LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 14*

Samrat kallon fuskar Zeey takeyi tamkar ta samu film cikeda tsagwaron tausayi da tsantsar zullumi tace"k'awata kina cikin tsaka mai wuya wannan maganar fa ina ganin sai an tashi tsaye akanta idan ba haka ba zata zamo babbar matsala arayuwarki..!".
"saboda shegen nan bazai tab'a barinki kiji dad'i aduniya ba so yake saiya kaiki mak'ura...!".
Zainab ta langwab'e kanta cikin tausayin rayuwarta tace"dukkan abubuwan da yayi mini Samrat nice na jawa kaina...!".
"da ace tun farko nayi hak'uri da dangana nayiwa iyayena biyayya da ban had'u da jarabawar rayuwa ba...!".
Samrat ta dafa kafad'arta tace"a'a k'addarorin rayuwa ne kike fuskanta Zeey ki daure ki cire komai aranki komai yayi farko yanada k'arshe..!".
"amma ki daina ganin laifin kanki duk da alokacin da guguwar soyayyarsa ta rufe miki idanu nayi matuk'ar k'ok'arin ganin na lurarsheki amma kika toshe kunnuwanki daga fahimtar gaskiya kika rungumi k'arya wadda bata tab'a dawwama arayuwa".
"ki cigaba da yawan istigifari da addu'ar ubangiji Allah yayi musu rahama..".
"dad'in abinma kafin su Ummi su rasu kin rok'esu gafara sun yafe miki shiyasa kika samu sassauci arayuwarki..!".
Zainab tayi murmushin mai ciwo azuciyarta tace"maganarki dutse ce Samrat..".
"tashi muje dinning table kiyi lunch..".
Samrat tace"ki bari zuwa anjima har cikina ya rage..".

"bazan bari ba".Cewar Zainab tana tsutsar yatsun hannun baby Amrah.
Samrat tace"to sarauniyar iyayi tashi muje.. ".Ta fad'a bayan ta mik'e tsaye zubur Zainab ta lece baki tace"babu komai ko shugabar damuwa kikacemin..".
Itace ta jagorancin Samrat har dinning table suka ja kujeru suka zazzauna tareda jawo plate ta zuba musu abinci aplate d'aya suka fara ci atsanake cikin matuk'ar natsuwa, babu mai magana acikinsu sai Amrah daketa wasa ajikin Zainab tana ja mata tsurayen gashinta Zeey tana lumshe idanunta tana cewa"lallai Amrah kinyi wayo d'an gashin da nake fashion dashi kikeson kin tsinka".
"ato gara dai data nuna miki ta girma tunda yaushe rabonki da zuwa ganinta..".
"bak'in ciki da tsantsar damuwa ne suka yimin yawa shiyasa ba kasafai nake fita ba Samrat..".
"ubangiji ya yaye miki bak'in ciki da damuwar dake cunkushe azuciyarki Zeey ai rayuwar duniyar nan sai ahankali yanzu..".
"kana zaune da mutum da zuciya d'aya shi yana nan yana neman hanyar dazai cuta maka...!".

Zainab tayi tagumi tace"babu shakka haka abin yake anyah ganin nakeyi kamar na kamu da hawan jini...!".

"dan Allah ki daina yiwa kanki muguwar fata Zeey ciwon hawan jini fa bayada k'yawo matuk'a..!".
"idan baki daina ba zanyi tafiyata gidan mijina...!".
"kiyi hak'uri k'awata ta rai da rai bazan k'ara ba kinji".

Samrat tayi k'yafci cikeda matuk'ar hasala tace"kima k'ara yanzu kiga aiki da cikawa...!".

"masifaffiya kawai".Zainab tace tana murgud'a mata baki.

"wurinki na koya".

"a'a wlh mijinki dai ya koya miki..".

"haka kika fad'a ko zan gayawa daddyn Amrah domin yaji abinda kika fad'a..".

Zainab ta rik'e baki tace"babu ruwana Samrat wlh karki had'ani rigima da daddyn Amrah...".

Samrat ta k'yalk'yale da dariyar k'eta akan yadda Zeey ta nuna tsoronta afili tace"inda kika kwafsa kenan Zeey wurin shegen tsoro..".
"ba damuwa ai tsoro gaskiya ne k'awata..".
"uhmm yadda kika fad'a kenan ba".

LAHANIWhere stories live. Discover now