LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 58*

Tun daga ranar da Laweezi ya kafa mata sharad'in ayyukan gida gaba d'aya suka rataya awuyanta,ta rasa mafita da taimakonta domin tun k'arfe biyar na safe take tashi ta fara ayyukan idan akayi sallar asuba taje tayi ta dawo ta cigaba da gudanar da ayyukanta,koda zata k'arasa ayyukan duk ta jigata da galabaita matuk'a sassan jikinta gaba d'aya ciwo sukeyi mata musamman k'afafuwa wad'anda sune jagorar tafiya.
Ayinin ranar haka zata yini barci tana hawayen rashin sabo Allah ya isa taketa surfa masa cikin zuciya yafi shurin masak'i,duk da haka idan ya dawo daga office ba shine zai hana ya nemeta ba adalilin tsabar taurin zuciya da rashin tausayi irin nasa,tana kuka tana komai zai biya buk'atarsa ya shallaketa ya wuce babu ko waiwaye balantana tausayi.
Azabobi iri iri daban daban da uk'ubobin rayuwa Laweezi ya dinga ya gana mata wanda saida ta gwammaci mutuwa akan rayuwa!Kafin sati biyu ya cika duk Zainab ta k'anjame ta jeme fatarta ta sauya asanadiyyar wahaloli da bak'in cikin rayuwa duk wani mai imani idan ya ganta saiya zubar mata da kwalla.
Dak'yar ta samu sati biyu suka cika sannan bodyguards d'insa suka amshi ayyukansu itama kuma ta kwanta rashin lafiya mai tsanani wanda har ya kaita kwanciya a asibiti na tsawon kwana hud'u,anyi mata k'arin ruwa da allurori da yawa kafin asamu jikinta yayi sauk'i ganin ta samu sauk'i ne yasa likita ya sallameta bayan yaja kunnen Laweezi akan ya kulata da ita domin akan wahala da bak'in ciki tana gab da kamuwa da ciwon zuciya!.
Laweezi ya jijjiga kansa alamar to suka tarkato suka dawo gida ya cigaba da gasa mata aya ahannu,alal hak'ik'a duniya makaranta ce domin duk tsiwa da taurin kai irin na Zeey Laweezi ya kaudashi yasa ta zamo salihar k'arfi da yaji..

Cikin kwanakin nan jikin Zainab ya fara dama dama ramarta ta fara gushewa yanzu ma  zaune take k'asan carpet tana yanke farce da razor blade,atamfa ce ajikinta gown wanda ya bayyana surarta d'inkin yayi mata k'yau sosai can taji wayarta tana tsuwa alamar neman agaji da hanzari tayi receiving call batare data dubi sunan dake kan screen ba tace"hello".
Jin muryar Aunty Maijiddah ne yasa ta fahimci itace"Zainab ya kike?".
"lafiya k'alau Aunty ina yarana suke..?".
"Baby Jawaheer tana can islamiya Mahafuz yana goye abayana yana barci".
"to ki shafaminshi idan babyna ta dawo kice momynta na gaidata".
"Suna amsawa Zeey ya hak'uri?".
Zainab taji ruwan hawaye sun cika mata idanu tace"Aunty ina nan inayi ina Ummina..?".
Aunty Maijiddah ta jijjiga kai cikin matuk'ar tausayin k'anwarta tace"ki cigaba da hak'uri wannan auren naki k'addara ce Ummi ta koma gidanta d'azu da safe".
"Allah sarki Auntyna zan cigaba da hak'uri saboda dukkan abinda ya sameni nina jawa kaina..!".Ta fad'a zuciyarta k'unshe take fal da tarin bak'in ciki.
"na fad'a miki ki daina cewar kece kika jawa kanki Zainab aduk lokacin da kika tsinci kanki cikin bak'in ciki da damuwa ki yawaita istigafari da karatun qur'ani kinji da izinin ubangiji zaki samu sauk'i aranki".
"To Aunty Maijiddah nagode sosai ki gaidamin da yaya Hayatu".
"sak'onki zai isa garesa".
"Sai anjima".
"Okay".Tana k'arashe maganarta ta katse wayar tagumi tayi da hannayenta biyu ta rasa wane irin mafita dayace ta nemarwa kanta saboda maganar gaskiya auren Laweezi ya isheta.

Ita kanta ayanzu ta gwammaci ta k'are rayuwarta agidansu da irin wannan auren na bak'in ciki,miyasa tun farko ta bari makahon so ya rufe mata idanu bata tsaya lura da la'akarin cewar Laweezi ba mutumen kirki bane,yanzu gata cikin kud'i taci mai k'yau tasha mai k'yau ta kuma saka irin suturar da takeso amma duk hakan bata cikin farin ciki, hmmm ayanzu ta fahimci cewar kud'i ba sune aure ba ba sune zasu jagoranci rayuwar farin ciki ba, tabbas ta hak'ik'ance har abada bazata daina nadamar aurensa ba domin ya cuceta cutarwa mafi tsanani!.
Ganin tunani da zancen zuci bazai tab'a haifar mata da d'a mai ido ba dole yasa asab'ule cikeda rashin kuzari ta mik'e tsaye tahau saman gado ta kwanta.

LAHANIWhere stories live. Discover now