LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 39*

Hajara ta isko momy kishingid'e saman pillow yayinda take d'an tab'a gyangyad'i alamar barci takeji,jin motsin shigowar mutum ne yasa ta farfad'o tace"Hajara kin kai masa abincin..?".
kanta noce ak'asa tace"eh momy nakai masa..".
"amma miyasa baki tsaya kika tayasa fira ba kika dawo..?".
Hajara ta rausayar da kanta cikin rashin kuzari tace"aiki yakeyi shiyasa na fito domin in barshi yayi aikinsa cikin natsuwa..!".
momy ta jijjiga kanta alamar gamsuwa tace"kin ko k'yauta sosai..".
"yaushe zaki tafi gida ko sai daddyn Nazeer ya dawo ne..?".
"idan ya dawo da wuri shizai kaini gida idan kuma bai dawo ba keke napep zan tara..!".
"OK ba matsala d'iyar albarka..".

*WA NENE DOCTOR NAZEER*
Asalin doctor Nazeer d'a ne ga Alhaji Ahmed Mai k'arfe da hajiya Khausar,mahaifinsa Alhaji Ahmed Mai k'arfe hamshak'in mai arzik'i ne wanda ya shahara aharakar saida mototi da mashuna, mutum ne mai tsananin taimako da k'aunar talakawa akowane lokaci cikin bada gudunmuwa yake amasallatu da makarantun islamiya domin ganin addinin musulunci ya cigaba,yanada sauk'in kai da d'aukar shi ba kowa bane idan ya shiga cikin jama'a hakama matarsa Khausar mace ce ma'abociyar son taimako da k'yautatawa marasa k'arfi, duk da ubangiji ya d'aukaka mijinta haka baisa ta raina mutane ba ko tayiwa matan talakawa girman kai ba.
Asalin sunan Mai k'arfe ya samo tushe ne daga mahaifin Alhaji Ahmed Mai k'arfe wato Malam Salmanu Mai k'arfe da Inna Meri, babansa sana'ar k'ere k'ere yakeyi yana amfani da k'arafuna iri iri daban daban wurin sarrafasu su koma kayayyakin amfani kamar lauje,tsinke,mashi dadai sauransu.
da sana'ar ce yake samun 'yan kud'ad'en dazai rufawa kansa asiri da kulawa da iyalansa, su biyu ne iyayensu suka haifa daga Ahmed sai k'anwarsa Baraka(mahaifiyar Hajara) sun taso cikin so da tsantsar rufin asiri ahannunsu mahaifinsu.
babu inda Malam Salmanu baya shiga neman kud'i domin ganin yaransa sunyi karatu mai zurfi musamman Ahmed dayake namiji sun d'auki buri na duniya sun d'ora akansa,shima Ahmed idan ya dawo daga school yakan je har rumfar mak'era wajen mahaifinsa yana taimaka masa da wasu ayyukan, tun bai koya komai ba har yazo ya iya wasu abubuwa da dama ganin ya k'ware ne yasa idan aka basu hutu mahaifinsa yabar masa ayyuka ya dinga tafiyar dasu yadda ya kamata.
Rayuwar gidan Malam Salmanu abar sha'awa ce domin suna tafiyar da ita yadda ya dace gwargwado sunfi k'arfin abinda zasu ci suyi sutura,su Inna Meri tsaye suke akan tarbiyar 'ya'yansu domin ganin yaran sun taso cikin matuk'ar ladabi da girmama na gaba garesu, shiyasa rayuwarsu Ahmed take daban da sauran yaran unguwarsu saboda komai nasu cikin tunani da tarbiya suke yinsa.
Haka rayuwarsu take gudana har Ahmed ya kammala secondary school result d'insa ya fito wani baban abokin abokinsa ya samo musu admission shida yaronsa a university, yayinda Baraka take SS1 cikin haka ta fara samun samari masu cewa suna sonta dayake ita mai tarbiya ce ko kulasu batayi saboda ta fahimta cewar wasu samari daga cewa suna sonki idan kuka fara soyayya zuwa wani lokaci bayan kin shak'u dashi zai iya bijiro miki da buk'atarsa gareki, idan kin amince to rayuwarki tagayyara kuma kin halaka idan baki amince ba to tun daga wannan ranar zaku iya rabuwa dashi.

_Allah ubangiji yayi mana tsari daga sharrin *SAMARIN SHAHO*._

Ahmed yana 300 level a university alokacin tuni Baraka ta kammala secondary school ta samu miji mai suna Abdulbasi,tana gama makaranta babu b'ata lokaci aka aurar da ita ga Abdulbasi dayake yaron yanada abin hannunsa ko gidan daya gina to ba shakka had'ad'd'en gida ne wanda ya amsa sunansa tsararren gida.

LAHANIWhere stories live. Discover now