LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 59*

Zainab ta maida hankalinta kacokam akan handout d'inta tana nazari saiga Laweezi ya shigo rik'e da briefcase ahannu, laptop d'insa tana a d'ayan hannunsa ta gabanta ya gifta zai wuce tayi masa sannu da zuwa,ko amsawa baiyi ba yayi tafiyarsa d'akinsa abin yayi mata ciwo azuciya matuk'a amma babu yadda zatayi sai hak'uri.
Cigaba da karatunta tayi tamkar batada wata damuwa aranta bayan wani lokaci ta maida handout d'in cikin handbag,ta mik'e tsaye ta kunna TV tana sauraren labaran duniya can k'amshin turarensa ne yayi mata iso ya fito rik'e da k'atanyar leda ahannu yazo ya zauna akan carpet bayan ya lank'washe k'afafunsa,sai alokacin ne giyar girmai kai tabarshi yayi mata magana yace"keee je kitchen ki d'aukomin tire da plate".
"To".Kawai ta iya fad'a ta mik'e ahankali ta nufi hanyar kitchen.
Bata dad'e sosai ba ta dawo da tire da plate ahannunta ta sunkuya k'asa ta ajiye agabansa sannan ta koma mazauninta ta zauna tana cigaba da sauraren labarai.
Laweezi ya bud'e ledar ya juye abinda yake cikinta kaza ce k'atanya sai lemu gora biyu,sai kuma k'unshin kilishi cikin takarda yana gama juyewa yace"Zeey zo kici".
"Na k'oshi".
Laweezi yace"da kika dawo school kinci wani abu ne..?".
"eh na girka macaroni".
Laweezi yaja bakinsa ya tsuke ya fara cin kazar ayangace yana shan ruwan lemu,haka dai ya cigaba da ci har ya k'oshi amma dayake kazar k'atanya ce ko rabi bai ci ba ya saka sauran cikin fridge saboda kada su lalace.
Dawowa wurinta yayi yana sakin gyashi alamar ya k'oshi yace"idan kinji yunwa kije kici ya school d'in..?".
"Lafiya k'alau".
"Ina fatar babu wata matsala ko?Idan akwai wani abu daya shige miki duhu kar kiji komai ki fad'amin koda wani lecturer ne keson takura miki zaki iya sanarmin".
Zainab ta yatsine fuska cikin gundura da surutunsa tace"babu saboda ko yau ne fa na koma school d'in taya za'ayi ace har na samu lecturer dazai takuramin".
Laweezi ya nisa yace"kuma fa haka ne Angel".

*************************
Tun ranar da doctor Nazeer ya gano matarsa Hajara tana d'auke da cikinsa ya d'auki wata irin kulawa da soyayyar duniya ya k'wallafa akan cikin,itama wani irin tarairaya da kulawa yake bata abin har mamaki yake bata yadda yake nuna k'auna da tsantsar soyayyar gaskiya.
Duk dayake kulawar dayake bata yana sakata cikin nishad'i da annushuwa mara misali,bugu da k'ari dukkan ayyukan gida idan yana nan shi yakeyi mata idan kuwa yana hospital zai turo wata mak'wabciyarsu tazo tayi mata komai idan ta gama Hajara ta d'iba mata abinci mai yawa ta kuma yi mata k'yauta.

Doctor Nazeer yana dawowa gida yayi wanka saiya hakimce akan kujera wurin dinning table yayinda Hajara tana zaune gab dashi,da kansa zaiyi serving d'insu su fara cin abinci atsanake suna kammala cin abincin saiya tattara plates d'in da suka b'ata ya wawwankesu tass ya adana cikin kwando.

Idan ya dawo parlour ya iske Hajara kishingid'e akan cushion wurinta ya isa ya zauna tareda tallafo kanta ya aza saman cinyoyi yana shafa kitsonta yace"babyna kinyi k'yawo matuk'a".
Hajara ta saki murmushin shagwab'a tace"My doctor ina wani k'yawo anan?".
"kece bak'ya ganinsa amma ni ina gani domin k'aunar dake tsakaninmu tafi k'arfin wasa".
Hajara ta fesar da iskar bakinta tace"naji yayana yaushe zamuje gidansu hajiya?".
"Ke kam baby kin cikason yawo keda bakida lafiya miyasa zaki takura kanki sai kinje can..?".
Hajara ta langwab'e kai cikin sagarci tace"lafiyata k'alau nikam yaya Nazeer saidai idan bakason kaini ingansu ne".
"Ni harna isa in raba tsakanin d'iya da iyayenta please rufamin asiri idan na samu lokaci zamuje tare mu gansu".
"Ko kaifa yanzu naji magana".
Hancinta yaja yana sakin murmushin dake k'awata fuskarsa yace"rigimammiya kawai".
"affff nice rigimammiya ko?".
"a'a bada ke nake ba".Yace azolaye yana k'unshe dariyarsa.

LAHANIWhere stories live. Discover now