LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 15*

Tana k'arasowa gab dasu kowanensu ya shiga taitayinsa domin bata musu horon sauk'i idan ka kuskura kayiwa Aunty Maijiddah laifi, to ko ka bata hak'uri bazata tab'a hak'ura ba aranar kashinka ya bushe sai kolo ya gwadeka saboda bata yarda tayiwa 'ya'yanta rub'ab'b'iyar tarbiya ba da kuma rik'on sakainar kashi, duk dayake itace ta haifesu tasan zafin nak'udarsu amma hakan baisa take nuna soyayya da tsantsar k'auna fiyeda kima ba saboda batason tarbiyar yaranta ya tab'arb'are arayuwa.
Domin idan kukayi la'akari da lura yaran da ake nunawa soyayya fiyeda misali to bazasu tab'a zamowa abin k'warai ba, bawai ina nufin bane kada ku nunawa 'ya'yanku k'auna da soyayya ba a'a ina son komai kuyi tsaka tsakiya kada yayi yawa domin idan yayi yawa yakan haifar da babbar illah da tsantsar matsaloli arayuwar d'an Adam.
Aunty Maijiddah ta dinga k'are musu kallo cikeda so tace"Mahafuz d'ina karatu akeyi ne..!?".
Mahafuz ya d'ago kansa yana sakar mata murmushi yace"Ammy nida yaya Jawaheer muke yin karatu da home work..".
"kayyyy amma naji dad'i araina ubangiji ya taimaka..".
Jawaheer tace"Amin".
anatse suka cigaba da gudanar da home work d'insu suna rubutu.
"Zeey ya kikaji da bari bari..?".

Zainab ta saki murmushin dake k'ayatar da fuskarta tace"gasunan ina fama dasu..".
  Maijiddah ta zauna gab da ita tana yamutsa fuskarta tace"ki cigaba da hak'uri Auntyn yara.. ".
Zainab tace"laahh babu komai Aunty ai 'ya'yana ne idan ban saba kula da yara ba tun yanzu idan na samu yarana kinga kenan bazan iya kulawa dasu ba balantana in basu tarbiyar data dace..!".
Aunty Maijiddah tace"maganarki gaskiya ne..".
"Aunty akwanakin nan na daina yawan ganin yah Hayatu ina yake zuwa ne..!?".
Maijiddah ta numfasa tace"ohh aiki yasha masa kai ne a high court shari'o'i sun sakoshi agaba bayada hutu wlh ni kaina wani lokacin yana rigayata tashi daga barci domin yayi sammakon zuwa ma'aikatarsu..".
Zainab ta jijjiga kafad'arta tace"gaskiya yaya yana fama da zirga zirgan zuwa court ubangiji yasa adace ya tsareshi aduk inda ya fad'a..!".
"Amin Zeey".
"ni kaina hak'uri nakeyi domin baya bani isasshen lokaci mu zauna muna tab'a fira wata rana muna farawa zai b'ingire da barci nan take..!".
"sai hak'uri da juriya lamarin aikinsa Aunty fatanmu dai shine ubangiji Allah ya bashi sa'a acikin dukkanin lamarinsa..".
  "akowane lokaci cikin yi masa addu'a nakeyi Zeey..!".
"hakan ya kamata..!".

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

Da yamma sosai yah Hayatu ya dawo daga wurin aiki agalabaice hannunsa rik'e da briefcase d'insa yana dawowa direct ya fad'a cikin room.
yana isowa room d'insa ya cire tufafinsa yana lumshe idanunsa alamun yanayin gajiya sun bayyana atattare dashi, fad'awa bathroom yayi ya sakarwa kansa shower sannan ya fito d'aure da towel a k'ugunsa saman gado yayi masauki ya fara shafa lotion mai daddad'an k'amshi, saiga Aunty Maijiddah ta shigo cikin room d'in wurinsa tace"k'albi sannu da zuwa har ka dawo shine baka kirani awaya ba..!?".

yah Hayatu ya nisa cikeda alamun gajiya yace"sorry Jiddana na gaji ne sosai shiyasa ban kiraki ba..!".

cikin matuk'ar tausayi da tsantsar tarairaya ta kashe murya tace"ayyah sannu kaji ubangiji ya hutar da gajiya..!".

"Amin Jiddana..".

Amsar kwalbar lotion d'in dake hannunsa tayi tace"bari in shafa maka da kaina in samu wannan ladar..".

LAHANIWhere stories live. Discover now