LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 74*

Har ga kawu Rabilu ya manta da zancen cewar dukiyar Laweezi ce suke juyawa ahannunsu saida Alhaji Yunusa ya tunatar dashi,gabansa ya fad'i zuciyarsa ta karaya cikin wani irin k'arfin hali da sanyin jiki yace"yanzu kana nufin matuk'ar aurensa da Zainabu ya rabu k'wace kud'ad'ensa zaiyi ahannunmu..?".Baba Yunusa ya saki gwauron numfashi yace"k'warai kuwa ko ka manta ranar ne agabanka yazo yace mana idan Zainabu ta rabudashi amshe dukkanin kud'ad'ensa ahannunmu zaiyi..".Kawu Rabilu ya yakune fuska cikeda damuwa yace"to ai naga mu bamuda wani laifi acikin wannan lamari.."."Mu kuwa mukeda babban laifi acikin wannan lamari domin mu kasa tank'wara Zainabu ta zauna dashi ko bata so..".Kawu Rabilu yaji kamar an sokeshi da kibiya k'irjinsa ne yayi masa nauyi sosai dak'yar ya had'iye miyau a mak'oshi yace"haka ne to amma yanzu ya zamuyi wace irin hanya ce ya kamata mu b'ullowa al'amarin Zainabu ta zauna agidan mijinta..".

Alhaji Yunusa ya saki wani irin murmushi yace"taro kunnenka kaji abinda zamuyi..".
"To Allah yasa ba kauce hanya zamuyi ba..".
"Banason gardama ka saurareni tukun kafin kace wani abu..".
Kawu Rabilu ya tara kunnensa asaitin bakin baba Yunusa ya dinga fad'a masa wasu maganganu k'asa k'asa wad'anda bana iya jiyo mi yake fad'a masa,saida yakai k'arshen zancensa sannan kawu Rabilu ya jaye kunnensa yana jinjina maganar a k'wak'walwarsa can yayi huci mai tattare da damuwa yace"Yunusa gaskiya bazan iya aikata abinda ka fad'a ba..".

Alhaji Yunusa ya sassauta murya sosai cikin son lurar dashi yace"ka fahimceni Rabilu duk abinda zamu aikata na wani lokaci fa kuma domin mu tseratar da kanmu ne daga talaucewa".
"Saboda haka ka bani had'in kai mu aiwatar da komai cikin sirri..".
Kawu Rabilu ya cire babban rigarsa saboda zafin dake kwaranya cikin gangar jikinsa ya kad'a kai cikin rashin gamsuwa yace"bazan tab'a iya aikata abinda kake so ba domin wani cikar burinmu na banza..!".
Aharzuk'e zuciyarsa tana suya yace baba Yunusa"auuuu hakama zaka fad'a..?".
"Na zata akan dukiya babu abinda bazaka iya aikatawa ba..!".
"Na zata zaka iya komai matuk'ar burinmu zai cika...!".
Kawu Rabilu yaji ransa ya b'aci kauda kai gefe yayi yace"bazan iya aikata abinda ka fad'a ba duk son kud'ina banason inyi abinda ubangiji zaiyi fushi dani..!".
Alhaji Yunusa yayi masa walak'antaccen kallo yace"hmm Rabilu kenan!Ashe duk tsanarka da talauci k'arya ne tunda har akwai abinda kake tsoron aikatawa..".
"Dole inji tsoron sab'awa mahaliccina".

"To tunda kak'i bani had'in kai mu gudu atare mu tsira atare kowa tasa ta fissheshi daga yau babu ni babu kaiiii...!".Alhaji Yunusa ya fad'i wannan maganar cikeda tuk'uk'in bak'in ciki.

"Na amince da sharad'inka Yunusa kowa ya kama gabansa..!".Cewar Kawu Rabilu yana muzurai da idanu.

Alhaji Yunusa ya mik'e tsaye yana aikawa kawu Rabilu sak'on harara zuciyarsa sai k'una da hargagin suya takeyi masa,fuuuu idanunsa har rufewa sukeyi adalilin tsabar b'acin rai ya fice daga cikin harabar gidan kawu Rabilu ya koma gidansa.

{{{}}}}{{{}}}}{{{}}}}{{{}}}}{{{}}}

*BAYAN KWANA BIYAR*
Zainab ta rasa yadda za'ayi ta fita daga cikin harabar gidan Laweezi ta kaiwa barisster Hayatu files da bindigar batare da an ganta ba,tunanin mafita takeyi acikin k'wak'walwarta can wata irin dabara ta fad'o mata arai murmushin farin ciki ta saki akan k'yakk'yawar fuskarta,mayafinta ta jawo ta rufa ajiki sannan ta zura takalmi a k'afafunta ta zarce a d'akin mijinta.
  Tana isowa abakin k'ofar ta iza k'ofar da sallama fuskarta k'unshe da lallausan murmushin dayake k'ara bayyana sirrin k'yawonta, Laweezi dake zaune akan doguwar kujera ya juyo ya kalleta sai yaga ta k'ara masa k'yawon gani isowa wurinsa tayi tana jifanshi da yaudararren kallo,danne k'iyayyarsa tayi a k'irjinta ta rausayar da kai cikin matuk'ar shagwab'a tace"My heart desire..".
Laweezi yace batare daya k'ara kallonta ba"Zainab mi kike buk'ata agareni..?".
Batayi mamakin jin ya kirata da ainahin sunanta ba domin idan ta lura akwanakin nan baya cikin natsuwarsa da kwanciyar hankali.
Zainab ta noce kanta k'asa tace"dama izini nakeso ka bani inje super market shopping..".
Shiru Laweezi yayi yana son gasgata cewar abinda ta fad'a da gaske ne ko so takeyi tayi masa yawo da hankali,tsura mata idanu yayi na tsawon mintuna yana son gano abinda ke cikin k'wayar idanunta amma bai gano akasin abinda ta fad'a cikin sassanyar murya mai taushi yace"na aiki driverna wani wuri saidai in baki kud'i kije kihau napep idan zaki iya..?".
"Eh zan iya aiba wani dad'ewa zanyi ba..".
"To shikenan kamar nawa kike buk'ata..?".Ya tambayeta cikin k'auna.

LAHANIWhere stories live. Discover now