LAHANI

9 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*THE END*

*PAGE 80*

Saida Zainab taga ya b'acewa ganinta sannan ta saki labulen window ruwan hawayen so cike tafff a idanunta,cikeda rashin kuzari da matsananciyar damuwa ta koma d'akinta tahau gado pillow ta jawo ta rungume ajikinta tanata tunanin iyayenta.
Zuciyarta sai k'ara azalzalarta takeyi tana k'ara dulmiya acikin kogin tunanin iyayenta wad'anda batada tamkarsu aduniya, wad'anda suka nuna mata tsantsar so da k'auna ita kanta ta tabbatar da cewar iyaye sune jigon rayuwa musamman mahaifiya itace kowane irin k'addara ya auku ga d'iya ko d'anta bata tab'a guje maka/miki, gashi ab'angaren d'aya na zuciyarta soyayya da k'aunar doctor Nazeer sai k'ara bunk'asa yake amuhallin ruhi da zuciyarta.
Ayanzu ta hak'ik'ance shi _So wani irin sinadari ne dake yawo acikin jinin jikin d'an Adam,yawan sakwanni,mintuna,awanni,kwanaki,makwanni,watanni ko shekaru bazasu tab'a shafe so na gaskiya ba._
_K'wayar so ce ke samun muhalli azuciya wanda cikakken aminci da yarda da juna ke tabbatar da son har ya kai matsayin da ba za'a iya aunashi a bisa mizani ba._
Haka kuma _So linzami ne dake jagorantar igiyar masoya,so harsashi ne dake harbin dukkan zuk'atan masoya_.

()()()()()()()()()()()()()()()()

Abinciken da doctor Nazeer yayiwa Zainab ya gano cewar ciwon yayi sauk'i matuk'a, magungunan daya rubuta atakarda shi da kansa yaje chemist ya siyo mata magunguna yaje har gidan barisster Hayatu yakai mata,dayake tanason ta warke shiyasa bata wasa da magani ko wane iri ne sha takeyi hakama Aunty Maijiddah takan samo mata magungunan ciwon sanyi tana bata saboda babu abinda ta tsana irin taga Zainab ta fad'a cikin mugun yanayi,gashi ayanzu itace matsayin uwa gareta shiyasa take k'ok'arin ganin ta kula da ita, Ramatu ma ba'a barta abaya ba k'ok'arin kulawa da Zainab batason ganin ta kad'aice cikin d'aki ita kad'ai tana kuka.
Saboda idan har Zainab ta k'unshe a d'aki babu makawa saika risketa tana rusar kukan takaici da nadamar auren Laweezi arayuwarta, wannan dalilin ne yasa suke kaffa-kaffa da ita basa barin ta kasance ita d'aya domin sun lura so takeyi ta tsanantawa kanta tsananin damuwar dazai zamo mata nak'asu arayuwa.

*BAYAN WATA D'AYA*
Aranar Assabar da safe k'arfe 5:30am bayan an fito daga masallaci anyi sallar asuba,Aunty Maijiddah ta tashi da matsanancin ciwon nak'uda sai murk'usu da zufa takeyi k'ungunta ta rik'e akan azaba tana ciccije baki!Yayinda wani irin azababben ciwon nak'uda ke kai mata farmaki akowane sassan jiki da magudanar jini,ta dad'e cikin matsanancin hali saiga mijinta barisster Hayatu ya dawo yana isowa tsakiyar d'akin yayi arba da Maijiddah durk'ushe k'asa dafe da k'ugunta tana nak'uda hankali tashe ya isa wurinta yace"subahanillah! Maijiddah ciwon mak'udan ne ya tisoki agaba..".
Aunty Maijiddah gyad'a kanta kawai tayi domin rad'ad'in ciwo bazai barta tayi magana ba.

Jikin Brr Hayatu yana k'yarrma ya cire jalabiyarsa ya chanza tufafi yana cewa"kiyi hak'uri kinji bari inzo in kaiki asibiti..!".
Yana kammala chanza tufafi yaji ta saki gigitacciyar k'ara wanda ya karad'e d'akin gaba d'aya da azama Brr Hayatu ya iso wurinta yana rirrik'eta yana cewa"kiyi hak'uri Maijiddah zaki haihu lafiya..".
Wani irin nishi mai k'arfi ya biyo baya tana yinsa saiga kan jaririya ya biyo baya da sauri barisster Hayatu ya taimaka mata ya ida ciro jaririya,razor blade ya d'auko sabuwa ya yanke cibi jaririya sai tsandara kuka takeyi yah Hayatu ya rungumeta cikeda matuk'ar k'auna da shauk'in so duk jikinta akwai jini hakan baisa k'yamarta ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 12, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LAHANIWhere stories live. Discover now