LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*RIGIJI GABJI,RANAR KUKE JIRA YAU GATA TAZO MASOYA*

*MARUBUCIYAR NAN TAKU WADDA TA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI INGANTATTU MASU TSUMA ZUCIYAR ME KARATU WATO HASSANA D'AN LARABAWA ,MARUBUCIYAR*:

SANADIN HOTO

     DA

HASSANA DA HUDSAINA

*YAU TA SAKE DAWO MUKU DA SABON LITTAFINTA WANDA YA ZARCE DUK LITATTAFANTA A KOMAI WATO CIN AMANAR RUHI,KAI DAGA JIN SUNAN KUN SAN AKWAI TAFKA TAFKA DA K'ULLE K'ULLE ,AMMA ZATA WARWARE MUKU K'ULLIN DA ZARAR KUN BIYA 200 DOMIN SAMUN LITTAFIN,KAR KU BARI YA WUCEKU ,DOMIN WANI IRIN LABARI NE DA BAKU TAB'A CIN KARO DA IRINSA KO MAI KAMARSA BA,FAD'AKARWA ,NISHAD'ANTARWA,ILIMANTARWA,TAUSAYI,DA SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA ,TARE DA WATA IRIN CIN AMANA DA BAKU TAB'A RISKAR IRINTA BA,KU DAI KU HANZARTA NEMAN MARUBUCIYAR DOMIN KU SIYA KU KARANTA AKAN KUD'I K'ALILAN 200*

*ZAKU IYA NEMANATA AKAN LAMBARTA KAMAR HAKA,08080049548 DAGA NAN ZATA GAYA MUKU YADDA ZAKU BIYA KUD'IN ,KU DAI KU HANZARTA KAR AYI BABU KU ,KU TUNA DA SUNAN LITTAFIN*

CIN AMANAR RUHI

*NA MARUBUCIYAR KU HASSANA D'AN LARABAWA*🥰🥰🥰🥰

*PAGE 56*

Suna dawowa gidansu suka cire tufafinsu suka fad'a bathroom atare suna wanka cikin tsabtacciyar soyayya da zallar k'auna,idan ta cud'anyashi haka shima zai cud'anyata haka suka cigaba dayi har suka gama wankan suka fito daga ciki hannunsu mak'ale da juna, kowanensu zuciyarsa cike take mak'il da soyayyar abokin zamansa musamman Hajara data rayuwa da k'aunarsa tun kafin takai minzalin haka.

*************************
*BAYAN WATA D'AYA*
Hajara ce na hango kitchen tana kichaniyar had'a breakfast doctor Nazeer yana tayata can naga ta fara toshe hanci tana yunk'urin amai,lura da hakan da yayi ne ya dubeta cikin tsantsar kulawa yace"wifey lafiya kike toshe hanci..?".

Hajara ta yamutsa fuska kamar zatayi kuka tace"hubby bana son k'amshin k'wai ne ji nakeyi zuciyata na tashi".

"je d'aki ki kwanta bari k'arasa breakfast d'in".

Hajara ta girgiza kanta tace"haba my doctor ya za'ayi in barka da aiki inje in kwanta wannan aida kunya".

Doctor Nazeer ya fuskanceta fuska d'auke da fara'a yace"lalura ce ba abin kunya bane saboda haka kije ki jirani aparlour".

"gaskiya ni bazan iya barinka kai kada........".Kafin ta k'arasa maganarta ya katse mata hanzari cikeda tsananin tausayi domin ya lura kamar tana d'auke da ciki yace"banason gardama baby ki koma parlour nace..".
"kayi hak'uri hubby".Har ta juya zata fice kamar jira aman yakeyi yayo mata suk'ut ta fara kwararashi abakin kitchen d'in,kakarin amanta ne ya jiyo muryarsa na rawa ya iso wurinta ta rik'eta harta kammala amayarda da dukkan abinda taci numfashi kawai take saukewa agalabance,shi kuma sai sannu yake jera mata ganin aman ya tsaya yasa Nazeer ya d'ebo ruwa ya wanke mata jiki ta kurkure bakinta,sungumarta yayi yakai parlour ya kwantar da ita sannan yaje ya ciro mata wasu tufafin ya zura mata ajiki duk da bataso hakan ba amma babu yadda ta iya.
Daya gama shiryata yaje ya kwashe aman yayi amfani da mopper ya goge wurin tasss, sannan yaje ya zubar awani k'ebantaccen wuri dawowa kitchen yayi ya ida breakfast d'in ya kwasa yakai a dinning table ya jajjerasu cikin tsari da gwaninta kamar mace.

LAHANIWhere stories live. Discover now