LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 55*

Can yaja nannauyar ajiyar zuciya yace"Hajara mahaifiyar Zainab batada laifi cikin wannan al'amari kafin mahaifinta ya rasu yana sona da ita,bayan rasuwansa ne aka d'aga ranar aurena da ita maimakon ayi aurenku atare sai aka d'aga asanadiyyar rashin baba Sa'idu,to aranar ne yayan mahaifinta baba Yunusa da kawunta Rabilu suka had'a k'ulalliyar da auren ya juye ya koma kan Laweezi! Shiyasa ma kikaga har ankai tsawon wannan lokaci bance komai ba gameda Zainab".
Hajara ta langwab'e kai cikin matuk'ar tausayin mijinta tace"ayyah hubby gaskiyar magana wad'annan mutane basu k'yauta maka ba sunci amanar dangantar dake tsakaninsu da baban Zainab".
"kansu suka cuta sweetie dukkanin cin amanar da suka yiwa wad'annan yara ubangiji ya sama yana kallonsu".
Hajara ta d'auko k'aramin turmi ta fara jajjage tace"tabbas haka ne hubby domin *SAKAYYAR ALLAH* tafi ta kowa".
Doctor Nazeer ya nisa yace"yanzu babu abinda yafi kamar inga an kama kosu waye sukeda hannun akan mutuwar baba Sa'idu".
Ad'ad'are Hajara tace"dama ba mutuwar Allah ce yayi ba kashesa akayi..?".
"haka result d'in asibiti ya nuna wanda abokina doctor Uwaisu ya bamu".
  "Allah ubangiji ya tonawa koma waye asiri su kuma ya basu hak'urin rashinsa".
Nazeer daya gama wanke wanken yana tsabtace hannunsa yace"amin sweetie".

*************************
*BAYAN KWANA BIYU*
Aunty Maijiddah tayi shirinta tsab cikin tsadadden lace d'inta ta rataya handbag a kafad'arta,kallo d'aya nayi mata naga cikinta ya tsufa sosai tana gab da haihuwa Jawaheer ta kirata ta shiryata cikin lace irin nata sannan suka fito daga cikin d'akin.
Iske yah Hayatu sukayi sanye da glass aface d'insa zaune yana dudduba takardun dake gabansa,jin takun tafiyar mutum ne yasa ya d'ago kansa idanunsa suka sark'e cikin na Maijiddah murmushi yayi mata yace"Jiddanah ina za'a je da akayi wannan uban kwalliyar?".
Aunty Maijiddah ta langwab'e kai tace"auuuu wai kana nufin cewar ka manta jiya nace maka zanje naga Ummina".
Jijjiga kansa yayi yace"I'm sorry dear na manta ne wai kinada labarin cewar tun ranar da akayi auren Zainab mijinta bai tab'a bari taje wurin Ummi ba ko sau d'aya".

Aunty Maijiddah ta gyad'a kanta tace"gidan mijina daban nata daban ya za'ayi in sani idan kuwa haka ne Laweezi yaci amanar k'auna domin Zainab bata cancanci haka awurinsa ba ko don saboda soyayyar data nuna masa".
Barisster Hayatu ya zaunar da Maijiddah gab dashi yace mata"Jiddanah duk inda kike zaton yaron nan ya wuce nan,ni damuwata d'aya ce binciken da mukeyi akan mutuwar baba Sa'idu har yanzu bamu gano komai ba".
Maijiddah tace"dear kubi komai asannu jikina ya bani jinin mahaifina bazai tab'a zuba k'asa banza ba saboda haka ka rage yawan damuwa akan wannan al'amarin".

Barisster Hayatu yaja numfashi yace"naji yanzu dai idan kikaje wurin Ummi ki rarrasheta akan lamarin Zainab ki nuna mata cewar ba laifinta bane ubangiji ne ya had'ata da shaid'anin miji shiyasa yake amfani da ikonsa akanta yana juyata yadda ya gadama".
Aunty Maijiddah ta lece baki tace"zanyi mata bayani yadda ya dace".

"Good". Barisster Hayatu ya dakatar da abinda yakeyi ya tashi tsaye itama Aunty Maijiddah tabi bayansa suka rankaya har parking lot.

*************************
Bintalo durk'ushe k'asa tana wanke wanken kwanoni harta kammala Khalilu yana manne kusa ga Ummi Aziza sai zuba mata surutu yakeyi kamar parrot,ita kuma dayake tanada son yara sai biye masa takeyi tana sakin murmushin murna sosai saboda koba komai Khalilu yana deb'e mata kewa da mantar da ita dukkanin bak'in cikin dake manne azuciyarta.

LAHANIWhere stories live. Discover now