LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 26*

Zazzafan sak'onni yaketa aika mata cikin kwarmin idanunsa masu haske da k'ara rura wutar soyayyarta azuciyarsa, itama shi take kallo tana murmushin dake narkar da zuciyarsa ya dinga shawagi asararin k'aunarta, ji takeyi asanadiyyar k'auna da tsantsar soyayyar gaskiya kamar taje ta fad'a cikin faffad'an k'irjinsa ko zataji sauk'in abinda takeji gamedashi arayuwarta,kallo d'aya zakayi musu ka gano dukansu kowanensu zuciyarsa cike take fal da tsantsar kishi da tsagwaron k'aunar juna,saboda yadda suka tsurawa juna ido zaka fahimci zuk'atansu sunada babbar dangantaka da juna alokacin ne yakejin soyayyarta tana azalzalarsa zuciyarsa tana begenta tareda muradin su kasance da juna har abada.

Ganin Sa'idu ya lula cikin wata jahar tunani ta daban yasa Aziza tayi k'ok'arin jaye idanunta daga cikin nashi cikin zazzak'ar muryarta tace"Ruhina lafiya naga kayi shiru mi kake tunani ne..?".
baima jita ba balantana ya samu sararin bata amsarta.
Ganin yayi shiru baice mata komai yasa taji gabanta ya fad'i hankalinta ya tashi cikin fargaba da zullumi tace"magana nakeyi maka kayi shiru..!".
Sa'idu sai alokacin ne yaji abinda ta fad'a ya dawo cikin hayyacinsa tareda b'oye damuwarsa yace"Mai sona ya kike..?".

Harararsa tayi da wasa cikeda k'auna tace"ban sani ba..!".

Sa'idu yaji hankalinsa ya d'unguma cikin tsinkewar zuciya yace mata"ayyah Aziza miye abin fushi kuma yanzu..!?".
Zumb'ura baki tayi cikin sagarci tace"ba kaine tun d'azu inayi maka magana ba ka shareni..!".
Langwab'e kansa yayi yana kallonta kamar zaiyi kuka yace"kiyi hak'uri ban kiji bane kema kinsan idan naji ki bazan tab'a iya k'yaleki ba batare dana maida miki martanin zancenki ba..!".
Aziza ta sassauta fuskarta daga fushin da tayi tace"to shikenan na hak'ura tunda har ka bani hak'uri..".

"auuuu idan ban baki hak'uri ba bazaki tab'a hak'ura ba ko..?".

"ai kaima kasan bazan tab'a hak'ura ba..".

"to naji afuwan shalelen Sa'idu gimbiyar zuciyata ina fatar babu abinda yake damunki arayuwa..".

Murmushi ta sakar masa ya maida mata martanin murmushinsa ta girgiza kanta cikin alkunyarsu ta fulani tace"k'alau nake babu abinda yake damuna kwana biyu kwata kwata ka d'auke k'afafunka wurina ko miyasa..!?".

"Ayyah saifa hak'uri Azizata abubuwa ne suka shamin kai shiyasa kika jini shiru...!".

"kai kullum akayi magana sai kace abubuwa sunsha maka kai wato kafi k'aunar aikinka akaina ko..?".

"ba haka bane Aziza ki fahimceni wallahi kinfi komai kima da daraja awurina kawai dai saboda ana gina ajizuwa a makarantar da nake karantassuwa shiyasa kikaga na d'auke k'afata saboda shugabanmu ne yace ya zamo dole mu dinga tsayawa ana yin komai agabanmu..".

"karki damu idan mukayi aure insha Allahu zan d'aukeki in maidake can shikenan kinga na huta da yawan aikata laifi...".

cikeda tsananin kunyar zancensa Aziza ta saka tafin hannunta ta rufe fuskarta saboda wani irin kwarjini da yayi mata a idanu.

yadda ta nuna kunyarsa takeji yayi masa dad'i arai murmushin dake k'ayatar da fuskarsa yayi yace"ohh kunyata ma kikeji Aziza..".
"to bud'e fuskarki bana k'ara yi miki maganar aurenmu tunda kunya tayi miki yawa...".

LAHANIWhere stories live. Discover now