LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 29*

Domin bayason mahaifiyarsa ta furta kalaman da ubangiji zai iya fushi dashi jikinsa asanyaye yace mata"karkice komai Inna nasan munyi kuskure amma kiyi hak'uri bazamu sake ba..!".Inna A'i ta kallesa idanunta suna bayyanar da tsantsar bak'in cikin da take ciki tace"haba Sa'idu miyasa zaka biye masa ku dinga hayaniya kamar karnunka..?".
"miyasa bazaka dinga hak'uri da halayyar Yunusa ba bayan kasanshi mutum ne mai tsananin son tashin hankali da fitina arayuwa..!?".
Jikin Sa'idu yayi matuk'ar sanyi yace"kiyi mana afuwa Inna nima ba'a son rainane na kulashi ba..!".
"to miye ya had'aka fad'a da d'an uwanka bayan kasan yayanka ne..!?".
Sa'idu ya sauke gwauron numfashi cikeda matuk'ar b'acin rai yace"Inna bansan hawa ba bansan sauka ba yaya yazo ya cukwikwiyemin riga!Ashe wai wurin Aziza ya tafi zance ta walak'antashi shiyasa yazo ya sauke takaici akaina..!".
Inna A'i ta jijjiga kanta cikeda rashin jin dad'in abinda ya faru tace"ka cigaba da hak'uri Sa'idu karka k'ara kulashi da izinin ubangiji komai zai daidaita..!".
"bazan k'ara kulashi ba Inna..!".
"karka damu zan san yadda zanyi in wargaza shirin baffan yara domin ka auri masoyiyarka..!".
"ina godiya sosai Inna".

"ka daina yimin godiya Sa'idu saboda komai zan iyayi domin ganinka cikin matuk'ar nishad'i da tsantsar farin ciki..".

Inna A'i ta cigaba da kwantar masa da hankali har saida Sa'idu ya samu natsuwar zuciya, sannan yayi tafiyarsa makarantar allo ita kuma Inna A'i ta fad'a cikin madafarsu tana kichaniyar girka musu abinci.

**********************
Tun lokacin da suka samu sab'ani atsakaninsu Yunusa ya d'auki k'iyayyar duniya ya d'ora akan Sa'idu tareda yin zazzafan fushi dashi, duk dayake Sa'idu yana k'ok'arin yi masa magana akowane lokaci amma baya bashi amsa domin shi mutum ne mai hassada da tsantsar bak'in rai idan ya k'ullaci mutum aranshi bazaka tab'a burgeshi ba har abada.
ya zamana duk lokacin da Sa'idu yayi masa magana saiya sassaka bak'ak'en maganganu masu bak'anta zuciya da tsantsar rad'ad'i arai, hakan ne yasa Sa'idu ya shareshi babu abinda ke had'asu sai kallon juna tun abin baya damun Sa'idu har yazo yana damunsa tareda ci masa tuwo a k'warya, wannan dalilin ne yasa Sa'idu ya gayawa Inna cewar yayansa fushi yakeyi dashi domin bazan iya jimirin fushinsa ba.
Inna A'i da kanta ta had'asu tayi musu nasiha mai ratsa b'argo da jinin jikin d'an Adam sannan ta rok'esu dasu shirya da juna, saboda gaba batada k'yawo ko kad'an arayuwar musulmai bayan ta kammala yi musu nasihohi ta umurcesu sukayiwa juna magana sannan ta sallamesu suka k'ara gaba.

Rayuwar ta cigaba da gangara ahankali alokacin ne Inna A'i ta tura k'annai da yayunta suka shawo kan baffa Zubairu dak'yar ya amince akaje aka nemarwa Sa'idu auren Aziza, domin yarinyar duk ta haukacewasu Mallam Jauro akan babu wanda takeso saishi shiyasa duk ta zabge ta rame saboda ganin takeyi kamar bazata auri muradinta ba.

Aranar da akaje neman aurenta to aranar Aziza har hawayen farin ciki ta zubar akan zata auri Sa'idu saboda ba k'aramin so takeyi masa ba, sunje gidan Mallam Jauro anyi musu tarba ta mutunci da karamci sannan magabatansa suka biya sadakin Aziza bayan sunsha fura sunci kayan marmari komai dai an gudanar cikin dattijantaka sannan suka d'ungumo suka dawo gidajensu bayan sun fad'awa Inna A'i yadda al'amarin ya kasance.

Inna A'i ta kasance cikin tsananin farin ciki da walwala arayuwarta domin ganin burin Sa'idu ya kusa cika.

Sa'idu yana dawowa gida Innarsa tayi masa albishirin cewa an bashi Aziza ai kuwa bakin nan nashi ya kasa rufuwa adalilin wani irin rikitaccen farin ciki dake kwaranya cikin k'ofofin jikinsa, aranar wuni sukayi suna zance guda domin abin ba k'aramin dad'i yayi musu arai ba, ab'angaren Yunusa bayada labarin baikon Aziza da k'anensa shiyasa yaketa babbazawa cikin gari yana cewa shugaba Mallam Jauro ya bashi aurenta, yayinda wasu suke masa kallon wawa wasu kallon mahaukaci wasu k'ebewa gefe sukeyi suna tsincesa da cewar suna ganin ya tab'u bayada isasshen hankali!.
sai wata rana kwatsam labarin baikonsu Aziza ya iso akunnensa ai kuwa nan take ya mik'e tsaye agigice zuciyarsa tana suya ya fad'a tsakiyar filin gidansu ahaukace! Yana shuri da duk abinda yaci karo dashi agabansa yana k'yallara uban ihu da kururuwa yana cewa"ina babbak'un munafukan mutanen cikin gidan nan..!?".
"wallahi garama ku fito fili tunda kuka munafurceni saina tayarda hankalin kowa cikin gidan nan..!".
"saina addabeku tsofaffin banza maciya amana ina kukeneehh..!?".Ya ida maganarsa yana d'aga muryarsa da k'arfi tamkar bai gayawa mutanen ruggarsu.

LAHANIWhere stories live. Discover now