LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 25*

Ab'angaren Yunusa kuwa abin ba haka yake ba domin ba wani soyayyar Lanti ke addabar zuciyarsa ba, shidai yana zaune da ita domin ya mori jikinta daga k'arshe ta biya masa buk'ata shikenan ya d'auketa abar hutawarsa yaji matuk'ar dad'i, dayake yarinyar akwai k'ok'arin gyara da tsananin tsabta shiyasa yakejin dad'in mu'amala da ita akowane lokaci.
Yayinda a b'oye kuma Yunusa yanada wani irin b'oyayyen hali wanda ko iyayensa basusan dashi ba balantana mutanen ruggarsu, da tsakar dare idan k'afa ta d'auke kowa yayi barci yake shiga gidajen mutane yana musu satar dabbobi da kud'ad'e masu yawa, idan kuma ya shiga cikin gidanka bai samu damar aiwatar da mugun nufinsa ba to kai ka shiga uku ka lalace saboda 'yarka zai samu yayiwa fyad'e ya gudu aci nemanshi ba'a ganshi ba domin ba'asan yana aikata mummunan d'abi'a bace shiyasa babu wanda zai zargeshi.
  haka mutanen ruggar ke wayuwar gari su riski wannan mummunan al'amarin dake addabar ruggarsu, saboda kowane magidanci ka kalli fuskarsa k'unshe take da tsagwaron bak'in ciki da tsananin tashin hankali mara misaltuwa! Domin gaba d'ayansu babu wanda Yunusa baiyiwa mugun lahani ba barinsa fintik babu ko kwabo ahancin d'uwawunsa,ganin ire iren k'alubalen rayuwar da suke fuskanta aruggar yasa shugaban ruggar ya sanya wakilan b'oye wad'anda zasu dinga lura da shige da ficen kowa saboda yaga sace sacen da fyad'en da akeyi cikin ruggar yayi yawa fiyeda tsammanin mai karatu.
Ganin shugaba ya saka muk'arabansa yasa Yunusa ya d'auke k'afafunsa ya rage sace sacen da yakeyiwa domin gudun tonuwar asirinsa abainar jama'a! Shiyasa har yanzu muk'araban shugaba suka kasa gano b'arawo ko k'warton daya addabi kafatanin rayuwar ruggarsu.

haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya Yunusa yana k'ara shahara da gunguma akan harakar fyad'e har ya zamo baya iya tab'uka komai idan ba yayi amfani da mace ba,har alokacin ganin ya girma yasa ya kakkab'e k'afafunsa da zuwa makarantar allo yayinda Sa'idu ya cigaba da zuwa har ya zamo shahararren malamin allo yana rubutu akan allo da kai babu inda zai gagareshi rubutawa saboda ya zauna ya karanci qur'ani da k'yau da zuciya d'aya.
Ganin ya zamo abin kwatance cikin al'umma yasa Inna A'i ta kasance cikin matuk'ar farin ciki akowane lokaci cikin suburbud'a masa albarka takeyi, yayinda shi kuma baffa Zubairu baiji wani dad'i sosai ba saboda bayason Sa'idu.
shi kuma gogan ganin tun ba'aje ko'ina ba Sa'idu ya fara samun d'aukaka da farin jini acikin mutanen ruggarsu yasa ya d'auki karan tsanar k'anensa ya sanya azuciyarsa, yaji aduniya gaba d'aya babu abinda ya tsana da k'ullatarshi azuciya fiyeda k'anensa Sa'idu yasha alwashin duk hanyar da zaibi saiya lalata rayuwarsa tareda gurb'ata masa farin cikin rayuwa!.

ab'angaren Sa'idu wanda ake kira da suna Malam Sa'idu ayanzu duk da k'arancin shekarunsa yana tsananin son iyayensa da d'an uwansa Yunusa, aduniya bai had'a k'aunarsu da komai ba duk daya fahimci kwata kwata yayansa baya sonshi hakan baisa ya daina bashi girma ba da darajashi.
Cikin haka ne Sa'idu ya koma makarantar allo da zama domin babban malaminsu ya jawoshi ajiki ya bashi babban matsayi acikin makarantar, wannan dalili ne yasa baya yawan zama gidan iyayensa akodayaushe yana can makarantar allo wannan matsayin da akaba Sa'idu shine sanadiyyar k'ara hab'b'aka wutar gaba azuciyar Yunusa saboda ayanzu ne nadamar tsayawa yayi karatu ya fara shigarsa saboda yasan daya tsaya yayi karatu da babu abinda Sa'idu zai nuna mashi arayuwa!.

Alokacin da Sa'idu yakai shekaru ishirin cifcif aduniya shi kuma yayansa Yunusa yanada shekaru ishirin da hud'u tsakaninsu dama tazarar shekara hud'u ne, to alokacin ne iyayensu suka bijiro musu da maganar kowanensu ya fitar da matar aure yayi musu aure, nan take Yunusa yayi sub'utar baki kada Sa'idu ya rigashi fad'a ya sanar musu yanada wadda yakeso mahaifinsa ya tambayeshi shi kuma yace masa d'iyar gidan shugaban ruggarsu yakeso bayan alhalin yasan Sa'idu k'anensa ke nemanta da aure, shine ya fad'i haka saboda yanason wani irin mugun rikici ya b'arke atsakaninsu.

LAHANIWhere stories live. Discover now