LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 38*

Bayan Zainab ta gama serving d'insa ta d'ago idanunta tana k'are masa kallo cikin muryarta mai kashe jiki tayi masa magana, amma ina sam baiji taba saboda ya riga yayi nisa cikin kogin tunani azuciyarsa sai k'issima yadda zai gudanar da rayuwar aurensa yakeyi idan har ya mallaketa amatsayin mata.
Zainab ta sake magana tace"na kammala serving d'inka..".
"zan iya tafiya..?".
sai alokacin ne natsuwarsa ta dawo ajikinsa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa yace"Ok thanks you can go..".
Zainab ta juya sannu ahankali tana tafiyarta mai d'aukar hankali da tafiyarda imanin duk wani cikakken namiji mai ji da kansa, duk da ta lullub'e jikinta da babban mayafi hakan bai hana bayyanuwar k'yawon surarta ba yana aikin kallonta harta fice sannan ya lashi leb'en bakinsa tareda kishingid'awa saman cushion.
koda yah Hayatu yazo ya sameshi baici komai ba saboda gaba d'aya jikinsa ya mutu mururus adalilin k'auna da soyayyar Zeey da tayi mishi mugun kamu, ganin yadda jikin Nazeer yayi sanyi ne yasa yah Hayatu yace"Nazeer tashi zaune muci abinci..".

Nazeer ya cize baki akasalance yace"na k'oshi..".

"kanama farawa in saka agirka abinci domin kai sannan kace bazaka ci ba..".

Nazeer ya tashi zaune yana fuskantar Hayatu kamar bazaice k'ala ba can ya musk'uta cikeda tsananin k'aunar Zeey yace"barisster Hayatu ina son inyi maka wata tambayar idan har kanason inci abinci ka bani amsa..".
"hakan ne zaisa in samu natsuwa azuciyata..!".
yah Hayatu ya rausayar da kansa cikeda matuk'ar mamaki yace"kai kuwa Nazeer wace irin tambaya ce zakayimin..?".

Nazeer ya sauko saman carpet ya zauna tareda lank'washe k'afafunsa cikin guguwar so yace"wa cece yarinyar data fita yanzu...!?".
yah Hayatu ya murmusa cikeda shek'iyanci yace"ohh Zainab kake nufi wai..?".
"eh wadda ka turo ta kawomin abinci ita nake nufi..!".
Hayatu yace"k'anwar matata ce uwa d'aya uba d'aya..!".

Nazeer ya saki murmushin dake fallasa asirin k'yawonsa yayi hamdala azuciyarsa yace"Alhamdulillahi barisster fad'uwa kenan tazo daidai da zama..!".
"ban gane ba fad'uwa tazo daidai da zama ba..".
Nazeer yace"yanzu kuwa zan fahimtar dakai barisster agaskiyar zance tun lokacin da idanuna sukayi tozali da k'yak'k'yawar fuskarta farat d'aya na tsumduma akogin soyayyarta sai shawagi nakeyi asararin k'aunarta..!".
"saboda haka ina rok'on alfarmarka daka taimaka ka shawomin kan Zainab ta amince dani ta amshi soyayyata..!".

barisster Hayatu saida ya bari yakai k'arshen zancensa jikinsa yayi sanyi alokaci d'aya cikin k'arfafa masa gwiwa yace"karka damu Nazeer da izinin ubangiji zanyi k'ok'arin ganin ka mallaki Zeey saidai da taimakonka zakayi amfani da dabararmu ta maza wurin siye zuciyarta kana k'yautata tareda yi mata kalamai masu nuni da tsantsar tausayi da soyayyar gaskiya..".
"domin kasan mata saida k'yautatawa, tausayi, da kuma iya lafuzza masu dad'i sannan zakaji dad'in zama da ita..".
Nazeer yace"da yardar Allah zanyi amfani da shawarorinka barisster..".
"good friend wanke hannunka muci girkin Zeey..".
atare suka wanke hannayensu cikin k'aramar roba suna gama wankewa suka sukayi bismillah tareda fara cin abincin atsanake.

**********************
Da marece k'arfe biyar daidai 5:00pm bayan tafiyar doctor Nazeer gidan iyayensa itama Zainab yah Hayatu ya sakata cikin motarsa ya kaita har bakin k'ofar gidansu ya aje, godiya tayi masa ya d'auko ledodin da Aunty Maijiddah ta bata cikeda kayayyaki ta amsa ta fad'a cikin gidansu sannan ya juya akalar motarsa ya nufi hanyar zuwa unguwarsu.

LAHANIWhere stories live. Discover now