LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 42*

Samrat ta jijjiga kanta kamar k'adangarwa tana ajiyar numfashi ahankali tace"Zeey kenan daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i..!".
"kibi dai asannu kada ki fad'a soyayyar wanda baki sanshi ba bakisan waye shi ba wace irin sana'a yakeyi? Domin gujewa afkawa cikin tarkon wahala da nadamar rayuwa..!".
"saboda maganar gaskiya naga wautarki da har kika bari saurayin ya sace miki zuciya da ruhi..!".
Zainab ta yamutsa fuskarta cikin haushin zancenta tace"dakata Samrat naji bayaninki tashi muje gida kada yamma tayi..!".Samrat tace"a'aaaa Zeey daga fad'ar gaskiya sai kiji haushina..!".
"to ba komai duk irin tsarin da kikayiwa rayuwarki ke kika sani..!".
Zainab ta b'oye mata ainahin abinda takeji asiyasance tace"ko d'aya Samrat banji haushin maganarki ba kawai dai cikina ne ya fara k'ugin yunwa shine na matsu bamu komai gida ba..!".
Samrat ta tashi tsaye tace"Zeey karki chanza salon abinda yake cikin zuciyarki saboda duk wani dabararki bazaki tab'a iya yimin wayo ba..!".
Zainab itama ta mik'e tsaye tareda rik'e handouts ahannunta tace"duk abinda kikaga na fad'a daga zuciyata ne..!".
"saboda haka mu ajiye chapter saurayi mai mota gefe kinji..!".
"naji tunda soyayya tana neman rufe miki idanu ga miji nagari daya dace dake kinason kiyi *SAKACI* har ya sub'uce miki asanadiyyar wanda bakisan shi ba..!".
Zainab ta rik'e kanta cikeda rashin son maimaita zance d'aya tace"kiyi hak'uri kibar wannan maganar Samrat nina daina wlh..!".
"kedai kika sani..!".

Atare suka jera suna tafiya har suka k'araso bakin get d'in makarantar Samrat sai mita takeyi tana mata nasihar akan tabi ahankali kada takai mahalaka, ita kuma Zeey dole tayi tana sauraronta domin tasan Samrat akwai nacin magana idan batayi ba hankalinta bazai tab'a kwanciya ba.

suna tsaye agefen titi har sun tari keke napep sukaji ana danna horn da k'arfi da azama suka juyo tare idanunsu ya sauka akan Laweezi daya fito daga cikin motarsa yana takun k'asaita hannunsa rik'e da kafceciyar phone.
Yana isowa wurinsu yayi musu sallama Samrat ta amsa adak'ile saboda ta tsani atsayar da ita akan titi arayuwarta.
Dak'yar ya fisgo maganar yace"sarauniyar mata bai dace ace kun shiga keke napep ba wannan ba girmanki bane..!".
Samrat tayi tsagal da sauri tace"kai malam wa nene kai...!?".
"miye dalilinka na tsayar damu akan titi..!?".
Laweezi saida ya k'are mata kallo na wani lokaci ya lashi leb'en bakinsa yace"k'awarmu kiyi hak'uri idan na b'ata miki rai..!".
"amma idan kikayi hak'uri zaki fahimci wa nene ni anan gaba kad'an idan na mallaki k'awarki amatsayin matata ta sunnah..!".
Samrat ta kalli fuskar Zainab taga ta duk'ar da kanta k'asa sannan ta maida dubanta wurinsa tace"hmmm ce maka akayi k'awata sonka takeyi ne...!?".
"to ka sani tun wuri kaje ka nemi daidai dakai domin babu wata sauran k'ofar da zaka shiga azuciyar k'awata saboda tuni wani wanda ya fika sa'a da rabo ya sace zuciyarta..!".
Laweezi ya furzar da iskar bakinsa cikeda jin zafin kalamanta yace"yarinya kenan bakisan wa nene Laweezi Haruna Ninja ba shiyasa kike fad'amin maganganu son ranki..!".
"ni mai sa'a ne arayuwata duk abinda nakeso saina mallakesa saboda haka ki iya bakinki..!".
"sanin ko kai waye bayada wani amfani agareni..!".

"kinada ja kenan..!?".

Samrat tace"k'warai kuwa".Da azama ta fisgo hannun Zainab suka fad'a cikin keke napep yayinda Laweezi yayi tsaye k'yam yana mamakin k'arfin halin k'awar gimbiyarsa.
yana kallo mai keke napep ya tadda napep d'insa ya fara tafiya akan titi aida sauri ya fad'a cikin motarsa yabi bayansu yana tafiya ahankali domin yaga gidansu Zeey yarinyar da yaji k'auna da tsantsar soyayyarta ta k'ara ninkuwa azuciyarsa.
yana nesa dasu kad'an aka fara ajiye Samrat sannan mai keke napep ya k'ara tafiya ya isa wani madaidaicin gida ya ajiye Zainab yana hangota ta ciro kud'i cikin handbag ta biyasa kud'insa, ya tadda napep d'insa ya k'ara gaba har Zainab ta fara taku zata shige cikin gidansu alokacin ne Laweezi ya k'araso da motarsa gab da ita yace"k'anwata please ki taimaka ki saurareni ko na minti d'aya..!".

LAHANIWhere stories live. Discover now