LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 77*

Kafin su k'arasa d'akin barisster Hayatu saida suka bincike d'akuna biyu dake tsakaninsu basu tsinci kowa ba,sannan suka rankaya sukayo d'akin dasu Aunty Maijiddah ke ciki suna isowa bakin k'ofar suka jita akulle wannan ya k'ara tabbatar musu da cewar su Brr Hayatu na ciki,shahararren keys d'in da suka zo dasu ne sukayi amfani suka bud'e d'akin.

Su Maijiddah dake mak'ale da juna jikinsu sai karkarwa yakeyi sun rasa hanyar da zasu bi su gudu domin sun fad'a cikin wani irin mugun yanayi mai ban tausayi,shi kansa duk ya daburce da rikicewa ya rasa tudun dafawa yayinda duk sun jik'e sharkaf da gumi.
"Zasu kashemu husby ka kira 'yan sanda kafin su shigo..!".Inji Aunty Maijiddah tana hawayen takaici.
"Babu abinda zasu iya yi mana Maijiddah ki natsu ki dinga addu'a azuciyarki..!".
"Kona kira 'yan sanda bazasu iya fitar damu daga cikin wannan musibar ba Jiddanah...".
Maijiddah ta saki ajiyar zuciya cikin rashin natsuwa tace"nasan tamu ta k'are mu haka rayuwarmu zata k'are an kashemin iyayena an rabani da Zainab da kuma 'ya'yana..".
"Ki daina d'ebe tsammani daga rahamar ubangiji Jiddah duk wanda ya mutu lokacinsa ne..".
"Daddyn Jawaheer ubangiji ma da kansa yace tashi in taimakeka idan bamu taimaki kanmu ba ta yaya kake tsammanin zamu tsallake tarkon wad'annan azzalumai..?".

Suna bud'e k'ofar suka shigo rududuuuu cikin dabara wani ya kunna light on saiga d'akin ya gameda haske,su Maijiddah mak'ale da juna k'iri k'iri.
Ogan ya kallesu ya kece da dariyar k'eta yace"ayyah miji da mata sai kukan rabuwa sukeyi ashe dai kuna tsoron mutuwa..!?".
Cikin dakiya Barr Hayatu yace"su wayeku mi kuke nema awurina..!?".
"Ranka muke nema sannan muka buk'atar mu d'and'ana dad'in iyalinka..!".
Daka masa tsawa yayi cikin hargowa yace"ka iya bakinka matsiyaci..!Iyalina tafi k'arfin wawa k'azami irinka..".
Ogan ne ya nuna kansa cikin zafin zagin da yah Hayatu yace"zagina kayi..?".
"An zageka..!?".
Tass Ogansu ya d'auke yah Hayatu da mari mai zafi bai aje hannunsa ba barisster Hayatu ya d'aukesa da mahaukatan maruka uku ajere asanadin haka saida Ogan yayi tanbal tanbal zai fad'i amma bai kai k'asa ba.
Yaran Ogan ne suka rufe yah Hayatu da duka ta ko'ina ajiki dum dum dum dum kawai kakeji Aunty Maijiddah sai kuwwa takeyi tana cewa"shegu azzalumai ku barmin mijina kada ku kashesa..!".
Ogansu yana dawowa cikin hayyacinsa ransa yakai mak'ura wurin b'aci azuciye ya shuri Maijiddah aciki wani irin rikitaccen zafi ne ya ziyarceta awurin ta fad'i k'asa asomee!.Sannan ya shiga cikin yaransa sukayita kashin Hayatu saida sukaji masa ciwo ko'ina ajikinsa duk raunika ne,dayake sarkin yawa yafi sarkin k'arfi haka sukayi masa rugu-rugu ya fad'i k'asa asome jini sai zuba yakeyi ajikinsa sannan suka sulala suka gudu.

Koda na lek'a d'akin baba maigadi da Labbo driver ashe d'ad'd'auresu sukayi da manyan igiyoyi sannan sukayi nasarar shigowa cikin gidan,Ramatu dake k'ark'ashin gado tana jiyo kuwwar Maijiddah alokacin da Ogansu ya shureta aciki babu halin taje ta cecesu bayan taji komai ya lafa ta fito a k'ark'ashin gado,kai tsaye ta fad'a d'akin yah Hayatu dukansu asome ta iskesu k'ara ta saki tana gunjin kuka da azama ta nufi hanyar zuwa bakin get wurin d'akin baba maigadi.
Tana k'arasa shigowa ta gansu d'ad'd'aure sunsha bak'ar wuya har sun galabaita matuk'a tana kuka ta fara laluben wuk'a saboda ta kwancensu,can ta samu k'aramar wuk'a tayi amfani da ita ta yayyanke igiyar da aka d'auresu tana kwance ta sanar musu cewar su barisster Hayatu suna kwance asome,cikeda matuk'ar tashin hankali suka rankaya gaba d'aya suka zo cikin d'akin Labbo driver dayake akwai sauran k'arfi atattare dashi shine ya sungumi yah Hayatu yakai cikin mota, sannan suka zo suka taimakawa Ramatu ta sungumo Maijiddah dak'yar tana nishi saboda nauyinta ya rinjayeta domin ga nauyin ciki ga nata.

LAHANIWhere stories live. Discover now