LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 49*

Tsura mata idanunsa yayi na tsawon lokaci yanason karantar damuwar dake k'unshe afuskarta,amma ina dayake ko kad'an yanayinta bai nuna alamar *RASHIN SO* agaresa ba shiyasa kwata kwata bai fahimci bata sonsa ba, asanyaye tana kallon gabanta ta iso wurinsa cikin raunanniyar murya ta gaidashi ya amsata.
Bayan gaisuwa bata sake magana ba shi kuma kallonta kawai yakeyi alokacin ne yakejin soyayyarta tana k'ara ninkuwa a k'ok'on zuciyarsa,wani irin sanyi ne ke kai masa farmaki a ilahirin sassan jikinsa dak'yar ya tattaro natsuwarsa wuri d'aya domin idan yace zai tsaya kallonta zata iya shagaltar dashi ya kasa aiwatar da komai.
Doctor Nazeer ya kalli k'wayar idonta yace"hearty kinyi shiru tun d'azu bayan gaisuwa bakicemin komai ba".
  Batare data dubeshi ba tace"yaya Nazeer to mi kakeson ince bayan gaisuwa..?".

Murmushi k'awace akan k'yakk'yawar fuskarsa yace"so nakeyi ki saki jikinki muyi fira tunda niba bak'onki bane".

Zainab kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa taja bakinta ta tsuke.
Ganin yayi batada niyar magana yasa ya gyara tsayuwarsa yana fuskantarta yace"Zainab dama dalilin dayasa nazo shine akan batun yadda kikeson tsari da kwalliyar room d'inki ya kasance shine nace bari inzo inji ta bakinki".

Murya k'asa k'asa tace"dukkanin abinda ka tsara acikin gidanka toni bayada wata matsala awurina".

Doctor Nazeer yace"a'a kar muyi haka dake nafison ki fad'i ra'ayinki saboda banason inyi abinda ba shine choice d'inki ba".
"ra'ayina kenan".
"Shikenan tunda bazaki bud'i baki kiyi magana ba kunyata kikeji duk dai abinda kika gani ba daidai ba sai kiyi hak'uri domin laifinki ne".

"Bazan ga ma laifinka ba".
"yayi miki k'yau sosai Hajara dai nasan idan na tambayeta ra'ayinta baza taji kunyar fad'amin sirrin zuciyarta ba".
Zainab ta bintsire baki cikin nuna halin ko in kula tace"Hajara daban Zainab daban".
"haka ne gaskiya".
Sun jima tsaye shi kad'ai yake zuba zance ita kuma daga eh sai uhmm babu abinda take cewa,can saiga Laweezi ya parker motarsa kusa dasu hankalinsa atashe zuciyarsa sai zugi da k'una takeyi masa yayinda kishin Zainab ya bayyana k'arara afuskarsa,jin tsayuwar mota yasa doctor Nazeer ya juya b'angaren dayake ya kallesa sannan ya maida kallonsa ga Zainab daya duk ta daburce da d'imaucewa asanadiyyar ganin b'acin rai kwance afuskar muradinta, doctor Nazeer ya lura da chanzawar Zainab farat d'aya ya kuma fahimci ta daburce adalilin ganin wancan wanda alamu sun nuna saurayinta ne.
Laweezi fitowa yayi daga cikin motarsa ya k'araso wurinsu ba ko sallama ya dubeta yace"Angel wurinki nazo".
Bak'in ciki ne ya mamaye zuciyar doctor Nazeer jin yadda ya kirata da Angel alhalin ta kusa zamowa mallakinsa,yanayinsa ne ya sauya idanunsa suka chanza colour ya dubi fuskar Zeey yace"Zeey wa nene wannan dayake kiranki da suna Angel?".
"miye had'inki dashi..?".

Ganin yadda yake jero mata tambayoyi ajere ya k'ara rikitar da ita jikinta yana rawa ta kasa magana!.
Laweezi ne yayi charapp yace"ni saurayinta ne kuma sonta nakeyi kamar yadda kake sonta".
Rayuwar doctor Nazeer ta k'ara b'aci zuciyarsa tana suya ya matso dab dashi yace"kai mahaukacin ina ne ka tab'a jin inda akayi neman aure cikin nema..?".
"ko baka sani ba bakada labarin cewar saura wata d'aya cif ta zamo matata..?".
Kallon banza Laweezi yayi masa yace"idan na sani sai mi to?Ni babu ruwana da aurenku saura wata d'aya ko saura kwana d'aya ne bazai daina gwada sa'ata ba domin ganin na k'waceta ahannunka..!".
Ahasale doctor Nazeer da shak'e masa wuyan riga saboda zuciyarsa ta kawo awuya idanunsa har rufewa sukeyi adalilin tururin yaji yaji dayake ji acikinsu!.
Da wata irin murya yace"kai har ka isa agabana kace zaka rabani da ita..!".
"wa nene kai agarin nan miye kake tak'ama dashi..!?".
Laweezi bai jaye masa hannu ba yayi killer smile yace"ba sai na baka amsar tambayarka ba amma da idanunka zakaga irin abinda zai biyo baya saboda haka sakarmin wuyan riga..!".
"in sakeka kaji dad'in fad'in kaci galaba akaina".
"nace ka sakemin wuyan riga..!".Ya sake fad'a akausashe.
"ank'i asaki munafuki mai neman aure akan aure..!".
"to tunda lalama batayi dakai zan nuna maka niba k'aramin shak'iyi bane".
"so nakeyi inga zahiri".

LAHANIWhere stories live. Discover now