LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 20*

Ganin yadda barisster Hayatu yak'i bashi amsar tambayarsa yasa yaji hankalinsa yayi k'ololuwar tashi tsananin fargaba da zullumi ne ya bayyana k'arara afuskarsa,dak'yar ya sake bud'a baki yace"haba barisster tun d'azu inata tambayarka kayi shiru ka k'yaleni..!".
"please ka sanarmin ainahin abinda ya sameta ko zan samu sukuni azuciyata...!".
"wallahi ayanzu ji nakeyi kamar zuciyata zata fashe akan tarin damuwa da tsantsar fargabar irin kalaman da zasu fito daga cikin bakinka..!".
Jikin barisster Hayatu yayi matuk'ar sanyi yace"ai ya zamo dole in gaya maka gaskiyar abinda yake faruwa domin abokin kuka shi ake gayawa mutuwa..!".

"fad'amin ina saurarenka..!".

Cikeda tsananin d'acin rai da k'unar zuciya yace"Zainab ta b'ace..!".
Azabure Nazeer yace"mi..!?".

"nace maka Zainab ta b'ace tun jiya da safe ta fita bata dawo gida ba..!".

Doctor Nazeer yaji wani irin sihirtaccen bak'in ciki da tsantsar tashin hankali ya ziyarcesa alokacin ne idanunsa suka chanza launi asanadiyyar damuwa da gushewar natsuwa yace masa"Ina lillahi wa ina ilaihirraji'una..!".
  "Hayatu ta yaya hakan ya faru..!?".
"ina taje ne aka saceta..!?".
"ziyara ta fita gidan k'awarta Samrat to ta samu damar ganin k'awarta akan hanyar dawowa zuwa gida ne aka samu damar saceta..!".

Doctor Nazeer jugum cikin matuk'ar dogon nazari ya saukar da numfashi yace"anyah wannan abin babu wata mak'ark'ashiya a k'asa barisster..!?".

barisster Hayatu ya musk'uta cikeda matuk'ar zullumi yace"nima haka nake tunani Nazeer..!".
"saboda akwanakin baya Laweezi ya turo abokansa wurina akan in rarrashi Zainab ta dawo gidansa shine nak'i amincewa da zancensu...!".
  "domin Zainab ta nunamin bata k'aunarsa kwata kwata azuciyarsa shiyasa ban goyi bayan ta koma ta cigaba da rayuwar bak'in ciki agidansa ba..!".

  "hmmm amma kana ganin wannan hukuncin daka zartar akan Zainab hakan bazai sanya Laweezi ya d'auki babban mataki akanta ba..!?".

"mataki! Kai atunaninka Laweezi zai iya d'aukar wani irin mataki akan Zainab...!?".
"bayan ya cutar da rayuwarta tareda tarwatsa mata farin cikinta...!".

"tabbas idan ya samu dama zai iya sanya a d'auketa Hayatu domin yaron nan da kake gani bayada hankali baisan inda mutunci yabi ba bale yabi bayansa...!".

"to yanzu ya za'ayi ni kaina tunani duk ya rikice k'wak'walwata duk ta daina aiki..!".

Doctor Nazeer yace"nidai shawarata gareka shine kayi k'ok'ari ka fara bincike akan Laweezi saboda zai iya cutar da rayuwarta bamuda labari..!".
"zan fara bincike akansa doctor Nazeer..!".

"ya dace kam kafin komai ya ricchab'e agareku..!".

  barisster Hayatu ya mere baki cikeda tsananin damuwa yace"zan fara bincike akansa asirrance kafin in mik'ashi kotu..!".
"OK ubangiji yasa adace..!".

"Amin".
Cigaba da tattaunawarsu sukayi akan yadda zasu gano ainahin wa nene Laweezi wace irin sana'a ce yake aiwatarwa wadda take kawo masa mak'udan kud'ad'e ta ko'ina, da wane irin mutane ne yake huld'a su waye suka fi kowa kusanci dashi..!?..

**********************
*BAYAN KWANA BIYAR*
Aunty Maijiddah duk ta zabge ta rame ta fice cikin hayyacinta kallo d'aya zakayi mata ka gane bata cikin walwala da tsananin farin ciki arayuwa, saboda rashin sanin inda Zainab take duk ya hana mata sukuni ko tsakar dare bata iya runtsawa asanadiyyar bak'in ciki da zullumi daya mamaye ruhi da b'argon jikinta.
yah Hayatu ne ke rarrashinta da nasihu masu dad'i domin ya tsani ya ganta cikin matuk'ar damuwa, dak'yar yake samu ya shawo kanta tana rage yawan saka damuwa da bak'in ciki azuciyarta wata rana har fad'a cikin lallashi yakeyi mata saboda bayason asanadiyyar b'acin rai ta kamu da hawan jini.!

LAHANIWhere stories live. Discover now