LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 32*

Agabansu suna ji suna gani aka zartawa Yunusa hukuncin dukkanin abubuwan daya sata saiya biya kud'ad'en mutane ko kuma akaishi gidan yari agark'ame, nan take Sa'idu ya tsoma bakinsa ya rok'i alfarmar akan ayi musu lamuni zasu sayarda d'an abinda sukedashi su biya mutane kud'ad'ensu, dayake Mallam Jauro yana jin nauyi da kunyarsa nan take ya amince da buk'atarsa ya sallami mutane tareda umurtar matasan samarin su kwance Yunusa, babu gardama suka kwanceshi.

bayan sun kwanceshi ne ya nufi hanyar zuwa gida yayinda alokacin ne Sa'idu ya taimakawa baffa Zubairu ya mik'e tsaye saboda ya afka cikin tsananin d'acin rai da k'uncin rayuwa, da taimakon Sa'idu baffa ya iso gida lafiya domin dafe kan saitin k'irjinsa yayi saboda wani irin azababben zafi da wurin yakeyi masa, suna isowa tsakiyar filin gidan Inna Wuro ta taso tazo wurin baffa batare data lura da irin yanayin dayake ciki ba ta rufeshi da ruwan masifa tana koro masa bayanin abinda Yunusa yayiwa d'iyarta Lantana.
Hmmm rashin sani yafi dare duhu da Inna Wuro tasan abinda maganganunta zasu jawo da batayi gigin fad'a ba, saboda tana k'arashe bobotaiyanta kawai suka ga baffa Zubairu ya fad'i k'asa rikchamm!Tashin hankali kenan da gudu Sa'idu da Inna A'i suka ruk'unk'umeshi cikeda tsananin fargaba da tsinkewar zuciya rusar kukan bak'in ciki kawai Inna keyi tana shassheka yayinda Sa'idu yaji kasa kuka hawayensa sun k'afe asanadiyyar ya fad'a cikin wani irin fitinannen k'unci da uk'ubar rayuwa.
Jijjigarsa Inna A'i keyi tana rok'onsa akan ya tashi zaune kada ya tafi ya barta cikin wannan duniyar mai tattare da bak'in ciki da k'addarorin rayuwa, ganin irin halin da iyalan baffa suka shiga yasa nadama da dana sani ta d'arsu azuciyar Inna Wuro itama Lanti kwallar zallar tausayinsu ne suka dinga kwaranya akuncinta domin bata fatar wani mugun abu ya samu mahaifin masoyinta.
cikin matuk'ar dauriya da k'arfin hali Inna Wuro ta nufi randa jiki asanyaye ta d'ebo ruwa masu sanyi cikin madaidaiciyar roba ta kawo ta watsawa baffa Zubairu ajiki, sai alokacin ne su Sa'idu suka tuna da idan mutum ya some ruwa ake watsa masa,tunda aka watsa masa ruwan sanyi har bayan tsawon mintuna talatin baffa ko matsawa baiyi ba balantana susa ran zai iya farfad'owa daga suman da yayi, kowanensu ka kalli fuskarsa k'unshe take da tarin damuwa da tsantsar fargabar irin abinda zai biyo baya domin ayanzu zuk'atansu sun afka cikin zullumi da tunani!.

Sun dad'e sosai zaman jiran farfad'owar baffa amma shiru shiru har yanzu adalilin haka ne Inna A'i ta k'ara volume d'in kukanta cikin bak'in ciki da tsantsar damuwa!Sa'idu ya rasa yadda zaiyi ya lallasheta saboda shima damuwar dake cunkushe azuciyarsa tafi k'arfin k'wak'walwarsa jiki asab'ule ya duk'a har k'asa ya saita kunnensa adaidai bakin baffa domin yaji ko yana fitarda numfashi, ya jima duk'e amma baiji yana fitar da numfashi ba ko alamun akwai rai atattare dashi ba.
cikin wani irin mayuwacin rad'ad'i Sa'idu ya rungume gangar jikin baffa alokacin ne hawayen da suka k'i fitowa suka samu sararin sintiri afuskarsa kalmar ina lillahi wa ina ilaihirraji'una! Kawai yaketa maimaitawa afili arikice su Inna Wuro suke kallonsa domin suji abinda zai fad'a can ya kallesu da idanunsa jawur kamar garwashi yace" saidai muyi hak'uri Inna ubangijin daya bamu baffa ya amshi ran abinsa..!".

"ina lillahi wa inna illaihirraji'una..!".Inna A'i ta fad'a tareda k'yallara k'ara da gigitacciyar kuwwa da k'arfi ta fad'i k'asa ta some!.

Arikice Sa'idu ya koma wurinta yana saki rikitaccen kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk wanda ya kalleshi alokacin saiya bashi tausayi domin jikinsa duk ya game da d'umi d'umi alokacin jin yakeyi gaba d'aya duniyar ta fice masa arai, alal hak'ik'a mutuwa tana tsantsar ciwo azuciya hardai idan mutum ya rasa iyayensa aduniya saboda sune suka fi kowa kusanci da k'aunar yaronsu, babu yadda muka iya ne kowane irin mahaluki aduniya baya tab'a tsallake wa'adinsa domin fad'ar ubangiji mabuwayin sarki ce *DUKKAN MAI RAI* saiya d'and'ani zafin mutuwa.

LAHANIWhere stories live. Discover now