LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 64*

Zainab ta dad'e cikin matsanancin mamaki wanda yaso ya rikita k'wak'walwarta ad'ad'are gudun kada ya risketa cikin d'akin ta maida akwatin ta rufe,zazzafan zufan dake zuba ajikinta duk da sanyin A.C dake cikin d'akin adalilin ta shiga wani irin yanayi wanda ya haifar mata da mummunan tashin hankali azuciyarta,bayan ta maida ne cikeda rashin walwala ta fito daga ciki ta zura key ta kulle k'ofar d'akin ta yadda bazai tab'a fahimtar an shiga ciki ba.
Tambayoyi ta dinga jerawa azuciyarta tace mi Laweezi yakeyi da bindiga ko ajiyarta aka bashi sannan mi nene dalilin dayasa bayason ta shiga cikin d'akinsa,anya ba kashe yaran mutane yakeyi ba?Wani b'angaren na zuciyarta ya kwab'eta yace mijinta baiyi kamada masu kashe mutane ba to kodai d'an mafiya ne..!?.Ire iren wad'annan tambayoyi ne sukayita kai mata farmaki akowane sak'o da lungu na zuciya,taso ta zauna parlour tayi nazari amma saita kasa zama direct room d'inta ta fad'a ta maida keys wurin b'oyensu tufafinta ta cire ta fad'a cikin bathroom tayo wanka ko zata samu sararin tunani da dogon nazari.

((((()))))(((()))))((((()))))(()

  Bintalo ce tayi shirinta tsab cikin riga da sicket ta kawo dogon hijabi ta aza saman kayanta k'aramar pause ce ahannunta,fitowa tayi ta iske Ummi Aziza saman tabarma tana askewa Khalilu gashinsa da razor blade.
cikin matuk'ar ladabi da girmamawa Bintalo tace"Ummi na shirya ki kawo kud'in inyi sauri in dawo".
Ummi Aziza ta d'aga k'asan tabarma ta d'auko kud'i dubu talatin ta bata tana murmushi tace"ke kuwa Bintalo miyasa kikeda hanzari ne?Nifa banason yawan k'unshewarki cikin gida nafison kina fita sarce sarce domin ki samomin suruki".

Bintalo ta saki murmushin jin kunya tace"kayyyyy Ummi ke kam kin matsu baki rabudani ba".

Ummi Aziza ta musk'uta tace"a'aa karkiyawa maganata gurguwar fahimta kinsan kowace uwa ta gari burinta shine ta aurar da 'yarta ga miji nagari wanda zai rik'eta amana".

"haka ne Ummi nima ina fatar ubangiji ya kawomin miji nagari inyi aure".

"yauwa ashe kema kinaso haka nake burin gani Bintana".
Bintalo tana amsar kud'in ta zura cikin k'aramar jikka zata wuce Khalilu yace"Allah ya kiyaye hanya Inna".

Bintalo ta lakaci kumatunsa tace"Amin yarona".Rufe bakinta keda wuya taja k'afafunta ta fice daga cikin gidan abakin hanya taci karo da keke napep ta tareshi ta shiga.

*************************
Da Laweezi ya dawo gida Zainab bata nuna masa cewar taga bindiga a d'akinsa ba,sake jikinta tayi dashi tana masa ladabi da tsantsar shagwab'a kamar dai lokacin da aurensu yana farko,shi kansa yayi mamakin yadda ta sauko ta biye masa hatta wanka tare sukayi cikin farin ciki da annushuwa.

Haka adinning table plate guda Zainab ta zuba musu abinci suna ci suna fira hankali kwance,bayan sun kammala suka tattaro suka dawo parlour tana mak'ale ajikinsa kamar mage can ya kasa b'oye sirrin dake cikin zuciyarsa yace"Zeey miyasa yau na ganki cikin farin ciki ko kinyi mafarkin wani abu ne mai girma?".

Zainab tayi fari da idanu tana wani narke masa tace"haba My heart sai nayi mafarkin wani abu mai girma zan farantawa mijina?Kaima kasan ina sonka kawai dai rashin fahimta ne yake sa muna samun matsala".

"kinyi tunani mai k'yau haka ne gaskiya Angel da kin fahimceni tun farko bazamu yita samun matsala ba".

"Ai yanzu na gane kuskurena ka yafemin kaji heart desire bazan koma b'ata maka rai ba..!".Ta k'arasa maganar cikin taushin murya da marairaice fuska.

LAHANIWhere stories live. Discover now