LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 16*

Aunty Maijiddah ta sassauta muryarta cikin sigar k'auna tace"shikenan karki dad'e sosai Zeey ubangiji ya kiyaye hanya..".Zainab tace"bazan dad'e ba muna tab'a fira zan dawo in taimaka miki wurin girki..!"."To ina dubin hanyarki k'anwata..!"."Zaki ganni kuwa nan da awa biyu cur da yardar Allah..!".Aunty Maijiddah ta tashi tsaye ta fara tafiya tana tunkarar hanyar shiga cikin parlour tace"uhmmm".Zainab ta tadda motar bayan ta k'ara saukar da glass k'asa dayake baba maigadi tun lokacin data fito ya wangale mata get d'in, batare da tayi horn ba ta fice daga cikin gidan da sassarfa maigadi ya maida get ya rufe..

Ahankali take jan motarta cikeda matuk'ar natsuwa da k'warewa tana sauraren karatun qur'ani mai girma har ta iso wurin wani irin madaidaicin shago ta parker motarta agabansa,k'yak'k'yawan k'afafunta ta zuro ta fito masu sanye da tsadaddin takalma d'aid'aikun mutanen dake giftawa ta gabanta sai kallonta sukeyi suna yaba k'yawon halittarta, sanya key tayi ta kulle motar handbag d'inta rataye a kafad'arta direct ta shige cikin katafaren shagon ta dad'e aciki tana sayayyar kayan masarufi sannan daga k'arshe ta fito rik'e da ledodi biyu manya manya ahannunta.
tana isowa wurin motarta tayi amfani da key ta bud'e motar tareda ajiye ledodin mazaunin gefen driver, sannan ta zagayo ta koma gefen driver seat ta shiga ta zauna ta tadda motarta tareda saitata akan kwalta tana tafiya sannu ahankali cikin yanayin natsuwa.

  Haka dai ta dinga sharara gudu akan titi harta k'araso cikin unguwarsu Samrat direct ta k'araso adaidai bakin gabjejen get d'in gidan Samrat ta parker motarta awaje, saida ta b'ata wasu mintuna k'alilan aciki sannan ta fito cikin asanyaye tamkar wadda akayiwa dole ta fito daga ciki, ledodin ta rik'e ahannunta bayan ta sanya key ta kulle motar direct ta isa bakin k'aramar k'ofar gidan maigadi yana ganinta yazo ya gaidata yana washe hak'ora yace"hajiya Zainab an iso lafiya..?".
"lafiya k'alau..".
"to madallah komai yayi k'yawo..".
Zainab ta saki fuskarta tace"ko matar gidan tana ciki kuwa..?".
"eh hajiya tana babu inda taje yau..!".
"OK ba damuwa".Ta fad'a tareda zuge zip d'in handbag d'inta ta ciro dubu uku ta bashi k'yauta.
Shi kuma ya amshe yana zuba mata godiya sosai da yi mata addu'o'in gamawa lafiya da duniya, Zainab bata tsaya k'arasa sauraren maganarsa ta tunkari hanyar da zata sadata da parlour.
Isowarta keda wuya ta iza k'ofar parlourn tareda kunna kai cikin tsakiyar parlourn babu kowa tsit kakeji hatta da makeken bango TV dake ciki akashe yake, ganin babu kowa yasa Zainab bata zauna ba direct ta nufi room d'in Samrat shiga ciki tayi ta hango Samrat kwance ta aza baby Amrah saman ruwan cikinta tana yi mata wasanni ita kuma sai b'angalar dariya takeyi, can taji takun tafiyar mutum a d'akinta da azama ta tashi zaune domin duk atsammaninta ba mutum bane, d'agowar da tayi ne idanunta suka fad'a cikin na Zainab ai kuwa da sauri ta sauke Amrah saman gado ta shek'o da sassarfa ta rungume Zainab cikeda tsagwaron murna da annashuwa afuskokinsu tace"lale marhaban da k'awata Zeey..".
Zainab ta jaye jikinta ana Samrat tace"ke ni duk kin ruk'uk'umeni tareda azamin nauyin jikinki saboda kin riga kin saba hayewa daddyn Amrah ajiki..".
Samrat taja hannunta sukayi masauki saman gadonta tace"eh naji babu komai duk abinda zaki fad'a bazai tab'a damuna ba..! ".
"ko..!?".

"k'warai da gaske Zeey..".

"kedai kika sani..".

"harda ke Zeey matar Laweezi..!".Ta fad'a azolaye cikin matuk'ar tsokana.

LAHANIWhere stories live. Discover now