LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 67*

Laweezi yaji maganarta tayi masa zafi tareda saka k'una aransa cikin wani irin zafin rai yace"Zainab naji ni azzalumi ne ki sani zama dani dole ko kina so ko bak'ya so..!". Zainab ta hararesa tace"k'arya ne zaman gidanka na wani lokaci ne Laweezi saboda haka kasa aranka komai daren dad'ewa saina bar maka gidanka...". Laweezi ya daka mata tsawa yace"dakata Zainab! Banason zancen banza da aurena akanki kika cewa sai kin barmin gidana..".
Zainab ta yamutse fuska tace"k'warai kuwa domin bazan iya cigaba da zaman aure da makashin iyayena ba..!".
Cikin zafin rai Laweezi yasa hannu d'aya ya fincikota kamar mage cikin kakkausar murya mai nuna alamun b'acin rai yace"ohhh ni kike zargi akan mutuwar iyayenki ko..?Zainab idan bakisan yadda zaki tsabtace kalamanki akaina ba to ina tabbatar miki wata rana rayuwa zata b'aci..". Zainab dake rik'e ahannunsa ta dinga kichaniyar k'wace kanta tace"kasheni zakayi kamar yadda ka kashemin iyayena ko sakarmin hannu Malam..!".
Idanunsa suka kad'a sukayi jajir zuciyarsa sai tururin k'una takeyi masa yace"eh kasheki abu ne mafi sauk'i agareni idan na gadama ko azatonki zaki iya tsallakewa tarkona ne..?".
"Hmm ko ban tsallakewa tarkonka yanzu ba wata rana kana ji kana gani zanyi maka nisa..".
"To shikenan zan nuna miki ni murucin kan dutse ne ban fito ba saida na shirya..!".Yana rufe bakinsa ya tunkud'eta ta fad'a akan tiles kaji gwaffff kanta ya bugi nan shi kuwa da hanzari ya fice daga cikin room d'in zuciyarsa sai k'una takeyi..!.

Zainab dake kwance saman tiles ta mik'e zaune cikin bak'in cikin abinda Laweezi ya aikata mata,inda kanta ya bugu ne taga wurin ya kumbura sosai jini ya taru wajen,wani irin d'aci da rad'ad'in ciwo ne taji ya mamaye ruhinta saboda yadda Laweezi ke neman nakkasa mata rayuwa.

*************************
Barisster Hayatu yana kishingid'e akan cushion jarida ce agabansa yana karantawa anutse, yayinda Aunty Maijiddah ke cikin kitchen tana hada-hadar had'o masa lunch bayan ta gama had'a komai akan tire,ta sunkuci tiren ahannunta sai cikin aparlour isowarta keda wuya ta aje tiren agabansa tace"daddyn Jawaheer sannu da aiki..?".

"Yauwa Jiddanah agaisheki da fama".

"Uhmm daddyn Jawaheer"...

Maijiddah tazo kusa gareshi ta zauna bayan tayi serving d'inshi atsanake barisster Hayatu ya fara cin abincin har ya kammala, sannan ya wanke hannu yasha ruwa yace"Alhamdulilahi cikina ya cika mak'il babu wurin tura wani..".

Maijiddah tayi yak'e tace"to haka akeso kenan babu wurin saka ruwa..".

"Inasa ran haka matata".

Aunty Maijiddah ta karkace kai cikin tsananin damuwa tace"hubbyna inason tattauna muhimmiyar magana dakai..".
Hayatu ya maida kallonsa gareta yace"ina saurarenki Jiddanah".

"Dama akan maganar Zeey ne naga har yanzu bamuyi dogon motsi ba,shine nakeson mukai k'arar Laweezi kotu ya sawwak'ewa k'anwata wannan jarababben auren ya isheni kaga ni kad'ai gareta aduniya nima haka".

Barisster Hayatu ya jinjina maganar yace"kibar komai ahannuna Jiddah wannan karon Laweezi bazaiji dad'ina ba ina fad'a miki saboda yaron ina kan bincike akansa duk inda naje bak'ya tab'a jin alkhairinsa sai sharrinsa".

Maijiddah ta numfasa cikeda matuk'ar zullumi tace"ai shiyasa kaga hankalina ya kasa kwanciya akan d'auketa da yayi ya maidata gidansa..!".

  "Babu abinda zai faru kedai ki zuba idanu kiyi kallo".

LAHANIWhere stories live. Discover now