LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 47*

Haka dai Nazeer ya cigaba da cin abincinsa dak'yar yaci rabin plate sannan ya ture sauran yasha ruwa,kallon mahaifiyarsa yayi yace"mommy na k'oshi".Hajiya Khausar ta tashi tsaye d'auke da tiren ahannunta tace"okay son bari inje in k'arasa ayyukana i hope dai babu abinda kake buk'ata..?".
"babu mom idan na buk'aci wani abu zanzo da kaina kona kiraki awaya".
"to shikenan son ahuta lafiya".
kai tsaye hajiya Khausar ta fito daga cikin room d'insa ta rufo masa k'ofar d'aki,direct kitchen ta wuce da tiren d'in ahannunta domin ta tsabtacesu.
_________________________

Da tsakar dare misalin k'arfe tara 9:00pm Ummi Aziza suna zaune saman tabarma suna shan sansanyar iskar dake kad'awa kad'an kad'an musamman da tsakiyar dare mai dad'in gaske,sai firarsu sukeyi cikin nishad'i da kwanciyar hankali yayinda Zainab tana can cikin d'akinta ta k'unshe ta d'auki damuwa da bak'in cikin rashin son doctor Nazeer ta d'aura azuciyarta.

Suna tsaka da fira baba Sa'idu ya dubi fuskar Ummi Aziza cikeda tsananin murna yace mata"Aziza".
"na'am baban Zainabu".
Baba Sa'idu yace"gobe idan ubangiji ya yarda magabatan likita zasu zo gidan nan neman auren Zainabu saboda haka ki kwana da shirin aikace-aikace agobe".
Ummi Aziza taji dad'i azuciyarta yayinda hakan ya bayyana akan fuskarta tace"to maigida abin yayi k'yawo matuk'a ubangiji Allah ya kaimu gobe lafiya".
"Amin ya rabbi".
"ina Zainabun take ne Aziza?".
"tana cikin d'akinta".
"kiramin ita inason inji ta bakinta".
Ummi Aziza ta tashi tsaye batare data sake magana ba ta tunkari hanyar zuwa room d'in Zainabu,tana isa bakin k'ofar taji ta akulle tsaye tayi ta fara knocking the door Zainab dake rakub'e saman gado rungume da pillow tanata zubar da kwallar soyayyar Laweezi taji ana buga k'ofar d'akinta.
saida Ummi Aziza tayita bugawa sannan dak'yar Zainab ta mik'e tsaye ta wanko fuska tareda gyara fuskarta domin kada afahimci tayi kuka tazo ta bud'e mata k'ofar, lokacin da sukayi ido biyu da juna Ummi Aziza ta tsura mata idanu tana nazarinta can tace"Zainab tun d'azu ina tsaye ina buga k'ofa kink'i bud'ewa mi kikeyi ne?".
Zainab tayi murmushin yak'e tace"barci nakeyi Ummi shiyasa banji ya ba".
Ummi Aziza ba domin ta yarda da zancenta ba tace"to naji miyasa idanuwanki sukayi ja ne".
Zainab ta murza idanunta tace"wani abu ne ya fad'amin cikin idanu".
cikin matuk'ar tausayawa mahaifiyarta tace"ayyah sannu kinji".
"yauwa".
"Uhmmm idan kin gama abinda kikeyi kizo mahaifinki yana son ganinki".
Dumm taji gabanta ya fad'i dayake ta iya siyasa saita fad'ad'a fuskarta da murmushi tace"to gani nan zuwa".
Ummi Aziza ta juya ta koma wurin baba Sa'idu suka cigaba da fira yayinda Zainab ta koma d'akinta ta shafa kwalli a idonta domin su rage ja, sannan ta zuro hijabinta tareda jawo k'ofar d'akinta ta tunkari hanyar da zata sadata da iyayenta.

Tun daga nesa ta hangosu zazzaune saman tabarma kallo d'aya tayi ta gane suna cikin kwanciyar hankali,da sallama ta k'araso suka amsa mata cikin jin dad'i da k'auna saita samu gefe dasu ta zauna murya atausashe tace"gani baba".
"na ganki".Cewar baba Sa'idu yana nazarinta.

Ankai tsawon mintuna shiru kakeji babu mai magana atsakaninsu can daga baya baba Sa'idu ya katse shirun ta hanyar cewa"Zainabu".
"na'am baba".

"dama dalilin dayasa na aika Umminki ta kiraki domin in sanar dake agobe idan ubangiji yasa muna masu numfashi likita zai turo magabatansa gidan nan asa ranar aurenku, shiyasa nace bari in gaya miki kada kiji maganar daga sama sannan ki sani ba ke kad'aice zai aura ba iyayensa sun umurcesa daya auri 'yar uwarsa".
"Saboda haka abinda nakeso dake duk halin da kika tsinci kanki aduniya to ki kasance mai hak'uri tareda rungumar k'addararki hannu bibbiyu".
Ummi Aziza ta k'ara da cewa"Zainab kiyi hak'uri ki daure kiyiwa mahaifinki biyayya k'aunarki ce yasa bazamu iya barin ki auri zab'inki ba ina ji ajikina aurenki da likita alkhairi ne".
Wani irin d'aci da k'unci ne ya mamaye zuciyar Zainabu yayinda ruwan hawaye suka cika taff cikin idanunta, dak'yar take iya jan numfashi saboda nauyin da k'irjinta yayi mata bud'ar bakinta tace"Baba Ummi nasan abinda kuke guje mini wato auren nadama amma idan kukayi duba da la'akarin cewa har yanzu zargin Laweezi akeyi,gaba d'aya mutanen dake tuhumarsa da aikata mugayen ayyuka basuda wata k'wak'k'warar shaida akan abinda suke zarginsa, saboda haka na rok'eku ku rabuda maganar mutane ku barni in auresa wallahi shi kad'ai ne namijin da nake burin aura arayuwata..!".Ta ida zancenta cikin raunin zuciya alokacin ne hawayen da take shanyewa suka fara shatata afuskarta.

LAHANIWhere stories live. Discover now