LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Tabbas mai k'aunarka shike k'ok'arin ganin akowane lokaci ya faranta maka rai,lovely sister kin cancanci dukkanin yabo tareda d'umbin k'auna daga gareni akan jajircewarki wurin bayyana soyayyarki gareni,sister *Faeezation* nakan rasa wace irin kalma zanyi amfani da ita wurin nuna miki tsantsar farin cikina,nagode matuk'a ubangiji ya biyaki da sakamakon Alkhairi arayuwarki._.

*PAGE 52*

Barisster Hayatu yana ficewa bai zarce ko'ina ba sai police station yana isowa can yayiwa DPO bayanin abinda ake ciki,dayake polices d'in susan barisster Hayatu fitaccen barisster ne wanda yayi suna akewayen jahar baki d'aya,batare da gardama ba DPO ya had'ashi yaransa hud'u cikin motarsu mai d'auke da tambarinsu,nan take yah Hayatu ya shige cikin motarsa suka biyosa baya suna tafiya ahankali   har suka k'araso cikin filin asibitin,parker mototinsu sukayi suka firfito daga ciki kai tsaye yah Hayatu ya jagorancesu har room d'in da aka kwantar da baba Sa'idu duk inda suka gifta ratsewa kawai akeyi ana basu hanya ana kallonsu.
  Suna isowa bakin k'ofar suka kunna kai atare tsakiyar room d'in yayinda suka iskosu doctor Uwaisu suna xazzaune saman kujerin roba.
Ganin barisster Hayatu da police's hud'u yasa doctor Uwaisu yace"har ka dawoo?".
"eh doctor".
"maganar gaskiya kayi sauri".
"ba dole ba wannan case d'in ba k'aramin abu ne doctor".
Barisster Hayatu ya umurci doctor Uwaisu daya k'ara bincike akan idanun police's d'in ba gardama yahau bincike akan gawar baba Sa'idu,an kai tsawon lokaci yana bincike the same result takardar ta sake basuwa wato dai pillow akayi amfani dashi aka kashe baba Sa'idu! Doctor da kansa ya mik'awa shugaban police mai suna ASP.Nafseen Adam da sauran abokan aikinsa,saida ya karanta takardar da k'yau sosai yaba sauran suka karanta sannan ASP.Nafseen yayi rubuce rubuce cikin wata doguwar takarda result d'in ya rik'e ahannu can ya zura takardun biyu a aljihunsa.
Saida akayi komai agaban idanunsu sannan suka bada umurnin ad'auki gawar aje gida ayi mata wanka,hardasu aka tafi gidan baba Sa'idu yayinda su Ummi Aziza basu fahimci cewar ubangiji ya amshi ran baba Sa'idu ba domin daga barisster Hayatu har doctor Nazeer babu wanda yakeda k'arfin halin sanar dasu abinda ake ciki,basu lura da har yanzu baba Sa'idu kwance yake lullub'e da farin zane ba saida akazo gida sukaga mutum kwance tamkar gawa!.
Alokacin ne Ummi Aziza ta samu sararin cewa"Hayatu ya naga kun lullub'awa baban Zainabu farin k'yalle..?".
"miye sameshi..?".
Jin yadda taketa jefo masa tambayoyi yasa hankalinsa ya k'ara tashi,ganin baiyi magana shiyasa Aunty Maijiddah ta kallesa ad'ad'are cikin matuk'ar karayar zuciya tace"dear kana jin Ummi tana tambayarka kayi shiru miyake faruwa ne wai..?".
"Jiddanah saidai hak'uri amma ubangiji.........".Sai kuma ya kasa k'arasa maganarsa domin baisan yadda zasu d'auki abin ba.
Ummi Aziza ta fara sharar zufa ta juya ahankali b'angaren doctor Nazeer tace"Nazeer tundashi yana neman ya b'oye mana abinda yake faruwa ka dubi girman Allah ka gaya mana miye ya sami baban Zainabu..?".
"Ko ya rasu ne shine kuke neman rufe mana ainahin abinda yake faruwa..?".
Sirarrun hawayen tausayinsu ne ya zuba afuskar doctor Nazeer cikeda rashin walwala ya gyad'a mata kansa alamar eh ya rasu!.
Wato hasashenta ne ya zamo gaskiya domin ta fahimci cewar eh yake nufi bud'ar bakinta tace"ina lillahi wa inna ilaihirraji'una! Ubangiji Allah ya jik'anka Sa'idu yakai haske kabarinka..!".
"Allah sarki rayuwa kenan azamanmu na duniya baka tab'a yimin laifi ba kullum cikin farantamin kake tareda sauke hak'k'ina dake rataye awuyanka tabbas ni Aziza nayi matuk'ar rashin abokin rayuwa mai halacci da sanin darajar d'iya mace..!".
"Ummi mi kike nufi kardai kice babanmu ya tafi inda ba'a tab'a dawowa..!?".
"Kardai kice babanmu ya tafi ya barmu cikin wannan duniyar mai cikeda k'unci da bak'in cikin rayuwa..!?".Cewar Aunty Maijiddah alokacin ne ta fashe da wani irin kuka tana shassheka.
  Zainab ta d'ora hannayenta akai tace"Ummi baba ya rasu da gaske..!?".
"Ya rasu batare da yaga aurena ba..!?".
"Ummi kice mana k'arya ne babanmu doguwar suma yayi ba mutuwa yayi ba..!".

LAHANIWhere stories live. Discover now