LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 72*

Aunty Maijiddah ta k'ara gaba rataye da handbag d'inta a kafad'a barisster Hayatu ya rik'o ledodin ahannunsa ya kulle motar da key,kafin ya juyo har Maijiddah ta shige cikin parlour da sassarfa yabi bayanta har ya k'araso cikin tsakiyar parlour su Mahafuz dake ruk'unk'ume ajikin Ramatu,jin muryar daddynsu yasa suka saketa suka shek'o da gudu sukayi tsalle suka rungumesa,wani irin sansanyar farin ciki ne ke ratsa jinin jikinsa alokacin daya ji 'ya'yansa shafasu ya dingayi yana sakin k'ayataccen murmushi can ya jayesu tareda rik'o hannayensu suka k'araso wurin Aunty Maijiddah data kwanta akan 3 seater agajiye, asanadiyyar ta gaji da yawa tayi wulli da handbag,takalmi da d'an kwalli tana sakin nishin gajiya.

Ramatu ce ta gaidashi ya amsa mata cikin jin dad'i da tsantsar k'aunar k'anwarsa yace"Rahama ya kikaji da bari-bari..?".

Ramatu ta sunkuyar da kanta k'asa tace"yaya kuna fita bada dad'ewa ba sukayi barci ai..".

"Kice yau kam baki sha rashin ji ba".

"Gaskiya ban sha ba yaya".

"To kunci abinci..?".
Ramatu tace"eh munci".

Barisster Hayatu ya juya ya kalli k'wayar idon Maijiddah yace"ni zan shiga ciki in watsa ruwa ajikina na gaji da yawa".

"Ok ba matsala yanzun nan zan biyoka..".

Barisster Hayatu tuni ya isa matattakalar yahau ya fad'a cikin d'akinsa,yabarsu Mahafuz sunata wasaninsu aparlour hayaniyarsu ce ya dami Aunty Maijiddah ta duk'a ta kwashi handbag, d'an kwali ta d'auki kayanta ahannu ta nufi hanyar d'akin mijinta.

[[[[]]]][[[]]]][[[]]]][[[]]]][[[[]]]]]]

Jummalo 'yar aikin Mama Halima ce ke wankewa mata zannuwan gado manyan robobi da bokitaiya ne jibge agabanta,hajiya Halima tana tsaye awindow tana hango dukkan ayyukan da take gudanarwa anatse.
Wayarta ce ta fara tsura nan ta saki labulen window ta jawo wayar sunan data gani saman screen ne ya sanyata sakin murmushi, ahanxarce ta d'aga wayar Laweezi ya gaisheta cikin ladabi ta amasa masa cikeda tsananin k'auna,anan ne yake fad'a mata gashinan tafe shida Hudairu inji akwai abincin dazai ishesu,Mama Halima tace karka damu ko abincin mutum goma kakeso zaku samu,wani irin sanyi yaji azuciyarsa cikin soyayyar mahaifiyarsa wadda bai had'ata da komai aduniya ba yace mata suna nan tafe tace sai kunzo sannan sukayi sallama da juna Laweezi ya fara katse wayar.

Mama Halima ta ajiye wayarta akan gado ta fito filin harabar gidan inda Jummalo take hada-hadar wanke zannuwan gado tace"Jummalo".
Jin an kira sunanta daga sama ta d'ago fuskarta tace"na'am hajiya".

"Akwai isasshen dafaffen abinci agidan nan..?".

"Eh akwai hajiya bak'i zakiyi ne..?".

"A'a Laweezi da abokinsa ne zasu zo gidan nan".

Jummalo ta karkad'a kai tace"zasu samu koda na mutum goma ne kinsan gidan nan akwai bak'i masu kawo ziyara shiyasa nake girka abinci da dama".

"Ai kuwa kin k'yauta Jummalo bari inje in zuba musu komai atire".

"To hajiya".

**** **** **** ***** *****

Mama Halima ta bud'e sabbin kuloli ta wanke tass ta zuzzuba musu abinci k'aton jug ta d'auko ta cika musu lemun abarba mai sanyi ta rufe,tire ta d'auko ta d'ora kulolin akai ta d'auka ta kai musu a a main parlour,tana ajewa ta jayo k'ofar parlourn ta rufe parlournta ta koma ta zauna cikeda gadara.

LAHANIWhere stories live. Discover now