LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 48*

Barisster Hayatu ya kallesa cikeda tsananin tausayin abokinsa daya gauraye sassan jikinsa yace"Nazeer ka daina damar da kanka akan abinda kayi imani da cewar zaka samu,iyayensu Maijiddah suna matuk'ar k'aunarka hakama ita d'in karan kanta Zainab bana jin zata k'i ka domin bakada wani abin k'i ,matata ma kasan ba tun yau ba ta aminta dakai kazamo abokin rayuwar k'anwarta".
"to miye abin damuwa ko so kakeyi ka illata kanka bayan kafi kowa sanin damuwa babu abinda take haifarwa arayuwar d'an Adam sai lahani..!".
Idanun Nazeer suka chanza launi kallo d'aya zakayi masa ka hango yanayin damuwa kwance k'arara afuskarsa numfashi yaja yace"nasan da haka abokina amma bakasan irin yanayin da nakeji ba shiyasa kake ganin laifina,hmm wata rana har mafarki nakeyi akan zan iya rasa Zainab arayuwata domin so ake ashiga atsakaninmu..!".
"don't believe that dude sharrin mafarki ne kawai amma nayi matuk'ar imani araina kaine mijin Zainab sannan ka dage da yawan addu'ar ubangiji yayi muku katangar k'arfe akan masu son rabaku"..
"Zan yawaita addu'a barisster".
"wannan hanyar kad'aice zata fissheka".

************************

*BAYAN SATI D'AYA*
Laweezi ya shirya cikin bak'ak'en suit d'insa wad'anda suka k'ara bayyanar da farar fatarsa da k'yawon surarsa ya kawo glass bak'i ya manna a face d'insa, sannan yayiwa jikinsa wankan turare direct room d'in mahaifiyarsa Mama Halima ya nufa ya isketa kishingid'e akan gado russunawa yayi cikin ladabi ya gaidata saboda duk iskancinsa yana son mahaifiyarsa da tsantsar shakkarta bayason ganin b'acin ranta.
Amsa masa tayi cikin k'auna ta rik'o hannunsa d'aya tace"son wannan wanka sai ina..?".
"Zanje gidan mahaifin Zainab ne in gani domin naga har yanzu bai nemi ba gashi lokaci yana tafiya".
"Okay son ubangiji ya kiyaye hanya".
"amin ya rabbi".
"But kaida waye zaku tafi..?".
"nida Hudairu zanje domin yau bana sha'awar fita da bodyguards d'ina".
Shafar sumarsa tayi tana jijjiga kafad'arta tace"shikenan you go".
"Thanks mom".
Laweezi da sassarfa yaja k'afafunsa ya fice daga cikin room d'inta kai tsaye parking lot ya nufa ya shiga cikin wata irin kafirar had'ad'd'iyar mota wanda duba d'aya zakayi mata ka gane mai mallakarta sai wane da wane,tun kafin ya danna horn getman ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan kai tsaye ya nufi inda zai d'auki abokinsa Hudairu.

***********************
Zainab ce xaune saman kujera tana tankad'ar garin tuwo sai fira Ummi Aziza takeyi mata tana amsawa jefi jefi cikeda tsananin damuwa,dayake duk wani motsinta da fushin da takeyi dasu mahaifiyarta tuni ta harbo jirginta amma sai tayi kamar bata fahimci fushin da takeyi dasu ba.

Ummi Aziza tana gyara takalminta daya tsinke tace"Zainabu idan kin kammala aikinki zuwa anjima zan aikeki gidansu Samrat".

Asanyaye Zainab ta furta"to Ummi ki bari idan rana tayi sanyi zanje".

"ba matsala to".

Awaje wurin shagon baba Sa'idu yara da manyan mutane sai tururuwar sayen kayan masarufi suke zuwa yi,duk dayake kayan shagon sunyi rauni sosai amma bai hana baba Sa'idu godewa ubangiji ba domin ya hak'ik'ance yafi wani jin dad'i arayuwa.
Can saiga motarsu Laweezi ta k'araso gab da shagon sun kai tsawon mintuna ishirin suna jiran mutane su tsagaita,babu dad'ewa yara suka jinkirta da zuwa.
Atsanake Laweezi yace"Hudairu mutane sun rage fito muje inje ta bakinsa".
Hudairu ya gyara zamansa yace"kaje kaji abinda zai fad'a mana".
"nufinka na tafi ni kad'ai?".
"eh duk yadda kuka zanta kazo ka sameni".
"haka za'ayi abokina".

LAHANIWhere stories live. Discover now