane ke aibantashi ba suna cewar bayada kirki..!".
"Saboda haka idan yaron nan likita yazo zan bashi aurenki domin bazan so ki fad'a cikin halaka ba..!".

Sirarrun hawayen takaici da rashin son doctor Nazeer ne suka wanke mata fuska numfashin bak'in ciki ta saukar race"na rok'eka baba ka rufa mini asiri ka barni in auri zab'in raina wlh duk wasu k'ananan maganganu da akeyi akansa k'arya ne kasan idan mutane sukaga ubangiji ya d'aukaka mutum k'ok'arin sukeyi subi duk wata hanyar da zasu bi su kushesa suna masa hassada..!".

Ummi Aziza ta daka mata tsawa tace"dallah ki rufewa mutane baki! Zainab miyasa bakida kunya wai babanki yace bazaki aureshi ba amma ke kina k'ok'arin yi masa gardama..!".

Zainab ta dinga yarfa hannuwa tace"ba haka bane Ummi inason Laweezi soyayyar da ban tab'a zaton zanyiwa wani d'a namiji ba..!".

"tashi ki fice daga cikin d'akin nan tunda rashin kunya zakiyi mana aure dai babu fashi atsakaninki da likita..!".

Zainab ta mik'e tsaye jiki asanyaye tace"Ummi kuyi hak'uri so...................!".

Kafin ta k'arashe maganarta Ummi Aziza ta katse mata hanzari tace"ki fita banason jin maganar komai abakinki...!".

LAHANIWhere stories live. Discover now