LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 62*

Rarrashinta Samrat ta cigaba dayi cikin tsananin tausayawa rayuwarta saida taga ta rage kuka sannan ta fuskanceta tace"Zainab kiyi hak'uri tabbas abin da ciwo matuk'a ka fahimci cewar mijinka neman matan banza yakeyi,amma tunda shine shugabanki babu yadda zakiyi dashi sai hak'uri..!".
"Hak'uri kuma?In cigaba da hak'urin zama dashi bak'in cikinsa ya kasheni gaskiya zance na gaji gara na tattara kayana na gudu inbar masa gidansa..!".
Atsorace Samrat take kallonta cikeda mamaki tace"kije ina Zeey idan kika gudu..!?".
"In koma wurin Ummina".
"Kul!Na fad'a miki kada ki soma wannan kuskuren Ummi tana zaman zamanta cikin kwanciyar hankali ki jawo mata wata masifar rana tsaka".
Zainab tace"gidanmu zanje wallahi saidai ina zuwa ta koroni..!".
"to shikenan tunda bak'ya jin shawara ga fili nan".Inji Samrat zuciyarta ab'ace.
"haka zaki fad'a saboda ba kece cikin irin wannan halin da nake ciki ba..".
Samrat tace"bazaki gane ba zuwanki can zai k'ara tunzara mijinki ne har ya k'ara musguna miki Zeey kema kinsan Laweezi ya tsani kije gidanku koda wasa..".
"Babu ruwana inace kusan kullum sai yaje gaida hajiya Halima ai uwa batafi uwa ba".
"kedai kika sani".Cewar Samrat taja baki tayi shiru tana kallon yadda Zainab ta fara had'a kayayyakinta wuri d'aya cikin k'aramar akwati.

*************************
Laweezi yana fita bai zarce ko'ina ba sai gidan doctor Blessing wanda dama ya saba zuwa can suna aikata abinda suka gadama.
Babu sallama ya shigo tsakiyar parlour zaune ya iskota daga ita sai mini skirt da ficiciyar riga wanda ta bayyana surar jikinta afili,jin k'amshin turarensa yasa ta iso da sauri ta rungumesa tareda yi masa peck agoshi tace"sannu da zuwa my sugar".
Hannunsu sark'e cikin na juna tajashi sai wurin dinning table ta zuba musu abinci aplate d'aya,saida suka ci sukayi nak sannan suka sha ruwa tana manne ajikinsa suka rankaya zuwa d'aki.
Suna shigowa sukayi masauki akan gado Blessing tayi shame shame akan jikinsa cikin duniyanci tace"my sugar ya jikin Zainab?".

Huci yayi mai k'unshe da d'acin zuciya yace"Blessing tana gida na barota taji sauk'i..".Har yaso ya fad'a mata abinda ya wakana atsakaninsu sai yaga rashin dacewar hakan.
"haka nakeson ji da sannu jikinta zai warware".
"Alamu sun nuna haka".
Blessing batare da b'ata lokaci ta fara aika masa zazzafan sak'onni iri iri shi kuma ya dinga maida mata martani,ganin sun fara numfashin buk'ata yasa naja k'afafuna nayi gaba domin nasan abinda zasu aikata ba mai k'yau bane.

*************************
Su barisster Hayatu suna tsaka ga tafiya suka had'u da wani tsoho mai suna Mallam Hakimi nan take suka tsayar da mota agefe, barisster Hayatu ya fito suka gaisa amutunce anan ne ya fara tambayar Mallam Hakimi yace"baba ko kasan wa nene Alhaji Laweezi?".
Mallam Hakimi ya nisa cikin yanayin b'acin rai yace"to yaro Laweezi d'a ne ga Mallam Haruna Mai dawaki ubangiji ya jik'ansa da rahama mahaifinsa mutumen kirki ne yanada mutunci da kima a idon jama'a,komai k'ank'antarka yana baka girmanka bayada girman ko ko jiji dakai arayuwarsa ya iya tafiyarda rayuwarsa cikin rufin asiri da wadatar zuci,sana'ar saida dawaki itace ya gada awurin mahaifinsa to dayake Haruna ya taso mai k'wazo da neman na kansa shiyasa ya koyi sana'o'i iri iri kala kala saboda ya samu abinda zai taimaki iyayensa ya auri budurwarsa Halima..".

"To baba kenan mahaifin Laweezi ya kasance abin kwantance wurin halayyar kirki da girmama mutane..?".

"Alal hak'ik'a haka abin yake yaro..".

LAHANIWhere stories live. Discover now