LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 66*

Ana tsirga mata allurar bada jimawa ba ta fara aiki nan take nannauyar barci yayi awon gaba da ita ruwan hawaye kwance yab'e yab'e kwance afuskarta,su Aunty Maijiddah sunji dad'in yadda doctor Nazeer ya damu da Zainab duk baisan cewar aurenta ya mutu ba,kallonsu kawai yakeyi yana nuna rashin jin dad'insa afili yace"Aunty please ku daina kuka Ummi ta riga ta rigamu gidan gaskiya babu abinda mamaci ke buk'ata sai addu'a, saboda haka ku daure nasan abin da ciwo amma dukanmu anan bazamu tab'a tsallake sirad'in mutuwa ba..".
"ubangiji Allah shine ya baku Ummi amatsayin mahaifiya to don ya amshi rayuwarta bai kamata ku nuna bak'in cikinku ba kuyi mata fatar samun rahamar ubangiji shine yafi dacewa..".
Aunty Maijiddah ta girgiza kai taja numfashi tace"tabbas Nazeer ka tuna mana abinda muke k'ok'arin mantawa nagode sosai da tunatarwa".
"ki daina yimin godiya ai dukkan abinda ya sameku nima ya sameni saboda tamkar matsayin mahaifiya Ummi take gareni..".
"Ku samu wuri d'aya ku natsu kada kuyi wata hayaniyar da zata tayarda Zainab".
"Insha Allahu zamu kiyaye likita".Cewar Bintalo tana nishin takaici da tsantsar fargabar komawarta k'auyensu.

Doctor Nazeer ya isa wurin barisster Hayatu yace"ka kirasu DPO Usman suzo su tabbatar cewar sanadiyyar wuk'ar da aka soka mata ne ta rasu..!".
"Inada niyar haka Nazeer". Barisster Hayatu ya ciro phone d'insa a aljihu yayi dialling nombar DPO Usman tana shiga yayi receiving call gaisawa sukayi atsakaninsu sannan ya fad'a abinda ake ciki,anan ne jikin DPO Usman ya mutu hankalinsa ya d'unguma yace masa gasunan tafe,k'it barisster Hayatu ya katse wayar iyayensa ya kira dasu Mallam Bojo ya fad'a musu abinda ake ciki suma hankali tashe suka ce gasunan tafe.
Shima doctor Nazeer ya sanarwa iyayensa cikin jimami da alhini suka ce suna zuwa.

Suna zaune jugum kowanensu da abinda yake sak'awa cikin zuciyarsa duniyar ce tayi musu bak'ik'irin komai ya dagule musu,su DPO Usman ne suka fara kunno kai da hanzari suka isa wurin gawar Ummi Aziza su doctor Nazeer suka iso gab dasu,wata farar takarda ce naga Nazeer ya fiddota yana wa su DPO Usman bayanin cewar wuk'ar da aka sokawa mata ta tab'a wani abu cikin d'iyan hanjinta shiyasa abin yayi affecting d'inta harta rasu sannan ga tunanin an keta mata haddi da takeyi shiyasa zuciyarta ta karaya sosai.
Su DPO Usman tsaye sukayi suna sauraren bayanin doctor Nazeer har ya k'arasa, jinjina maganar sukayi aransu sukace zasuyi k'ok'arin tsananta bincike akai idan ubangiji ya yarda,tun anan dai akwa d'auki gawar Ummi Aziza aka saka cikin mota Zainab dake barci cikin matsanancin hali Bintalo aka bari ta cigaba da kula da ita kafin ta farfad'o.!.

Suna isa gidan baba Sa'idu suka taradda iyayensu har sun zo anan take wurin ya k'ara kachamewa da koke-koken mutuwa,har mutanen ruggarsu Ummi Aziza sunzo hardasu baba Yunusa ba'a barsu abaya ba sai sharar kwalla sukeyi cikeda tsananin tausayin rayuwarsu Maijiddah.
wanka akayiwa gawar Ummi Aziza aka sakata cikin likkafani😭 su Mallam Bojo sukayi mata sallah, mak'wabta,'yan uwa da abokan arzik'i suka shisshige cikin mototi aka d'unguma zuwa mak'abarta,dayake daga gidansu zuwa mak'abartar ba nisa nan take suka iso aka fara gina kabari saida akayi rami mai zurfi daidai tsawon jikinta da fad'inta sannan aka sakata cikin kabarin.
Ana sakata ciki aka kawo ganyayyaki ana lullub'e kabarin dasu domin ba'a son abar ko k'aramin k'ofa ce ga mamaci,k'asa aka dinga zubawa kabarin ana yi ana k'arawa har saida suka tabbatar da ko'ina ya rufe babu k'ofar shan iska sannan suka juyo suka dawo gida suka barta daga ita sai abinda ta aikata aduniya..!.

LAHANIWhere stories live. Discover now