LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 34*

Akan cin bashin daya keyi yasa jarin Sa'idu yayi k'asa 'yar ribar dayake samu tana neman ta ragaice abanza, wannan dalilin ne yasa hankalinsa ya tashi yaji ya tsani irin halayyar Yunusa ta cin bashi da almabuzzaranci da kud'ad'e! Saboda ya saba rik'e kud'ad'e masu kauri shiyasa yake bin duk wata hanyar da zaibi yana d'auke kud'ad'en da Sa'idu yake samun riba yana zuwa kasuwa yaje ya kaso kud'in wurin siyen tsire ko nama su k'unshe shida Lantana suna shan galarinsu.
Ganin komai nashi yanada ja da baya yasa yazo yayiwa shawara da Aziza tareda sanar masa damuwarsa domin ayanzu itace abokiyar shawara kuma matsayin mahaifiya agareshi, saida tayi jugum tana tunani can ta bashi shawarar cikin 'yan kud'ad'en da suka rage nashi ya raba biyu ya d'auki kaso d'aya yaba Yunusa saboda aganinta idan mijinta ya rasa wata rana dole ya zamana Yunusa nada kud'i, baiyi musu ba ya amince da zancenta nan take yaje ya bawa yayansa kud'ad'e masu kauri yace yayi sana'a babu godiya babu komai ya amshe kud'in ahannunsa cikeda matuk'ar rainuwa yana zaginsa a k'ark'ashin zuciyarsa.

Yunusa bai juya kud'ad'en awata sana'ar ba yaje ya kashesu abanza suka ciwa bakinsu dad'i shida Lantana.

Alokacin ne Lantana ta sake haihuwar d'a namiji yaci suna Basiru har ila yau Sa'idu ne ya d'auki d'awainiyar biki da komai da komai babu abinda mahaifin yaro ya tab'uka, duk ire iren hidimomin da Sa'idu yakeyi musu basa gani balantana su gode mashi saima shigewa dak'insu suna zaginsa tareda aibantashi!.

Ganin 'ya'yan Lantana biyu har yanzu Aziza bata samu ciki ba yasa taji hankalinta ya tashi natsuwarta ta gushe saboda ayanzu itama tana buk'atar haihuwa, agefe ga gorace goracen da Lantana ta isheta dashi babu dare babu rana akowane lokaci cikin yi mata habaici takeyi, wata rana da kanta take fad'awa Sa'idu damuwar rashin haihuwarta tana kuka shi kuma sai lallashinta yakeyi yana rungumeta ajikinsa domin baya k'aunar ganin hawayenta idan da abinda ya tsana to bai wuce yaga Azizarsa tana cikin damuwa ba, hak'uri da nasihohi yake mata tareda nusar da ita cewar komai na duniya yanada iyaka idan da rabon su haihu duk daren dad'ewa saita haifa musu yara, yadda taga mijinta ya shiga cikin damuwa shiyasa taji tausayinsa ya gauraye magudanar jijiyoyinta nan da nan ta saki fuskarta ta nuna masa cewar ta dogara ga ubangiji mad'aukakin sarki duk abinda ya k'addaro arayuwarsu mai k'yau.

Tun daga lokacin suka mik'awa ubangiji lamarinsu tareda tashi tsakiyar dare suna nafiloli da karatun qur'ani suna kai kukansu wurin ubangiji, haka ne yasa suka samu sassauci da tsantsar natsuwa azuciyarsu tuni suka daina damuwa akan maganganunsu Yunusa da suke jifansu dasu.
Dayake ubangiji Allah maji rok'on bawa ne saigashi rana tsaka ciki ya bayyana k'arara ajikin Aziza ai kuwa nan da nan farin ciki da annashuwar zuciya ta shimfid'u afuskokinsu, suka dinga sadaka suna mik'a godiyarsu ga ubangiji Allah cigaba da rainon cikin Aziza sukayi cikin tsantsar so da k'auna.

Sa'idu ya d'auki soyayyar duniya ya d'ora akan cikinta domin kwad'ayin samun 'ya'yansa na cikinsa haka ne yasa duk irin cikamar da takeso shi yake aiko mata ko yazo ya kawo mata, tun Lantana bata fahimci Aziza tana d'auke da juna biyu har tazo ta fahimta aranar kuwa tasha kuka tareda tsinewa Aziza kamar itace ta bawa kanta ciki.
mijinta Yunusa yana dawowa wurin yawon gantalinsa yazo ya riski wannan mugun labari (awurinsu ba 😂) mai tattare da d'acin rai da k'uncin rayuwa hankalinsa yayi matuk'ar tashi kamar zai kuwwata saboda maganar ta gigitashi tareda hargitsa masa tunani dak'yar Lantana taga ya sassauta b'acin ransa suka yanke shawarar zasu tsaya suga abinda Aziza zata haifa idan namiji ne kashesa zasuyi! Idan mace ce babu abinda zasuyi mata domin mace tanada rauni ko ta girma suka tashi aikata abinda ransu yakeso bata isa ta hanasu ba, suna kammala yanke shawarar suka binne maganarsu cikin d'aki babu ya jiyo bale yasan ainahin abinda yake mak'ale azuk'atansu.

LAHANIWhere stories live. Discover now