LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 76*

Su barisster Hayatu sunje duk inda ya dace suje amma basu ga ko masu kamadasu Mahafuz ba,ganin haka ne yasa suka yanke shawarar sanarda DPO Usman abinda ake ciki kai tsaye hanyar zuwa gidansa suka nufa suna magana cikin mota.
Barisster Hayatu ya rausayar da wuya yace"Nazeer da mun hak'ura da sanarwa DPO Usman abinda ake ciki saboda na riga nakai photunansu akafafen yad'a labarai kuma nayi report a police station.".
"Duk da haka ai ya kamata ya sani ko akwai wani taimakon dazai iya yi mana..".
"Aganinka zai iya tab'uka wani abu ne akan wannan maganar naga ko akotu babu abinda yake iya yi idan muna gabatar da shari'a..".
Doctor Nazeer yayi murmushin yak'e yace"hmm barisster Hayatu aiko babu abinda yake iya tab'ukawa ya cancanta ya sani..".
"Tunda baka d'aukar shawarata saboda sonsu Jawaheer ya rufe maka idanu muje to..".

"Ai ko baka amince ba zuwa zamuyi..".

"Kaidai ka sani da shisshigi..".
Doctor Nazeer ya cigaba da tuk'insa cikin natsuwa bai k'ara tanka masa ba har suka k'araso adaidai bakin get d'in gidan DPO Usman,anan suka hangoshi tsaye da Alhaji Yunusa k'anen baba Sa'idu suna maganganu atsakaninsu suna babbakar dariyar farin ciki,duk dayake basa iya jiyo abinda suke fad'a amma kallo d'aya sukayi musu suka gano cewar suna cikin tsantsar nishad'i da kwanciyar hankali mara misaltuwa.

Cikeda matuk'ar mamaki suke kallonsu barisster Hayatu ya kasa hak'uri yace"Nazeer kalli wannan abin mamaki ko miye had'in baba Yunusa da DPO Usman haka..?".
Doctor Nazeer ya rik'e baki cikin haushi yace"Allah masani amma daga gani ba yau ne suka fara sanin juna ba..".

"Alamu sun nuna haka doctor..".

Da sauri doctor Nazeer ya kalli fuskar Hayatu yace"wane irin alamu ne suka nuna haka..?".

"Yanayinsu kawai zaka duba ka gano cewar akwai wata alak'a mai k'arfi atsakaninsu doctor Nazeer,idan babu alak'a mizai sanya suna fira da juna harda k'yak'yatawa tamkar wad'anda aka basu kujerar makkah..".
Doctor Nazeer yace"abar maganar kada mu zargesu Hayatu idan ma wani abu kake tunani akansu ka daina Laweezi shine ya sanya asacesu baby Jawaheer..".

"Miye hujjarka akan wannan magana..?".

Doctor Nazeer ya saki gwauron numfashi cikin matuk'ar zullumi yace"domin shine kake k'ok'arin ganin ka raba aurensa da Zainab..".

Barr Hayatu yayi jugum kamar bazaiyi magana ba can yace"to ai ba'a nan gizo ke sak'ar ba wasu abubuwan dake faruwa lullub'e suke acikin duhu wad'anda babu mai iya warwaresu sai wanda abin ya faru akan idonshi..".
"kuma maganarka gaskiya ne Hayatu to yanzu muyi masa bayanin abinda ke faruwa komu juya..?".
"Tunda munzo mu fad'a masa damuwarmu kada mu juya su zargemu..".

Saida suka gama yanke shawarar yadda zasu fuskanci DPO Usman da zancen, sannan suka firfito daga ciki suka k'araso wurinsu da sallama DPO Usman ne kawai ya amsa musu sallamar amma baba Yunusa murtuk'e fuska yayi yana jifansu da wani irin walak'antaccen kallo mai nuni da tsananin tsana da rashin so,basu damu da kallon dayake aika musu ba doctor Nazeer yayi gyaran murya yace"DPO Usman wurinka muka zo".

DPO Usman ya maida hankalinsa akan Nazeer yace"ina saurarenku".

"Munzo ne mu sanar maka cewar an sace mana 'ya'ya Jawaheer da k'anenta Mahafuz..".

LAHANIWhere stories live. Discover now