LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 27*

Nasihar Mallam Jauro tayi matuk'ar tasiri azuciyarsa tareda d'aure jijiyoyin jikinsa wani irin tsantsar rashin kuzari ne ya gauraye jinin jikinsa,amma dayake shakku da tsantsar tsoron Yunusa ya rinjayi zuciyarsa domin ya tabbatar muddin Sa'idu ya auri Aziza akwai mummunan al'amarin dazai biyo baya saboda yasan Yunusa farin sani zai aiwatar da koma miye yaga ya hargitsa rayuwar gidan tareda tarwatsa duk wani farin ciki nasu!.
baffa Zubairu ya tamk'e fuska cikeda tsananin damuwa yace"nifa ba wa'azi nazo kayimin ba nazo ne domin ka amince kaba Yunusa auren d'iyarka...!".
  "amma ka nunamin bazaka bashi aurenta ba..!".
"k'warai kuwa baxan lamunce in d'auki yarinyata inba wanda bataso ba..".
Jijjiga kansa baffa yayi cikin matuk'ar d'acin rai yace"kana nufin kenan bazaka aurawa Yunusa Aziza ba..!?".
Mallam Jauro ya d'aga murya asuk'e yace"eh mana Sa'idu zan bawa d'iyata..".
baffa Zubairu yayi masa wani irin mugun kallo mai tattare da d'acin rai da tsantsar bak'in ciki arayuwa yace"tunda har ka hanawa Yunusa d'iyarka to ka rik'e abarka domin muddin ina raye Sa'idu bazai tab'a aurenta ba kaji na gaya maka.. ".
"zancen kakeso kenan baffa nidai ina kan bakana akan cewar bazan bawa Yunusa aurenta ba..!".
"haka ka fad'a..?".
"eh na fad'a kuma ko agaban waye zan iya furta maganar nan domin nasan nine akan gaskiya..!".
"kuma ko ka hanawa Sa'idu aurenta hakan bazai tab'a damuna ba saboda Aziza bata rasa masoya acikin ruggar nan ba..".

Baffa Zubairu ya yamutsa fuskarsa yace"ta lik'ewa d'ana tace batason kowa sai shi..!".

"eh saboda so babu abinda baya sawa shiyasa tace sai Sa'idu takeso da burin mallakarsa...!".

"affff saidai ta mutu da sonshi amma matuk'ar nine mahaifinsa bazai tab'a aurenta ba saida ta auri waninsa...!".

Cikeda matuk'ar takaici da tsantsar b'acin rai Mallam Jauro yace"ubangiji ya had'a kowa da mai sonshi baffa saboda haka ka b'acemin abakin k'ofar gidana..!".

"bazan tab'a tafiya ba har saina zazzage maka abinda yake cikin cikina..!".

"to saika kama jikinka...!".Mallam Jauro yana k'arashe zancensa yaja k'afafunsa ya shige cikin gidansa yabar baffa Zubairu tsaye k'yak'yam.

**********************
Asab'ule baffa Zubairu cikeda tsananin b'acin rai da tsantsar takaici daya tokare masa a mak'oshi idanunsa har wani duhu duhu yake gani cikinsu asanadiyyar zuciyarsa ta cunkushe da tunanin maganganun mahaifin Aziza, dak'yar ya iso gidansa ya taras Inna A'i tana zaune saman kujerar katako tana tatsar nonon shanu tana zubawa cikin roba madaidaiciya, alokacin ne baffa ya iso wurinta tana gaidashi amma bai jita ba saboda rayuwarsa ta gama b'aci zuciyarsa sai tafarfasa takeyi masa tana lura dashi har ya shige cikin bukka, sannan ta daure ta k'arasa tatsar nonon ta d'auko robar nonon ta kunna kai cikin tsakiyar bukkar.

  tana isowa ciki ta samu gefen gadonta na kara ta ajiye robar nonon ta dawo wurin baffa Zubairu dayake zaune yana huci kamar zaki,kallonsa takeyi tana hango b'acin rai shimfid'e afuskarsa nan take taji tausayinsa ya d'arsu azuciyarta tace"baffan yara waye ya b'ata maka rai agarka..?".
"mi yake faruwa ne..?".

Baffa Zubairu ya nisa cikin zafin zuciya da tsantsar takaicin rayuwa yace"Indo gidansu Aziza ne aka tab'oni..!".

Inna A'i ta waro idanunta cikeda mamakin kalamansa domin alokacin dazai fita bai sanar mata inda zaije ba kauda mamakinta tace"mi kuma ya kaika gidansu Aziza..?".
"mi kaje yi gidan shugaba..!?".

LAHANIWhere stories live. Discover now