LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 22*

Laweezi yaji wani irin sihirtaccen bak'in ciki da tsantsar zogi ya gauraye k'ofofin jikinsa nan take ran maza ya b'aci! Zuciyarsa ta kawo awuya wani irin d'aci da tsantsar k'una yakeji a k'ark'ashin zuciyarsa cikeda hargowa yace mata"Zainab ki iya bakinki idan kika kai hak'urina bango to zaki sha mamaki da tsantsar takaici akan irin hukuncin da zanyi miki..!".
Ido cikin ido babu alamun tsoronsa afuskarta yayinda cikin k'ark'ashin zuciyarta wani irin shakku da fargabansa takeji tace"mi zaka iya yimin Laweezi..!?".
"ai tunda zuciyar karnunka gareka bazaka iya yimin komai ba saboda matattar zuciyarka bazata bari ba..!".

Nuna kansa yayi yace cikin matuk'ar mamakin kalamanta yace"nine nakeda zuciyar kare da matattar zuciya Zeey..!?".
"ni kike zagi kina aibantawa saboda kin d'aukeni wani irin mugun mutum arayuwa..!?".
Zainab ta lece baki cikin tsagwaron rashin kunyar data motso mata tace"eh kai nake nufi idan bada kai nake ba ai babu wani mutum tsaye agabana sai kai..!".
Laweezi yaji zafin kalamanta har cikin k'ok'on ransa yayinda yaji tamkar an soka masa mashi a k'ahon zuci yace"zakiyi nadamar zagina arayuwarki saina babance miki tsakanin aya da tsakuwa..!".

"ai babu nadamar da zanyi fiyeda wadda nayi ayanzu saboda kaine silar rabani da iyayena da kuma tarwatsewar farin cikina...!".
"taya kake tunanin zan iya cigaba da zama dakai amatsayin miji bayan zuciyata cike take da zarginka akan kaine makashin iyayena..!".
"bana sonka! Bana sonka!! Bana sonka Laweezi har abada kada kayi tsammanin zan k'aunaceka azuciyata...!!!".

Laweezi ya sanya hannunsa ya toshe dodon kunnensa yace atsawace"keeeeee kisan irin kalaman da zaki gayamin fa idan ba haka ba zanyi miki abinda har abada bazaki tab'a mantawa dani ba..!".

"ya wuce wanda kayimin azzalumi maciyi amana mai fuska biyu bazaka tab'a yin k'arshe mai k'......................".Kafin ta k'arashe maganarta Laweezi ya d'aga hannunsa cikin matuk'ar bak'in rai da tafasar zuciya ya kifeta da maruka biyu masu k'yau wanda asanadiyyar haka saida ta saki rikitaccen k'ara tareda fad'awa k'asa adalilin marukan sun shigeta har cikin k'wak'walwa!.
Tana kwance tana kukan zafin mari wiwiwi kamar bazata daina ba taji muryar Laweezi daga sama yana cewa"tunda na fahimci cewar bakida mutunci 'yar iska kike to daga yau mun saka k'afar wando d'aya nida ke zaki gane kurenki...!".Yana kammala maganarsa yaja k'afafunsa fuuuuu ransa a b'ace yabar cikin d'akinta zuciyarsa sai tafasa takeyi masa.
yabarta kwance tana birgima a k'asa tanata zubar da kwallar zallar rad'ad'i azuciya alokacin ne takejin duniyar gaba d'ayanta tayi mata bak'ik'irin tareda fice mata arai, domin ta lura da fahimta da k'yau rayuwarta yake nema ba soyayya ta hak'ik'a yakeyi mata nan take ta fara tunanin rayuwarta ta baya rayuwar da tayi tareda iyayenta cikin matuk'ar farin ciki da tsantsar shak'uwa.

Abinciken da 'yan sanda sukeyi sun gano motar da Zainab ta fita da ita zuwa gidan k'awarta Samrat aranar da aka saceta,da kansu suka kira yah Hayatu yazo ya ganarwa idanunsa abinda yake faruwa bayan sun d'auki wasu bayanai acikin motar sannan aka kira mechanic yazo ya d'auki motar ya wuce da ita garejin kanikawa.

*TUSHEN LABARI*
Malam Sa'idu mahaifinsu Maijiddah bafulatanin asali ne daya taso aruggarsu ta fulani a k'ark'ashin mahaifinsa baffa Zubairu da mahaifiyarsa Inna A'i, sun taso shida yayansa Yunusa cikin tarbiya da rik'o da addinin musulunci domin duk da sun taso acikin rugga bai hana baffa Zubairu sakasu amakarantar allo ba.
Tunda safe suke kora shanunsu suje kiwo su dawo da yamma su wanke jikinsu suje makarantar allo yayinda Sa'idu ya maida hankalinsa sosai wurin k'ok'arin ya iya karatun allo, shi kuma Yunusa zuwa kawai yakeyi yana wasanninsa cikin yara idan akace yazo ya fad'i karatu yak'i yi ko yace bai iya ba, haka malamin zai sake gaya masa batare da gajiyawa ba haka dai lokacin tashinsu zaiyi batare da Yunusa ya k'aru da komai ba.

LAHANIWhere stories live. Discover now