LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 60*

Bata jima da zama zuciyarta ak'untace babu wani sauran farin ciki aranta Laweezi ya izo k'ofar parlour ya shigo tsakiyar parlourn,mik'ewa tsaye tayi zata amshi kayayyakin dake hannunsa ya dakatar da ita yace"kibarshi kawai Angel nagode".
Cikin d'acin rai Zainab ta koma ta zauna batare data k'ara kulashi ba saboda ta tsani walak'anci da disgi arayuwarta, saida ya zauna na d'an wani mintuna k'alilan sannan ya mik'e tsaye yayi tafiyarsa d'akinsa babu ko kallon arzik'in daya shiga atsakaninsu.

Bayan ya wuce ne Zainab tayi k'yafci cikin b'acin rai tace"na gaji da wannan auren bafa zai yiyu in tsaya takabar mai rai ba saboda na fahimci cewar so yake ya kasheni diss inyi mutuwar k'ask'anci..!".
Sak'a da warwara ta dingayi azuciyarta hanyar da zata b'ullowa al'amarin Laweezi da kuma fitar da kanta daga cikin k'angin rayuwa.

*************************
Bayan baba Yunusa ya dawo daga wurin aiki ne yana sanye da jalabiyarsa Inna Lantana tazo har wurinsa tana fad'a masa irin bala'in da Gid'ad'o yakeson jawo musu arana tsaka!.
Baba Yunusa ahasale ya kalleta yace"to ke miye amfanin fad'amin cewar Gid'ad'o yanason zuwa ya tunkari Alhaji Laweezi ya fad'a masa yanason matarsa..?".
"Anya kuwa kunsan wa nene Laweezi..?".
"Anya kunsan had'arin dake tattare dashi kuwa Lantana..?".
"Hmm yaron nan da kike gani koni nan tsoronsa nakeji saboda haka kiyi gaggawar sanarda Gid'ad'o kada ya kuskura ya bari wannan maganar taje kunnensa idan ba haka ba ya gama yawo..!".
"Nidai ina zaman zamana lafiya bazan yarda d'anki ya jefani cikin masifa ba akan tseratar da rayuwata da dukiyata zan iya aikata koma miye Lantana..!".
Inna Lantana ta sassauta murya sosai tace"kwantar da hankalinka Yunusa ai k'anensa yayi masa nasiha kuma yaji saboda haka ina sa ran babu abinda zai faru sai alkhairin ubangiji".
"Kudai kuka sani ba ruwana kowa ya d'ebo da zafi ya sakawa bakinsa..".
Inna Lantana ta rausayar da kanta tace"babu ma wanda xai d'ebo da zafi ya sakawa bakinsa Yunusa har ya k'onashi".
"Banason dogon surutu zaki iya tafiya..!".
Inna Lantana ta mik'e tsaye ranta ab'ace tace"aiko baka fad'a ba tafiyata zanyi".Tana rufe bakinta taja k'afafunta ta fice daga cikin d'akinsa cikeda tsananin bak'in ciki.

*************************
Acikin wani irin had'ad'd'en lambu dake cikin wani b'angaren gidan doctor Nazeer ne na hangoshi da Hajara suna shak'atawa tareda k'yakk'yawar 'yar Khairat wadda tuni ta iya rarrafe.
Kallonsu juna kawai sukeyi suna sakin murmushi duba d'aya zakayi musu ka gane suna cikin nishad'i da kwanciyar hankali arayuwar aurensu.

Hajara ce ta aza kanta akan kafad'arsa tace"My doctor ka sani har kaine farin cikina alokacin dana shige cikin kogin k'auna na rasa wanda zai tsamoni har ina neman sumewa acikin kogin sai daga sama ubangiji ya jefomin kai ka tsamoni mijina".
Doctor Nazeer yaji dad'in kalamanta har cikin jini da tsoka yace"Hajara ada naso nayi matuk'ar wauta na rashin amsar tayin soyayyarki akan soyayyar Zeey data makantar dani daga kallon kowace d'iya mace da sunan so amma ayanzu dana d'and'ani zumar soyayyarki sai naji kema kinada daraja da babban matsayi azuciyata".
"har kasa naji sanyi araina mijina domin banyi zaton zanji wannan maganar daga bakinka ba tabbas kai mai k'aunata ne da gaskiya".
"Ai ya zamo dole in k'aunaceki sweetheart saboda tuntuni kika bani farin ciki na har abada sannan kika haifamin k'yakk'yawar 'ya Khairat".
Hajara taja numfashi cikeda dad'in rai tace"ubangiji Allah ya k'ara mana k'auna da soyayyar junanmu".

LAHANIWhere stories live. Discover now