LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 40*

Maigadi ya wangale masa get suka fice daga cikin gidan da sauri, suna fara tafiya akan titi Labbo driver ya maida hankalinsa wurin tuk'insa can yace"hajiya ina zamuje..?".Aunty Maijiddah dake kallon mototin dake wulgawa akan tsakiyar titi murya asanyaye tace"gidanmu zaka kaini..".Labbo driver yace"uhmm hajiya".
cigaba da tafiya sukayi ahankali har suka k'araso bakin k'ofar gidansu Maijiddah Labbo driver ya parker motar tareda fitowa ya bud'ewa Aunty k'ofa ta rik'e da hannun Jawaheer,bayan ta fito ne ta kalleshi tace"zaka iya tafiya".
Labbo driver yace"k'arfe nawa zan dawo d'aukarki..?".
"k'arfe biyar na yamma zaka dawo..!".
Labbo driver cikin girmamawa tace"to hajiya..".
Aunty Maijiddah taja hannun d'iyarta suka bar wurin yayinda Labbo driver ya fad'a cikin motarsa yabar unguwar.

Aunty Maijiddah tana isowa tsakiyar filin gidan ta hangosu Ummi Aziza zaune suna tab'a fira Zainab tana lahe ajikin Umminta tana zuba surutu, sallamar da Aunty Maijiddah tayi ne yasa suka farga da zuwanta wurinsu fuskarsu asake cikeda matuk'ar farin cikin ganinta suka amsa mata,zaunawa Maijiddah tayi tana sakin murmushi afuskarta tace"Ummi ina wuni..".
"na sameku lafiya..?".
Ummi Aziza tace"lafiya k'alau kika samemu..".
"ya maigidanki..?".
Maijiddah tace"k'alau yake Ummi".
Zainab dake manne ajikin mahaifiyarta tace"Aunty sannu da zuwa".
"ashe zaki zo yau shine baki fad'amin ba inyiwa baby Jawaheer girki mai dad'i..!".
Aunty Maijiddah tace"yauwa tafiyar girshi ce shiyasa ban kiraki awaya ba..!".
Zainab ta tashi zaune ta waro fararen idanunta awaje tace"to Allah yasa alkhairi ne ya kawoki gidanmu..!".
"alkhairi ne yama kawoni wurinki k'anwata..!".
Zainab ta gyara zamanta tace"ina jinki Aunty..".
Ta kalli gefen Jawaheer tace"zo nan babyna..".
Jawaheer ta mak'e kafad'a cikeda matuk'ar k'yuya tace"yani juwa..".
Ummi Aziza ta tara mata hannu tana murmushi shimfid'e afuskarta tace"zo wurina Jawaheer rabuda Zainab kinji..".
Jawaheer ta mik'e tsaye taje wurin Ummi ta zauna saman cinyoyinta tana wani langwab'e mata ajiki.
"iyayin banza wato wurina ne bak'ya son zuwa ko Jawaheer..?".Inji Zainab tana kallon fuskar Jawaheer.
Jawaheer ta chuno bakinta gaba tana sakin murmushi.
"Aunty mu shiga cikin d'aki ko saboda wata k'ila maganar sirri ce..".
"eh mana hakan zaifi gaskiya..".

Har zasu mik'e tsaye sukaga su Inna Lantana sun fito tsakar gida suna zagin Ummi da k'yaro mata kalamai masu zafi da k'una azuciya.

"munafurcin banza anyi aure amma ba'a iya tsayawa gidan miji sai anzo yawon tsegumi saboda an gada awurin tsohuwa..!".Inna Lantana ta fad'a tana rik'e kwankwasonta cikeda son tashin hankali.
Gid'ad'o ya lece baki tareda wurgawa Zeey yace"ina ko zata iya zaman aure tunda ba'a nuna mata muhimmanci aure ba yawon tambad'arta takeyi any how..!.".
Zainab ta harzuk'a tace"kai kuwa yah Gid'ad'o waye ya sako bakinka..!".
"keee!Zainab kibi asannu bar ganin ina sonki ki nemi ki tozartani hakan bazai hana inyi guntu guntu naman jikinki ba..!".
"d'iyar matsiyata kawai..!".
Zainab tace"iyayena ba matsiyata bane saidai idan naka ne ma....................!".

Ummi Aziza ce ta daka mata tsawa cikeda tsananin b'acin rai tace"kul!Karki kuskura ki zagi iyayensa..".

Inna Lantana ta k'yallara ihu tace"ahayyeeehhhh aida kin barta ta zagemu wallahi dako na lahira yafi ta jin dad'i..!".
"shegiyar yarinya mara tarbiya...!".

Gid'ad'o ya hura hanci cikeda tink'ahon rashin ji yace"ai Inna banso ku katseta ba naso ku barta ta ida zaginku dana jibgeta yau babu ubanda ya isa ya rama mata...!".
Aunty Maijiddah ta marairaice fuskarta tace"please yah Gid'ad'o kayi hak'uri wannan ba girmanka bane fad'a da Zeey..!".
"dallah rufemin baki Maijiddah!Kinzo kina yimin wata nasiha sai kace kin ganni kafiri...!".
"ba haka bane manufata yaya Gid'ad'o..!"
"Allah ya tsareni in zamo yayan shahararriyar karuwa irinki..!".

LAHANIWhere stories live. Discover now