LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 69*

Sun dad'e sosai suna k'usu-k'usu bana iya jiyo abinda suke zantawa akai,ganin haka ne yasa naga babu amfanin tsayuwata naja k'afafuna nayi gaba.
Zainab bayan ficewarsa daga gida taji jikinta yayi matuk'ar sanyi gabanta sai d'ar d'ar yakeyi,nan da nan ta tsinci kanta da fad'uwar gaba wani irin fargaba da zullumi ne ke kawo mata farmaki azuciya,ta rasa dalilin dayasa Laweezi ya shigo mata cikin d'aki arikice d'azu yanayinsa kawai ta duba ta hango bak'in ciki bayyane k'arara afuskarsa.
Jan numfashi tayi cikin kasalalliyar murya tace"ubangiji dai yasa ba wani ne ya tab'oshi ba kada yazo ya sauke fushinsa akaina..".
"Bazan ma sauke fushina akanki ba".Taji saukar muryarsa daga sama da sauri ta waigo idanunta suka fad'a cikin nashi daburcewa tayi adalilin ganinsa agabanta alokacin da batayi tsammani ba.
Bakinta yana rawa tace"yau..she...ka..da..wo..?".
Laweezi ya lece leb'e yace"yanzun nan na dawo Angel".
Duk'ar da kanta k'asa tayi tace"sannu da zuwa".
"Uhmmm Angel".
Shiru ne ya biyo baya domin babu wanda ya sake magana acikinsu Laweezi sai kad'a kai yakeyi yana jujjuya maganar k'ararsa akotu,a k'ark'ashin ransa wani irin mololon d'aci da rad'ad'in abinda barisster Hayatu yayi masa yakeyi.

Ganin yayi shiru yasa Zainab ta karkace baki tace"mi yake damunka..?".

Laweezi yayi ajiyar zuciya yace"Zainab yayanki Hayatu mijin Maijiddah ya kaini k'ara kotu akan suna son araba aurenmu,nasan zakiji dad'i matuk'a azuciyarki domin bak'ya son cigaba da zama dani saboda ba k'aunata kikeyi ba..!".
Duk da har aranta taji dad'in abinda barisster Hayatu yayi masa amma dayake ta iya kissa da kisisina ta langwab'e kai cikin marairaicewa tamkar zatayi kuka tace"kayi hak'uri mijina kwata kwata banida labarin cewar yah Hayatu sun kai k'ararka kotu dana sani bazan bari suyi k'ararka kotu ba".

"Nasan baki sani ba Zeey shiyasa na fad'a miki ko akwai wani taimakon da zakiyimin idan muka halarci kotu..".

"Wane irin taimako kake buk'ata..?".

Gyashi yayi cikin tsantsar damuwa yace"so nakeyi kiyimin halacci arayuwa idan muka had'u akotu karki goyi bayan mijin yayarki ki goyi bayana Angel..".
"Nayi miki alk'awarin dukkan abinda kikeso shi zanyi miki kuma bazan k'ara musguna miki ba agidana..!".

Cikin zuciyarta tace bak'in munafuki sai yanzu kasan cewar bazaka k'ara musgunamin ba bayan aikin gama ya gama,hmmm ai wannan karon bazan tab'a yarda ka k'ara cutar dani ba but afili ta saki murmushin munafurci tace"karka damu heart desire zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari domin k'aunar da nakeyi maka bazai tab'a bari inci amanarka ba..".

Laweezi yace"shikenan ba damuwa Angel".

((++))((++))((++))((++))((+

*BAYAN SATI D'AYA*
Ranar lahadi da misalin k'arfe tara 9:00am su Aunty Maijiddah suka shirya da wuri bayan sunyi breakfast,domin ayau ne zasu fara halartar kotu akaro na farko adalilin k'arar Laweezi da sukayi nason ya saki Zainab saboda irin k'untatawa rayuwarta da yakeyi.

Suna gama shiryawa suka rankaya har parking lot suka shisshige cikin mota barisster Hayatu ya rik'o rigar aikinsa ya saka abayan kujera inda babu kowa,danna horn yayi da k'arfi maigadi ya wangale musu get suka fice agaggauce daga cikin unguwar.

Ab'angarensu Laweezi tun cikin tsakiyar dare ya kasa runtsawa saboda baya cikin natsuwarsa, d'aci da rad'ad'in zuciya kawai ne yake fama dashi ayinin ranar k'unshewa yayi cikin d'aki ko d'igon ruwa baisha ba.
Mama Halima dake zaune parlour ganin har yanzu Laweezi bai fito ba yasa ta d'auki tiren abinci ahannunta ta nufi room d'insa,a jingine ta iskoshi idanunsa alumshe suke kamar mai barci alhalin idanunshi biyu jin motsin tafiyar mutum ne yasa ya bud'e idanu ahankali,ganin mahaifiyarsa ce yasa ya fad'ad'a fuskarsa da murmushi domin kada ta hango fargaba da damuwa akan fuskarsa,maida masa martanin murmushinsa tayi tace"son duk yinin yau baka fito ba kana d'aki k'unshe ko ruwa banga kasha ba".

LAHANIWhere stories live. Discover now