LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 37*

Aziza tayi jugum cikeda tsananin sanyin daya mamaye ilahirin gangar jikinta hak'ik'a batason yadda Gid'ad'o ke neman tirsasa Zainab ta soshi, da kuma takura mata akan sai tayi soyayya dashi bisa dole amma babu yadda zatayi dashi ne shiyasa take kaffa kaffa da d'iyarta saboda tana gudun ta afka cikin tarkonsa!.
tagumi tayi da hannunta cikin raunanniyar muryarta mai nuni da tsantsar damuwar dake tattare da ita tace"Zainabu na rok'eki ki dinga taka tsan-tsan da kanki ki daina shiga sabgarsa..!".
Zainab tace"Allah Ummi bana shiga sha'aninsa shine yake bibiyata har school yana damuna akan sai nayi soyayya dashi..!"."Naji amma duk da haka ki kiyaye..".Zainab ta langwab'e kanta tace"zan kiyaye Ummi..!".
"da yafi miki..!".
Zainab ta mik'e tsaye ta cire tufafinta saboda wani irin fitinannen zafi da takejin ya gauraye cikin k'ofofin jikinta ta d'auko zane tayi d'aurin k'irji tace"Ummi mi kika girka yau..!?".
Aziza ta murmusa cikeda tsantsar tausayinta tace"waina da miya ce na girka..!".
Zainab ta saki murmushinta mai k'yau tace"yeeee naji dad'i sosai Ummi bari inyi wanka inzo inci..!".
"akwai sauran furar da kika ajiyemin ko..?".
Aziza ta harareta cikin k'auna tace"eh na ajiye miki Zainabun baba nasan ai duk had'amarki bazaki iya cin waina ba sannan kisha fura...".
"waye ya gaya miki Ummi saina ci dukansu..?".
"to shikenan zan gani idan zaki iyayi..".

Zainab bata k'ara magana ba ta d'auko soso da sabulun wanka zunbulelen hijabinta ta zura ajikinta, sannan ta fito tsakar gidan ta d'ebi ruwa afamfo takai toilet ta aje har zata shiga ciki ta tsinkayo muryar Gid'ad'o yana ce mata"idan kika kuskura kika shiga toilet wallahi ayau saina b'alla k'ofar makewayin na ganki zindir..!".
Azabure ta waigo idanunta suka fad'a cikin nashi cikeda matuk'ar k'arfin hali tace"auuuu yaya Gid'ad'o iskancinka har yakai minzalin zaka iya b'alla k'ofar toilet domin kaga tsiraicina...!?".
  "to karka fasa idan na shiga ina wanka ka tattaro duka mutanen garin nan kazo dasu ka b'alla k'ofar ka gani shin nida kai waye zaisha tsinuwa agun mutane..!".Ta fad'a amasifance.

Gid'ad'o yayi k'yafci yace"zaki gane bakida wayo Zainab saina koya miki hankali..".

"mu dai koyawa juna..!".Zai sake magana kenan saiga Basiru k'anensa yazo wurinsa yace masa Innarsu tana kira bisaga dole Gid'ad'o yabi bayansa, ba domin yana so saboda yaso ya tozartata da kunyatar da ita atsakiyar gida.

Zainab ganin sun wuce ne yasa tayi addu'ar shiga toilet ta kunna kai ciki tareda sanya sakata.

**********************
*BAYAN WATA BIYU*
Zainab takai ziyara gidan Aunty Maijiddah ta isketa cikin kitchen tana kichaniyar girka abinci yayinda Jawaheer ke biye da ita duk inda tabi tana damunta da kukan banza, abin duk ya taru ya damu Maijiddah gashi tana son yin girki gashi Jawaheer ta dameta da koke koken banza, tana tsaye cikin tana shawarar irin kalar girkin da zatayi domin tun jiya yah Hayatu ya sanar mata abokinsa doctor Nazeer zaizo wurinsa.
Shiyasa take tunanin kalar abincin da zatayi ta burge mijinta kamar daga sama taji muryar Zainab tana sallama tareda nufo kitchen, wani irin rikitaccen dad'i Aunty Maijiddah taji ya d'arsu azuciyarta har ta kasa b'oyewa Zainab.
Zainab tana k'arasowa wurinta taga Aunty tana sakin murmushin farin ciki tace"Aunty Maijiddah miye kika samu naga kinata farin ciki..!?".Ta fad'a bayan ta d'auki Jawaheer tana goge mata majina da hawayen fuskarta.

Aunty Maijiddah tace"kedai dole inyi farin ciki k'anwata domin kinzo adaidai lokacin da nake buk'atarki kinga kenan fad'uwa ce tazo daidai da zama..!".

LAHANIWhere stories live. Discover now