LAHANI

6 2 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

_Idan babu comments zan maida novel d'ina na kud'i saboda bana jin dad'in yadda kukeyimin masoyana._

*PAGE 2*

Bata dad'e sosai ba ta fito d'aure da towel ajikinta bayan ta d'auro alwala gashin kanta duk ta jik'ashi da ruwa domin wankensa tayi da man wankin gashi,gaban mirror ta isa tana tsane ruwan jikinta da towel k'arami lotions ta d'auko ta shafe jikinta dasu, sannan ta d'auko mataji ta taje yalwatacciyar gashinta mai tsawo da santsi, mayukan gashi ta shafa agashinta ni'imtaccen k'amshi mai sanya nishad'i sai tashi yakeyi akanta, sannan ta d'auko powder da lipstick ta shafa abakinta.
kallo d'aya zakayi mata ka gane Zainab k'yak'k'yawar gaske ce domin k'yawon surarta kad'ai yana d'imautar da samari, saboda ubangiji yayi mata surar da ko kallo d'aya kayi mata zakaji farat d'aya ta shiga cikin zuciyarka, domin Zainab ta kasance chocolate colour matsakaiciya ce ita ba doguwa ba kuma ba gajera ba akwaita da dara daran idanuwa masu girma barakallah sannan gashin girarta gazar gazar,bakinta k'arami ne wanda yake d'auke da k'ananan fararen hak'ora wanda ya k'ara k'awata fuskarta, tanada doguwar fuska da siririn hanci kamar biro ubangiji Allah yayi mata baiwar surar jiki mai k'yau daga sama har k'asa komai yaji.
Saboda irin surarta itace ake kira da eight figure domin tanada hips da boob's tantsama tantsama masu d'aukar hankali da rura wutar sha'awa azuciyar duk wani lafiyayyen namiji.
bayan ta kammala kwalliyarta ta mik'e tsaye zubur ta d'auko doguwar rigarta awardrobe ta zura ajikinta, d'an kwalin rigar shine tayi amfani amatsayin mayafi tana gama shiryawa ta d'auko turare ta fesa ajikinta sannan ta koma wurin madubi tana k'arewa jikinta kallo, yadda taga masifar k'yawo sosai sai taji hawayen k'unci sun gangaro afuskarta saboda tunanin iyayenta daya fad'o mata arai zama guda dak'yar ta had'iye sauran kukanta ta gyara kwalliyarta ta d'auko sallaya ta kabbarta sallah.
  tana zaune saman sallaya tana addu'ar ubangiji ya jik'an iyayenta saiga sallamar Aunty Maijiddah ta shigo cikin tsakiyar room d'in, ganin Zainab tana addu'a yasa dole ta zauna gefen gado tana jiranta harta k'arasa addu'o'inta,Zainab ta dad'e tana karanto addu'o'i sannan daga k'arshe ta shafa addu'ar afuskarta ta waigo cikin matuk'ar ladabi da taushin murya tace"an wuni lafiya Aunty?".
Maijiddah ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tace"k'alau Zeey ya jikinki ina fatar kinji sauk'i...?".
"eh da sauk'i Aunty".
Maijiddah ta saukar da numfashi cikeda tausayinta tace"haka nakeson ji kizo parlour ga Abban Jawaheer da doctor Nazeer acan parlour suna jiranki...".
murya asanyaye tace"gani nan fitowa".
"OK sai kin fito d'in..".Aunty Maijiddah tana rufe bakinta taja k'afafunta ta fice daga cikin room d'in ta koma wurinsu doctor Nazeer dake zaune aparlour ga tire shak'e da abinci da kayan mak'ulashe agabansu suna ci suna zuba santi Aunty Maijiddah sai kallonsu takeyi tana k'yalk'yalar dariya sosai.
Acan cikin Zainab saida ta k'ara kintsa kanta ta yadda babu wanda zai fahimci cewar tana cikin matsanancin hali sannan ta zaro hijabinta ta zura saman doguwar rigarta,takalminta masu tudu kad'an ta zura a k'afafunta sannan ta fito daga ciki tareda jawo k'ofar d'akinta.

Koda ta isa cikin parlourn tuni su Jawaheer sunyi barci saman carpet yayinda su doctor Nazeer tuntuni sun kammala cin abincinsu har Abbansu Jawaheer ya shige room d'insa shida Aunty Maijiddah, Zainab ta iso cikin tsakiyar parlourn nesa kad'an da doctor Nazeer ta zauna kanta asunkuye yayinda yake binta da kallo cikeda tsananin so da shauk'in k'auna zuciyarsa sai tsananta bugawa takeyi adalilin soyayyar Zainab data mamaye ruhi da zuciyarsa ya rasa yadda zaiyi ya shawo kanta ta amshi soyayyarsa hannu bibbiyu tareda amincewa dashi amatsayin mijinta akaro na biyu.
Parlourn ne ya d'auki shiru na tsawon lokaci yayinda kowanensu da abinda yake sak'awa acikin zuciyarsa can doctor Nazeer ya kasa daurewa da miskilancinta ya bud'i baki yace mata"Zeey ba magana yau..".

LAHANIWhere stories live. Discover now