LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 19*

Jikin Gloria yayi matuk'ar sanyi akan yadda taga Zainab duk ta yamutse tareda ficewa daga cikin natsuwarta ta k'ara isowa gab da ita zata rik'o hannunta d'aya, Zainab ta dakatar da ita ta hanyar cewa"karki kuskura ki tab'amin hannu Gloria..!"..
  "idan ba haka zanyi mummunan sab'a miki..!".
Gloria ta ajiye hannunta cikin raunanniyar muryarta da tsantsar damuwa tace"calm down madam Oga yana masifar sonki bazai tab'a cutar dake ba...!".
"what is wrong with you..!?".

Amasifance Zainab tace"no need to know saboda haka you better get out of this room before i lost my temper..!".
Gloria ta mak'e kafad'a tace"haba madam ki saurareni i will not cheat you..!".
"bana buk'atar taimakon kowa saina mahaliccina Gloria..!".
"you though that you can help me to get out of this house never you better change your mind Gloria..!".
"if not Laweezi Haruna Ninja can even kill you..!".
Gloria ta kalli k'wayar idanun Zainab domin ta gasgata gaskiyar abinda ta fad'a arazane jikinta yayi lak'was tace"no no madam Oga cann't kill even grasshopper bale human being..".
"to nayi miki k'arya ki ficemin a d'aki one day one time gaskiya zata bayyana..!".
"am so sorry madam take care yourself..!".Gloria tana k'arashe maganarta taja k'afafunta ta fice daga cikin d'akin cikeda matuk'ar mamakin furucin Zainab tana maimaita maganar a k'wak'walwarta.

Ganin Gloria ta fice daga cikin room d'in yasa Zainab ta ture tiren abincin agabanta tanata rusar kukan bak'in ciki da tsagwaron takaicin rayuwa domin arayuwarta bata tab'a zato ko tsammanin zata tsinci kanta cikin sark'ak'k'iya da k'angi arayuwa ba!.

Gloria direct parlour taje wurin Laweezi dake hakimce akan cushion yana kurb'a lemu a glass cup yayinda a gefensa ga laptop d'inshi nan yana aiki, isowarta wurinsa keda wuya ta russuna k'asa cikin ladabi da taushin murya tace"Oga nakai mata abincin a tire.".
Laweezi yana kallonta ta wutsiyar idanunsa saboda tsabar jin kai da miskilanci kamar bazai yi mata magana ba saida ta dad'e azaune kusan minti talatin, har ta fidda rai akan zai tanka mata taji maganarsa slow yace"you can go".

  Gloria ta mik'e tsaye da guntun sicket d'inta kusan cinyoyinta gaba d'aya awaje suke yayinda ko rigarta 'yar ficiciya ce ana hango breast d'inta kusan rabi afili, kai tsaye ta fad'a room d'in dayake mallakinta domin ta dad'e tana rayuwa a k'ark'ashin companyn Laweezi mai suna *LAWEEZI MOTOR'S COMPANY* .

**********************
Da safe misalin k'arfe bakwai na safe 7:00am agaggauce Zainab ta farko daga barci bayan tayi sallar asuba shine ta koma tayi kwanciyarta, wata irin kafirar yunwa ce ke nuk'urk'usarta da hautsine d'iyan hanjinta dak'yar ta fad'a cikin bathroom tayo wanka akasalance babu wani sauran k'arfi ajikinta, sannan ta bud'e kulolin abincin jiya na ledodin da aka dinga kawo mata taga abincin dake cikin kuloli ya chanza colour yayi bashi, da sauri ta maida murfin kulolin ta kulle tana toshe hancinta cikeda matuk'ar k'yamk'yami taji zuciyarta na tashi asanadiyyar tozalin da tayi da abincin daya kwana.
Kwantawa k'asa tayi tana murk'usun yunwa cikinta sai k'ugi k'uuuuuuu yakeyi mata zuciyarta ta tashi tanata tofar da yawu!Can ta mik'e tsaye zubur k'afafunta suka gagara d'aukarta yayinda taji wani irin jiri ya rufe idanunta tayi luuuuuu zata fad'i k'asa.
Laweezi daya turo k'ofar d'akin ya shigo yanata baza k'amshin turarensa mai sanya zuciya natsuwa ganin Zeey zata fad'i da azama ya isa wurinta ta fad'o masa ajiki, jin ta fad'a ajikin mutum yasa ta saki nannauyar ajiyar zuciya ta fara kichaniyar k'wace kanta amma ina ta kasa saboda batada wani sauran kuzari ajikinta cikeda matuk'ar k'arfin hali tace"miye haka..?".
"kazo ka wani ruk'unk'umeni dan girman Allah karka k'ara tab'a ni da k'azamin hannunka..!".

LAHANIWhere stories live. Discover now