LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 17*

Ganin yadda suke rarrashinta ahalin sune zasu taimaketa ba ita ce zata taimakesu ba kuma tayi dogon nazari da tunani muddin ta bari suka sub'uce mata, ba lalle bane ta sake had'uwa da masu taimakonta hakan ne yasa bisa dole ba domin ranta ya soba ta yanke shawarar bari ta amince kada ta bari wannan damar ta kufce mata ahannu, su kuma rok'onta kawai sukeyi kamar masu neman wani abu awurinta ganin tayi sun dameta sosai yasa tace musu ta amince zata shiga motarsu.
  farin ciki da murna ne ya shimfid'u afuskokinsu nan take sukayi waya agabanta sukayi magana da mechanic mai gyaran mota tareda gaya masa adaidai inda zaizo ya d'auki motar, su kuma suka jagoranceta har cikin motar ta shiga ta zauna suka maida k'ofar suka rufe tareda saita motarsu akan kwalta suna driving anatse babu garaje ko rashin kamala.
Zainab ta fara hamma alamun barci ne kwance cikin k'wayar idanunta wani irin mutuwar jiki taji ya ziyarceta alokaci d'aya ta kishingid'a saman kujerar, batare da b'ata lokaci barci ya fisgeta su kuma ganin barci ya saceta yasa sukaji dad'i sosai saurayin na farko yace"amma yau kam munyi nasarar satota batare da mun wahala sosai ba..!".
d'ayan yace"ai shiyasa nake ce maka komai na duniya asannu ake binsa ba'a yin garaje..!".
"na tabbatar da ace bamu bita ta lalama ba da har yanzu bata amince ta biyomu ba..!".
"wannan gaskiya ne yanzu dai mun cika umurnin Oga bamuda wata fargaba ko damuwa..".

"k'warai kuwa ashe matarsa shegen k'yawo ne da ita shiyasa duk yabi ya rud'e da gigicewa akanta..!".

"hmmm ni abin har mamaki nakeyi ace wai Oga dabai maida mace abakin komai ba shine yau yake shiga cikin damuwa asanadiyyar mace d'aya lalle wannan ta taki babbar sa'a arayuwa..".
"uhhhh zancenka gaskiya ne..!".
maganganunsu suka cigaba dayi acikin motar suna mamakin yadda guguwar k'auna da shauk'in soyayyar Zainab ta mayarda Laweezi wani iri alokaci d'aya..

*********************
Acan gidan barisster Hayatu kuwa tun lokacin da Zainab ta sanya k'afafunta ta fita Aunty Maijiddah taji hankalinta ya tashi zuciyarta ta girgiza gabanta sai luguden tsoro da d'imaucewa yakeyi, yayinda taji ta kasa samun sukuni da natsuwa azuciyarta adalilin rashin dawowar Zainab gida ta ciro wayarta ta shiga kiran nombar Zeey d'id'id'id'i taji kukan phone d'inta amma harta katse ba'a d'aga wayar ba.
tunda taji phone d'inta ta shiga taji sauk'in damuwarta kai tsaye ta fad'a cikin kitchen ta d'ora tukunyar abincin dare tuwon semovinta da miyar shuwaka,nan take k'amshin girkinta ya k'amsasshe kewayen gidan ciki da waje, itace bata fito ba saida ta kammala girkin ta zuzzuba abincin cikin kuloli masu tsananin k'yawo sosai ta dinga jidar kulolin tana kaiwa dinning table tana jajjarasu cikin matuk'ar tsari da burgewa, bayan ta gama jerawa ta koma kitchen ta tsabtaceshi tareda wawwake kayayyakin data b'ata.
tana kammala wanke wanke ta fito daga cikin kitchen d'in ta fad'a bathroom domin ta watsa ruwa ajikinta taji sanyi azuciyarta.

Ta dad'e tana gurza dukkan sassan da sak'on jikinta sannan ta d'oraye kanta da ruwa ta fito jik'a jik'a da ruwa ajikinta tana amfani da k'aramin towel tana goge ruwan dake d'iga,wurin wardrobe taje ta d'auko mayukanta ta shafa ajiki sannan tayi light make up ta ciro shadda doguwar riga ajikinta.

Aunty Maijiddah ta komo parlour ta zauna tana jiran dawowar k'anwarta Zainab,tana zaune taji zaman ya girsheta ta kishingid'a saman kan cushion d'in can saiga sallamar yah Hayatu rik'e da hannunsu Jawaheer wad'anda suketa zuba masa surutu shi kuma sai saurarensu yakeyi yana sakin murmushi afuskarsa domin diramar yaran dariya take bashi fiyeda misali.
Maijiddah tana ganin mijinta ta mik'e tsaye tazo ta amshi briefcase da system d'in dake rik'e ahannunsa tareda yi masa sannu da zuwa,amsa mata yayi fuskarsa k'unshe da fara'a tana amsar kayayyakin ahannunsa kai tsaye ta fad'a cikin d'akinsa ta ajesu tareda had'a masa ruwa masu d'umi atoilet.
yah Hayatu anan parlour ya zauna shida 'ya'yansa sai surutu da gardama suke zubawa, da yaga ya d'auko gajiyar aiki gashi kuma sun sakoshi gaba da surutu dole ya kallesu yace"ku tashi ku tashi kuje d'akinku kuyi wanka nima yanzu wanka zanyi in kwanta saboda agajiye nake..!".
Jawaheer ta chuno baki tace"idan mukayi wanka muzo d'akinka Abba ka kunna mana system muyi kallo..?".
"eh Abba Indian film zaka sanya mana mu kalla..!".Inji Mahafuz yana washe hak'ora kamar gonar auduga.
yah Hayatu yace"a'a karkuzo ku dameni barci nakeji sosai kuyi kallonku anan parlour..".
"to shikenan mun hak'ura har wani lokacin..".Fad'ar Jawaheer yah Hayatu agalabaice ya sance jikinsa ahankali ya mik'e tsaye tareda ficewa daga ciki ya fad'a cikin d'akinsa.

LAHANIWhere stories live. Discover now