LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 31*

Saida Inna Wuro ta kammala nazari da duban yatsunta da k'yau taji gabanta ya fad'i dummmm hankalinta ya tashi ad'arare ta mik'e tsaye tana salallami tace"wayyo naga ta kaina ni Dije mi zan gani haka Lanti..!?".Lanti ta zumb'ura baki tace"mi kika gani Innata da kike saka salati..!?".Inna Wuro ta dinga sharce zufan dake tsiyayo mata ajiki zuciyarta cunkushe da tsantsar tarin damuwa da rashin walwala ta koma ta zauna tace"Lantana".
Jin mahaifiyarta ta kira ainahin sunanta yasa ta fahimci cewar duk maganar da zatayi mata mai matuk'ar muhimmanci ce shiyasa ta maida natsuwarta wurinta tace"na'am Innata".
Inna Wuro taji jimm cikeda tsananin yadda zata tunkari mahaifin Lanti da wannan mummunan maganar tace"ina ganin fa tun ranar da kikace 'yan fashi sun tareki ahanya sunyi miki fyad'e kika kwashi cikin shege...!".
Arazane Lanti ke duban fuskar mahaifiyarta cikin matuk'ar damuwa domin bata tab'a zaton zata d'auki cikin shege amararta tace"cikin shege fa kikace Inna..!?".
"babu shakka kina d'auke da ciki Lanti..!".
Lanti ta aza hannunta saman kai ta rausayar da kanta cikin tsananin tashin hankali tace"asirina ya tonu Inna ya zanyi da rayuwata..!?".
"yanzu idan wannnan maganar ta fita awaje mi mutane zasu d'aukeni..!?".
kai tsaye Inna Wuro ta bata amsarta tace"mazinaciya zasu d'aukeki..!".
hawayen takaici ne suka dinga sintiri afuskarta alokacin ne takejin k'asan zuciyarta yana mata wani irin k'una tace"Inna ya zanyi da rayuwata ina zan saka zuciyata inji sanyi araina..!?".
dafa kafad'arta Inna Wuro tayi tace"share hawayenki 'yata zanyi tunanin mafita in gani ko za'a samo sayyu(maganin gargajiya) in jik'a miki kisha cikin ya zube..!".

Lanti ta jijjiga kanta alamar tsoro da fargaba suka bayyana k'arara afuskarta tace"bazan iya sha ba Inna mutuwaaa akeyi..!".

"to idan mutuwa akeyi bazaki sha ba kenan...!?".

"gaskiyar zance bazan iya ba domin ina jin tsoron insha in mutu Innata...!".

Inna Wuro ta k'yara mata harara kamar idanunta zasu fad'o k'asa tace"ai ko kinsha idan lokacinki baiyi ba bazaki mutu ba idan lokacinki kuma yayi ko baki sha ba zaki iya mutuwa..!".
"domin haka ki natsu ki kwantar da hankalinki babu abinda zai biyo baya sai alkhairi..!".
"In..na..ba..fas..hi...ba..ne..suk..a..ta..re..ni.....ba..!?".Ta fad'a bakinta yana rawa atsorace.

Inna Wuro ta maimata maganar cikin kanta tace"ba 'yan fashi bane suka tareki ba su waye suka tareki Lanti fad'amin gaskiyar abinda ya faru akan hanyarki ta dawowa..!?".

Lanti ta saka lallausan hannunta ta goge hawayen dake sintiri akuncinta tace"Yunusa ne ya tareni acikin dokar daji..!".
"ya tareki adokar daji kuma wane Yunusa kike nufi kenan Lanti..!?".Ta k'yaro mata tambaya cikeda son jin gamsasshiyar amsa.

"na gidan baffa Zubairu da Inna A'i nake nufi..!".

Inna Wuro tace"to ina saurarenki bani labarin abinda ya gudana atsakaninku...!".

Lanti ta karkace baki ta kwashe labarin duk abubuwan da suka wakana atsakaninsu tun daga farkon alak'arsu har k'arshe ta fad'awa Inna Wuro, babu abinda ta b'oye mata domin barin kashi aciki baya tab'a maganin yunwa kuma tasan itace zata k'watar mata 'yancin kanta.

bayan ta k'arashe sanar mata labarin Inna Wuro ta buga kuwwa da razananniyar k'ara tace"tafd'ijam lallai yau za'ayi tashin duniya acikin ruggar nan..!".
"garama da kika fad'amin cewar Yunusa ne yayi miki ciki kinga kenan ko mutuwa zaiyi saiya aureki..!".
"saboda haka tashi ki sako hijabinki muje gidansu ayita ta k'are ko ya amince ya aureki ko asirinsa ya tonu cikin ruggar nan kowa yasan miyagun abubuwan da yakeyi..!".

LAHANIWhere stories live. Discover now